Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Martanin iyalan Abacha kan kalaman Janar Babangida
Makonni biyu bayan tsohon shugaban mulkin soji a Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ƙaddamar da sabon littafinsa kan rayuwarsa mai suna ' A journey in Service' inda a ciki ya yi zargin cewa marigayi Janar Sani Abacha ne ke da alhakin rushe zaben 12 ga watan Yunin 1993, iyalan marigayi Abacha sun fito fili sun musanta zargin.
"Abin da ya faru, abin da na sani ne. Ƙasar nan na son ganin na nuna nadamata," kamar yadda Babangida ya rubuta a cikin littafin.
Cikin littafin nasa, tsohon shugaban mulkin sojin ya amince cewa cif Moshood Bashorun Abiola, shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasar na ranar 12 ga watan Yuni.
Da ya ke bayyana rushe zaɓen a matsayin 'kuskure'', Janar Babangida ya ɗaura laifin kan wasu muƙarrabansa, bisa jagorancin marigayi Janar Sani Abacha, wanda a lokacin shi ne babban hafsan tsaronsa, kan ɗaukar matakin, wanda a cewarsa an yi hakan ne ba tare da umurninsa ba.
Wannan zargi ya jawo cece ku ce a tsakanin alumma wanda a cewar iyalan, ya sa ya zama wajibi iyalai da kuma zuri'ar marigayi Sani Abachan su fito su mayar da martani domin fito da sahihin tarihi da kuma adalci.
A cikin wata sanarwa da Mohammed Abacha ya fitar a madadin iyalan, ya ce ''ya na da muhimmanci in bayyana cewa Janar Sani Abacha ba shi ba ne shugaban ƙasa ko kwamandan dakarun Najeriya a lokacin da aka rushe zaɓen 12 ga Yuni ba, kuma an yanke hukuncin soke zaɓen ne ƙarƙashin mulkin Janar Ibrahim Babangida wanda a lokacin shi ne shugaban mulkin soji kuma shi ke da ƙarfin iko a, hakazalika shi ke da alhakin dukkanin ayyukan da gwamnatinsa ta yi''.
Sanarwar ta kuma ce "duk wani yunkurin ɗaura alhakin kan Janar Sani Abacha, wanda a lokacin babban jami'in soja ne, sauya gaskiyar tarihi ne da gangan".
Sanarwar ta ƙara da cewa "tsawon shekaru, mutane da dama sun yi kokarin canza tarihin wannan lokacin mai muhimmanci a tarihin dimokraɗiyyar Najeriya, sai dai a cewar su, ba za a iya canza gaskiyar lamarin ba".
Iyalan sun kuma buƙaci ƴan Najeriya su yi taka tsan-tsan da labaran kanzon kurege "waɗanda ake shiryawa domin sauya tunanin mutane saboda dalilan kansu ko na siyasa.
''Ba za mu yarda a lalata tarihin mahaifinmu ba kuma shugaba, Janar Sani Abacha, da wasu zarge zarge marasa tushe domin wanke waɗanɗa ke da alhaki.''
Har ila yau ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin ɗaura mishi laifi, Janar Abacha ya kasance amini ga Janar Ibrahim Babangida har zuwa lokacin mutuwarsa.
''Shi mutumi ne mai matuƙar saduakarwa ga abokansa'' in ji shi.
Ya kuma kara da cewa akwai buƙatar ya bayyana cewa a lokacin da rayuwar Janar Babangida ke cikin barazana, Janar Abacha ne ya cece shi, ya kuma tabbatar da tsaronsa.
Mohammed Abacha ya kuma bayyana godiyarsa ga ƴan Najeriya da suka tsaya tsayin daka wajen kare Janar Sani Abacha a ƙoƙarinsu na fayyace yadda abubuwa su ka faru da kuma hana a sauya tarihi.
Ya ce littafin IBB na 'A journey in service' ya rasa damarsa kuma ya gaza wajen kafa tarihi a matsayin labari kan gaskiyar abin da ya faru a baya.
Baya ga batun zaɓen shugaban ƙasa na watan Yunin 1993, tsohon shugaban ƙasar ya taɓo abubuwa kamar juyin mulkin Najeriya na farko da zamantakewarsa da matarsa, marigayiya Maryam Babangida da kuma kisan aminisa Mamman Vatsa bayan kama shi da laifin kitsa juyin mulki.
Me ya faru a ranar 12 ga Yunin 1993?
A ranar 12 ga wata Yunin 1993, ɗan takarar SDP Abiola ya fafata da ɗan takarar NRC Bashir Tofa a zaɓen shugaban ƙasa. Abokin takarar Abiola shi ne Baba Gana Kingibe, inda Sylvester Ugoh ya zama mataimakin Tofa.
Duk da cewa masu sharhi na ganin zaɓen na 12 ga Yuni ya fi kowanne inganci, sai dai gwamnatin mulkin soja ta Ibrahim Badamasi Babangida ta soke shi bisa zargin maguɗi.
Matakin ya jawo ce-ce-ku-ce kuma daga baya Babangida ya sauka daga mulki a 1993. Ernest Shonekan, wanda ɗan garinsu Abiola ne, ya zama shugaban ƙasa na riƙo.
A ranar 11 ga Yunin 1994, Abiola ya ayyana kan sa a matsayin shugaban ƙasa a Legas, jihar da ke kudu maso yammacin ƙasar. Matakin nasa ya sa gwamnatin Sani Abacha ta soja ta zarge shi da cin amanar ƙasa kuma aka kama shi a ranar 23 ga Yunin 1994.
An tsare Abiola tsawon shekara huɗu, har ma wasu rahotanni na cewa ban da Ƙur'ani da Bibble masu tsarki ba shi da wata hanyar samun wasu bayanai.
Abiola ya rasu ranar 7 ga watan Yulin 1998, ranar da ya kamata a sake shi daga gidan yari.