Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴar jaridar Kenya, Rukia Bulle ta lashe gasar Komla Dumor ta BBC a 2024
An bayyana wata ƴar jaridar Kenya, Rukia Bulle a matsayin wadda ta lashe kyautar Komla Dumor taa BBC News ta shekarar 2024.
Matashiyar ƴar shekara 26 wadda ita ce mutum ta tara da ta taɓa lashe kyautar, tana aiki ne a kamfanin jaridar Kenya's Nation, inda ta ƙware kan labaran da ya fi shafan mutane.
Bulle ta kuma shahara a shafin sada zumunta na TikTok saboda irin abubuwan da take wallafawa kan rayuwar ƴan jarida.
An ƙirƙiro lambar yabon ne don girmama Dumor, wani ɗan jarida daga Ghana kuma ɗaya daga cikin masu gabartar da labaran duniya na BBC wanda ya rasu a shekarar 2014.
Dumor ya mutu ne yana da shekara 41.
Dumor ya yi aiki matuƙa ba tare da gajiya ba da nuna jajircewa da sadaukarwa domin kawo labarai kan nahiyar Afrika inda ya nuna ƙwazo da dagewa.
Bulle ita ma ta nuna ƙwazo da sadaukarwar da kuma jajircewa wajen labarai da suka fi shafar mutane inda take jin ta-bakin mutanen da ba a cika ji daga gare su ba da kuma ƙwarewarta wajen gabatarwa wanda hakan ya gamsar da alƙalan.
"Lashe wannan kyautar na da matukar amfani a gare ni," in ji Bulle," A matsayinmu na ƴan jarida, a kodayaushe ya kamata mu riƙa nuna ƙoƙarinmu ba tare da la'akari da ko ana gani ba ko ba a gani, saboda haka samun wannan kyautar ya tabbatar min da cewa jajircewata ta yi amfani."
Bulle ta kuma bayyana a shekarar da ta gabata a cikin jerin sunayen Musulman Kenya 100 da suka fi shahara da tasiri.
"Ina fatan wannan kyautar da na samu za ta ƙarfafa gwiwar mata matasa kamar ni da ke saka hijabi kuma daga ƙananan al'ummomi wajen samun babban buri da cimma abin da suka fatan su zama.
Ƴar jaridar za ta yi wata uku tana aiki da BBC da ke ɓangaren talabijin da rediyo da kuma shafukan intanet.
Kuma za ta samu gogewa daga manyan ƴan jaridan BBC.
Tarik Kafala, mukaddashin daraktan sashen yaɗa labarai na BBC, ya bayyana jin daɗinsa kan nasarar da aka samu na lambar yabo ta Komla Dumor wajen raya ayyukan ƴan jarida a faɗin Afirka.
“Waɗanda suka samu kyautar a baya sun bayar da gudummawa sosai ga aikin jarida, don haka muna farin cikin maraba da Rukia Bulle a matsayin wadda ta lashe kyautar ta bana,” in ji shi.
Waɗanda suka taɓa samun kyautar a baya sun haɗa da Paa Kwesi Asare da Dingindaba Jonah Buyoya da Victoria Rubadiri da Solomon Serwanjja da Waihiga Mwaura da Amina Yuguda da Didi Akinyelure da kuma Nancy Kacungira.