Man Utd ta dage a kan Osimhen, Barcelona na son Kante da Aubameyang

Victor Osimhen

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Manyan kungiyoyi na son sayen Victor Osimhen na Najeriya daga Napoli

Manchester United ta kara tashi tsaye wajen zawarcin Victor Osimhen bayan da ta tura masu nemo mata 'yan wasa suka duba yanayin dan Najeriyar mai shekara 24 a wasan Napoli na gasar Zakarun Turai a makon da ya gabata. (Star)

Kociyan Celtic Ange Postecoglou ya kasance na baya-bayan nan da Chelsea ke duba yuwuwar dauka, ko da yake har yanzu tsohon kociyan Tottenham Mauricio Pochettino shi ne kan gaba. (Guardian)

Julian Nagelsmann, wanda ya fice daga jerin masu son Chelsea ta dauke su a makon da ya wuce, yana sha'awar zama kociyan Tottenham. (Bild)

Paris St-Germain za ta bar Lionel Messi ya tafi idan kwantiraginsa ya kare a bazara mai zuwa, a shirin da kungiyar ke yi na rage dogaro da manyan taurarin 'yan wasa da kuma mayar da hankali kan renon matasa. (Mirror)

Newcastle na shirin zawarcin dan gaban Barcelona Raphinha na Brazil. (Mundo Deportivo)

Manchester United da Liverpool na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Argentina Alexis Mac Allister daga Brighton. (Fabrizio Romano)

Aston Villa na shirin taya 'yan wasa biyu na Manchester City, dan baya Kyle Walker na Ingila da kuma dan wasan tsakiya Kalvin Phillips shi ma dan Ingila kan fam miliyan 55. (Football Insider)

Ollie Watkins ya amince da sabon kwantiragi na tsawon lokaci a Aston Villa duk da cewa kungiyoyi irin su Arsenal da Tottenham Hotspur da Newcastle United na nuna sha'awarsu a kan dan ingilar mai shekara 27. (Teamtalk)

Barcelona na harin sayen 'yan wasan Chelsea biyu N'Golo Kante da Pierre-Emerick Aubameyang a lokacin bazara. (Mirror)

Akalla 'yan wasan Chelsea 10 ne ke shawara kan zamansu a kungiyar bayan da Real Madrid ta kawo karshen duk wani fata na kungiyar na cin wani kofi da kuma buga wasan Zakarun Turai a kaka mai zuwa. (Standard)

Barcelona ta gudanar da bincike kan 'yan wasa kusan 13 a kokarin da take yi na sayen dan baya na gefen dama a bazara, ciki har da dan Manchester United Diogo Dalot da kuma Joao Cancelo, wanda a yanzu yake zaman aro a Bayern Munich daga Manchester City. (Mundo Deportivo)

Chelsea ta amince ta dauki matashin dana gaba na gefe na Portugal Diego Moreira mai shekara 18, idan kwantiraginsa ya kare da Benfica a bazara. (Record)

Brighton na dab da cimma yarjejeniyar sayen matashin dan bayan Celtic Ronan Ferns dan Scotland mai shekara 16. (Football Insider)