Zaben Osun: Abu biyar da muka koya bayan PDP ta kayar APC

Asalin hoton, PDP/APC
Daga Umar Mikail
Ɗaya daga cikin manyan darussan da zaɓen gwamna a Jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya ya koya wa mahukunta da ma ‘yan Najeriya shi ne; har yanzu jam’iyyar adawa za ta iya kayar da mai mulki kuma babu abin da zai faru.
Wakilinmu Umar Mikail, wanda ya shaida yadda zaben ya gudana a ranar Asabar 16 ga watan Yuni, ya duba darasi biyar da masu riƙe da madafun iko da ma ‘yan ƙasar za su koya daga sakamakonsa.
_________________________________________________
Mutane da dama na ganin cewa duk lokacin da jam’iyyar adawa ta kayar da mai mulki ya tabbata sahihin zaɓe.
Kila haka ne, amma dai zaɓen gwamnan Osun na 2022 ya zo da darussa da dama, ciki har da wanda ‘yan Najeriya kansu za su koya.
A taƙaice dai, ana iya cewa an yi nasarar gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali duk da sayen ƙuri’u da tutsun na’urar tantance masu ƙuri’a da kuma ‘yan daba masu ɗauke da makamai.
Siyasar addini ba ta yi tasiri ba

Asalin hoton, @GboyegaOyetola
Tasirin addini da ƙabilanci na da girma sosai a siyasar Najeriya musamman idan masu kaɗa ƙuri’ar suka fito daga ɓangarori biyu mabambanta irin Jihar Osun.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da cewa jihar Yarabawa ce, al’umommin cikinta sun kasu zuwa mabiya Musulunci da Kirista, kamar yadda ɗan takarar APC kuma gwamna mai-ci Gboyega Oyetola yake Musulmi, shi kuma Ademola Adeleke ya fi mu’amala da Kiristanci, duk da cewa yana hulɗa da dukkan addinan biyu.
Kazalika, mataimakin Adeleke mai suna Kola Adewusi Kirista ne.
Kasancewar Oyetola a matsayin gwamna ɗaya tilo Musulmi a yankin Yarabawa ta sa wasu sun dinga yin kamfe da cewa ‘yan uwansa Musulmai su zaɓe shi, ciki har da Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje wanda ya je Osogbo a matsayin mataimakin shugaban kwamatin kamfe na APC.
“Mun zo mu roƙi ‘yan uwa Musulmi su zaɓe shi [Oyetola]...saboda shi kaɗai ne gwamna Musulmi a yankin kudu maso yamma.
"Ka san an ce idan ana bikin balbela ba sai an gayyaci farar kaza ba,” kamar yadda ya shaida wa BBC bayan ya yi Sallar Juma’a a masallcin Juma’a da ke unguwar Sabo, inda ‘yan Arewa ke da yawa.
Hatta mazaɓu biyu mafiya kusa da inda Ganduje ya ziyarta raba ƙuri’a aka yi tsakanin APC da PDP, inda kowacce ta lashe mazaɓa ɗaya.
Duk da cewa babu wasu alƙaluma da ke tabbatar da cewa Musulmai sun fi Kiristoci yawa a Jihar Osun, ana yi wa jihar kallon wadda Musulman suka fi rinjaye.
Tsohon mai bai wa gwamna shawara kan ƙabilu mazauna Osun, Imam Muhammad Bashir, ya ce rikiicin cikin gida ne ya kayar da jam’iyyar tasu sakamakon yadda ba a jituwa tsakanin tsohon gwamna kuma Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola da Gwamna Oyetola.
Cinikin ƙuri’a ya gagari hukumomi

Yayin da masu sa ido kan zaɓuka a Najeriya ke murnar zaɓuka sun fara kyautata a ƙasar, sai kuma ga matsalar sayen ƙuri’a na mamaye zaɓukan da ake kallo a matsayin mafiya inganci a tarihin ƙasar.
Ƙungiyoyi da cibiyoyi da suka bibiyi zaɓen Osun sun tabbatar da cewa an tafka cinikin ƙuri’u a ranar zaɓen kamar dai yadda aka yi a zaben gwamnan Jihar Ekiti na ranar 18 ga watan Yunin 2022, wadda ita ma ke a kudu maso yamma.
Shaidu sun nuna cewa wakilan jam’iyyun PDP da APC ne kan gaba wajen cinikin ƙuri’a a zaɓen na ranar Asabar.
Wata mace mai matsakaicin shekaru ta faɗa mana cewa wani gungun mutane sun yi mata duka a birnin Osogbo saboda ba ta biya su kuɗin jefa ƙuri’a da ta yi musu alƙawari ba – bayan ta ɗauki sunayensu da zimmar za a biya su ida suka zaɓi jam’iyyar da take wakilta.
Tun gabanin kaɗa ƙuri’a wani matashi mai suna Mustapha Akibu ya faɗa wa tagawar BBC cewa ba lallai ya kaɗa ƙuri’a ba idan ba a ba shi kuɗi ba.
“Zaɓen namu yanzu a Najeriya ya sauya, ko da ka yi saboda Allah shirme ake ɗaukarsa. Don haka gara a ba ni kuɗi sai na je na jefa ƙuri’a tun da dai ana ba da kuɗin,” in ji shi.
Duka wannan na faruwa ne yayin da hukumomi ke ƙara azama wajen yaƙi da sayen ƙuri’a.
Misali, tun kafin zaɓen hukumar tsaron ‘yan ƙasa ta Civil Defense ta ce ta kafa ruduna ta musamman don yaƙi da cinikin ƙuri’a.
Kazalika, EFCC mai yaƙi da rashawa ta tura dakarunta don hana cinikayyar.
Bugu da ƙari, ita ma ICPC mai yaƙi da almundahana ta ce jami’anta sun kama mutum uku da zargin sayen ƙuri’a a rumfunan zaɓe uku daban-daban, ciki har da wanda ‘yan daba suka far wa ma’aikatanta.
Hakan na nufin hukumomin yaƙi da rashawa na da babban aiki a gabansu na yaƙi da sayen ƙuri’a a zaɓuka masu zuwa.
‘Sakamakon zaɓen ba manuniya ba ce a 2023’
Jim kaɗan bayan Inec ta ayyana PDP a matsayin wadda ta lashe zaɓen na Osun, magoya bayanta suka dinga bugar ƙirji cewa manuniya ce kan abin da zai faru a babban zaɓe na 2023 mai zuwa.
An ga ‘yan takarar shugaban ƙasa na PDP da APC, Atiku Abubakar da Bola Tinubu, suna gaisawa da juna a Osun bayan kowannensu ya taya ɗan takararsu kamfe a manyan tarukan da suka gudanar.
Sai dai masu sharhi na nuna shakku kan wannan iƙirari ganin cewa Najeriya na da jihohi 36 da kuma Abuja bayan Osun.
“Gaskiya duk wanda ya ce wannan sakamakon manuniya ce kan 2023 bai taki gaskiya ba, saboda muna da jiha 36 a Najeriya da kuma Abuja,” in ji Farfesa Abubakar Mu’zu na Sashen Aikin Jarida a Jami’ar Maiduguri.
“Ba mu san yadda siyasa za ta kaya a wasu jihohin ba sannan kuma wannan sakamakon zai koya wa ‘yan siyasa darasi a wasu yankunan Najeriya.”
Kowa ya yi da kyau zai ga da kyau

Asalin hoton, Yiaga Africa
A shekarun baya kamar yadda aka saba gani a zaɓukan da suka gabata a Najeriya, akan shafe rabin yini kayan zaɓe ba su isa rumfunan kaɗa ƙuri’a ba a wasu mazaɓun bisa wasu dalilai.
Sai dai lokacin da na isa hedikwatar hukumar zaɓe ta Inec reshen Jihar Osun a birnin Osogbo da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Alhamis, na tarar an tura fiye da rabin kayayyakin zaɓe mafiya muhimmanci zuwa ƙananan hukumomin jihar da ke da nisa.
Hasali ma, kayan zaɓe na ƙaramar hukuma shida kacal daga cikin 30 na tarar waɗanda ba su riga sun kama hanya ba, kuma su ma na ga ana shirin tura su a lokacin.
A taƙaice dai, tun a ranar Alhamis Inec ta kammala tura kayayyakin zaɓe zuwa dukkan ƙananan hukumomi 30 na Osun, saɓanin na zaɓen Ekiti wanda har sai ranar Juma’a aka kammala tura su.
Ya zuwa ƙarfe 7:30 na safiyar ranar zaɓe, ma’aikatan Inec da kayayyakin zaɓe sun isa kashi 77 cikin 100 na rumfunan zaɓe a faɗin Osun, a cewar cibiyar Yiaga Africa.
Ya zuwa 8:30 kashi 41 sun fara tantance masu zaɓe da kuma kaɗa ƙuri’a. Ya zuwa ƙarfe 9:30 kuma an fara jefa ƙuri’a a kashi 96 cikin 100 na rumfunan zaɓen jihar.
Duk da cewa zaɓen ba na ƙasa ba ne baki ɗaya, hakan na nufin idan aka shuka abin da ya dace za a girbi abin da ya dace.
Idan abu ya yi kyau kowa zai alfahari

A kowace rumfar zaɓe da muka ziyarta akwai jami’an tsaro fiye da ɗaya hatta a rumfar zaɓe mai mutum 31 kacal.
A mafi yawan rumfunan zaɓen mun ga rundunar haɗin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da kuma Civili Defense, har ma da jami’an kiyaye haɗurra.
A rumfar zaɓe mai suna Open Space da ke Owode I a birnin Osogbo – wadda ke cikin sababbi da Inec ta ƙirƙiro – mun ga ɗan sanda da kuma ‘yar Civil Defense.
Mataimakin sufeton ‘yan sandan Najeriya mai kula da tsaro a zaɓen Osun, Johnson Kokumo, ya ce dakaru 21,000 aka tura jihar don gudanar da aikin tsaro yayin zaɓen.
Wannan ta sa mai magana da yawun rundunar na ƙasa, Olumuyiwa Adejobi, ya yi alfaharin cewa sun cika alƙawarin da suka ɗauka “tabbatar da sahihin kuma karɓaɓɓen zaɓe cikin kwanciyar hankali” a Osun.
“Na tabbata mutane da yawa za su bi sahun ‘yan Najeriya mutanen kirki wajen yaba mana da sauran jami’an tsaro saboda zaɓe mai cike da kwanciyar hankali a Osun,” in ji shi cikin wani saƙon Twitter da ya wallafa.











