Su wane ƴan addinin Baha'i masu da'awar zuwan annabin zamani?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, وليد بدران
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بي بي سي
- Lokacin karatu: Minti 9
An haifi Muhammad Ali Shirazi da ake kira "Bab" a ranar ɗaya ga watan Muharram na shekara 1235 bayan hijira, wato 20 ga watan Oktoban 1819 miladiyyar Annabi Isa.
Ya yi iƙirarin samar da wani addini wanda wani annabi zai zo domin ci gaba da kawo saƙo daga wurin mahalicci, kuma annabin zai kasance daga jerin annabawa irin su Musa da Isa da kuma Annabi Muhammad.
Sai dai Bab da mabiyansa sun sha uƙuba daga hukumomin Qajar, da ke cikin ƙasar Iran a yanzu.
Rubuce-rubuce na tarihi sun bayyana cewa Bab ya fara da'awarsa ne da mutum 18 kacal, waɗanda suka riƙa yaɗa da'awar tasa a yankuna da dama a yankin ƙasar Iran zuwa Iraqi, inda suke wa mutane wa'azin zuwan sabon wahayi.
Wa'azinsa ya ci gaba har zuwa kimanin shekara shida, kuma ayyukansa sun haifar da damuwa tsakanin shugabannin siyasa da na addini, wanda a sanadiyyar haka ne aka sha kama shi, bayan da aka riƙa samun takun saƙa tsakanin mabiyansa da hukumomi.
Wa'azin Bab ya ci karo da na addinin Musulunci wanda ya bayyana annabi Muhammad a matsayin na ƙarshe.
Sai dai a tasa koyarwar, ya ce kowane zamani na zuwa da annabinsa kuma ana sabunta koyarwar addini ne ta hanyar turo annabawan da ke gadar wadanda suka gabace su.
Yayin da da'awar Bab ta riƙa haɓɓaka, inda daga baya suka ayyana kansu a matsayin addini mai zaman kansa, sai hukumomin ƙasar Iran suka yanke hukuncin kisa a kan Bab.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An zartar masa da hukuncin ta hanyar harbe shi da bindiga a garin Tabriz a shekara ta 1850, bisa umarnin Firaiminista Mirza Taqi Khan.
Bayan zartar masa da hukuncin kisa an ɓoye gawarsa tsawon sama da shekara 50, har sai lokacin da aka mayar da gawar zuwa yanki mai yawan tuddai na 'Mount Carmel' da ke Haifa a shekarar 1909, wanda a lokacin ke ƙarƙashin ikon Daular Ottoman.
A can ne aka gina masa wani ƙawataccen hubbare, wanda ya zama ɗaya daga cikin wurare uku masu tsarki ga mabiya addinin Baha'i, inda mabiya ke zuwa ziyarar ibada daga sassa daban-daban na duniya.
A yanzu haka dukkanin wurare masu tsarki guda uku na mabiya addinin Baha'i suna a ƙasar Isra'ila ne: Hubbaren Bab da ke a gangaren tuddan Carmel a Haifa, da Hubbaren Baha'ullah da ke Acre sai kuma Hubbaren ƴaƴansa maza Abdul-Baha da ke a birnin.
A shekarar 1852, ɗaya daga cikin mabiya Bab, Mirza Husayn Ali, wanda aka haifa a shekarar 1917 a Persia, a lokacin da yake zama a gidan yari, ya ce ya yi mafarkin cewa shi ne annabin da Bab ya yi bushara da zuwan sa, inda ya laƙaba wa kansa sunan "Baha'ullah."
A shekarar 1863, Baha'ullah ya yi iƙirarin annabta a birnin Baghdad, tare da kafa addinin Baha'i, wanda ya yaɗu zuwa sassa da dama na duniya.
Bahá'u'lláh da sahabbansa

Asalin hoton, Getty Images
Kundin bayanai na Encyclopædia Britannica, ya ce Baha'i addini ne da ya bazu a duniya, wanda Mirza Husayn-Ali Nuri, wanda ake kira "Baha'ullah ya samar a tsakiyar ƙarni na 19.
Ya fara ne a matsayin ƙungiya a ƙasar Iran, kafin daga bisani Baha'ullah ya ayyana shi a matsayin addini mai zaman kansa a lokacin da yake zama a Iraqi.
Da'awarsa ta zo ne a wani lokaci mai sarƙaƙiya na siyasa, bayan da aka kore shi daga Persia zuwa Daular Ottoman sanadiyyar matsi daga hukumomi.
Hijirarsa ta fara ne daga Baghdad, zuwa Istanbul kafin yada zango a birnin Acre na yankin Falasɗinu da ke ƙarƙashin Daular Ottoman, har zuwa ƙarshen rayuwarsa a shekarar 1892.
Lokacin da yake gudun hijira, Baha'ullah ya yi rubuta maƙaloli da litattafai wadanda suka zamo tamkar tubalin gina koyarwar addinin Baha'i, ɗaya daga cikin litattafan da suka shahara shi ne Kitab-i-Aqdas, wanda ya zamo littafin dokokin mabiya addinin Baha'i.
Bayan mutuwar jagoran addinin, sai ɗansa Abbas Effendi, wanda aka fi sani da "Abdul-Baha" ya karɓi jagorancin addinin, inda ya ɗaukaka koyarwar mahaifinsa, kuma ya taimaka wajen yaɗuwar addinin zuwa ƙasashen Yamma.
Lokacin da ya kai ziyara ƙasashen Turai da Amurka a farkon ƙarni na 20, Abdul-Baha ya gabatar da Baha'i a matsayin addinin da ke kira ga haɗin kan addinai da kuma tafiya da dukkanin al'umma.
Bayan mutuwarsa a 1921, sai jikansa Shongi Effendi ya karɓi ragamar addinin, inda ya zamanantar da shi tare da tsara yadda ake tafiyar da lamurran addinin a yanzu.
Bayan mutuwar Shonghi Effendi ba tare da barin magaji ba a shekarar 1957, sai shugabancin addinin ya karɓi ragamar tafiyar da addinin.
An kafa wannan majalisa ce a shekarar 1963 a birnin Haifa a matsayin cibiya ta ƙoli da aka ɗora wa alhakin jagorantar mabiya addinin Baha'i da kuma samar da manufofinsu.
Majalisar ƙoli ta Baha'i ta ƙunshi wakilai tara, waɗanda ake zaɓowa a cikin kowace shekara biyar daga ƙasashe daban-daban na duniya. Wannan majalisa ita ce ke lura da al'amuran Baha'i a faɗin duniya, inda take shiryar da mabiya kan tafarkin cimma manufofin addinin.
Imaninsu

Asalin hoton, Getty Images
Addnin Bahá'í ya dogara ne a kan imanin cewa Bahá'u'lláh da magabatansa, Báb, abubuwa ne biyu na wani abin halitta da kuma zatin Allah, wanda tunanin dan'adam ba zai iya cikakkiyar fahimta ba.
A bangaren tauhidi, mabiyan addinin Baha'i sun yi imani cewa Allah daya ne wanda ba za a iya fahimtar buwayar zatinsa ba, amma ana iya gane siffofinsa ta hanyar abin da ake kira "Sigogin Ubangiji," wato, annabawa da manzonni wadanda kan zo zamani bayan zamani a tarihi gwargwadon bukatun dan'adam.
Mabiya addinin Baha'i na ganin wahayi abu ne da ke ci gaba da gudana, inda yake sauya fasali a kan cikar kamalar mutum bisa la'akari da shekaru, ta yadda kowanne wahayi, zai kasance dorawa yake a kan abin da ya gabata da kuma wani sabon lamari daidai da bukatun wannan zamani.
Shika-shikan akidojin Addinin Baha'i sun dogara ne a kan hada kan addinai da hadin kan bil'adama.
Mabiya addinin Baha'i sun yi imanin cewa dukkan wadanda suka zo da manyan addinai – kamar Musa da Isah da Muhammad da Krishna da Buddha – sigogin Allah ne kuma manzonnin wani kudurin mahalicci ne ga tsarkake ruhi da tarbiyya da kuma ci gaban bil'adama a tsawon tarihi.
Daga wannan mahanga, mabiyan Baha'i ba sa daukar kansu daban da sauran addinan da suka rigaya, maimakon haka suna ganin addininsu ne a matsayin wata sabuwar mahada da ke isar da ci gaban wahayin da akan saukar. Suna bayyana haka ne ta hanyar azancin "hada saukar wahayi", ma'ana ita ce duk annabawa tushensu daya ne kuma su siffa ce ta ruhin gaskiya daya, duk da bambance-bambancensu a tsawon zamani da al'adu.
Mabiya addinin Baha'i sun yi imanin cewa, aiki na musamman da aka aiko Baha'u'llah a ban kasa shi ne ya yi yaki da rarrabuwar kai tsakanin addinai kuma ya kafa wani tafarki na hadin kai da ya karade duk fadin duniya da kuma dukkan mutane.
Sun kuma yi imani cewa dan'adam daya ne kuma suna aiki don kakkabe bambancin launin fata da addinai da aji, tare da fifita zaman lafiyar duniya.
Daidaito da zaman lafiya

Asalin hoton, Getty Images
Mabiya Addinin Bahá'í sun yi imani a kan cikakken daidaito tsakanin jinsin maza da mata da kuma wajabcin ba da ilmi dole ga kowa.
Suna kuma kira a kawar da tsananin talauci da kuma tsananin arziki, sannan suna karfafa gwiwa neman gaskiya ba tare da shamaki ba, kuma suna tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.
Rubuce-rubucen 'yan Baha'i na nuna wa karara cewa babban burin addininsu shi ne cimma zaman lafiya a fadin duniya da hada kan dan'adam bisa wani tsari na zaman adalci.
A cewar Kundun Kalmomi na Encyclopædia Britannica, 'yan Baha'i sun yi imani cewa dan'adam a yanzu yana fuskantar wani sauyin rayuwa ne daga yarinta zuwa balaga, kuma rikice-rikice da yake-yake wani bangaren rayuwa ne mai zafi amma da ya zama dole na kai wa ga hadin kan al'ummar duniya.
Addinin Baha'i bai yarda da tsarin manyan limamai ba. Babu wani rukunin addini da ke raba mutum da Ubangijinsa.

Asalin hoton, Getty Images
Mafi girman koyarwar addinin shi ne kyautata dabi'un kwarai tsakanin al'umma da kuma gina wani tsarin taimakekeniya da sanin ciwon kan mutum.
A fannin halayya, Addinin Baha'i na kira ga mutum ya kyautata da'ar kansa kuma ya kasance mai hidima ga al'umma, sannan yana karfafa gwiwar tsare gaskiya da amana da hakurin zaman tare da aiki tukuru da mutunta doka.
Sai dai an haramta shan barasa da kwaya da caca.
Addinin yana bai wa rayuwar iyali muhimmanci a matsayin wani ginshikin al'umma, inda yake karfafa gwiwar auren mace daya bisa tushen kauna da fahimta. Ana ba da izinin saki ne kawai a wani yanayi na musamman da kuma bayan shafe tsawon shekara daya ana kokarin sasantawa.
Ibada da zahirin addini

Asalin hoton, Getty Images
Ibadar mabiya addinin Baha'i na da sauki idan an kwatanta da na sauran addinai. Ana ganin sallah a Addinin Baha'i a matsayin wata hanyar sadarwa kai tsaye da Allah, kuma tana daya daga cikin shika-shikan bauta ga mabiyi.
Duk dan Baha'i ana bukatar ya yi daya daga cikin salloli uku na rana: gajera, matsakaiciya da kuma doguwar salla. Ana iya zabar kowaccensu a rika yin ta kullum.
Sallar 'yan Baha'i na mayar da hankali ne a kan ayyukan ibada da karfafa dabi'u na kwarai kamar tsare gaskiya da hidimta wa sauran jama'a, babu tsawwalawa ana iya yin sallar a ko'ina kamar a gida ko a wurin bautar mabiya kai ko ma a sararin Allah ba tare da bukatar wani abu na musamman ba.
Ana hada ta da sauran ibadu kamar azumi a watan Ala, lokacin da baligai ke kaurace wa cin abinci da abin sha tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana don kara kusanci da Allah da tsarkake zukatansu.
Watan Ala, shi ne na karshe a shekarar Baha'i.
'Yan Baha'i kuma sun yi imani cewa gaskiyar addini ba kafaffen abu ba ne, sannan ci gaban kimiyya da basira ba sa cin karo da addini. maimakon haka dukkansu hanyoyi ne na neman sanin gaskiya.
Baha'is

Asalin hoton, Getty Images
A jimillance, mabiya Addinin Baha'i a yau sun kai kiyasin miliyan 5 zuwa 6 a fadin kasashe da al'ummomi fiye da 200 na duniya, lamarin da ya sa addinin ya zama daya daga cikin mafi bazuwa a tsakanin al'umma bayan Kiristanci.
Ana samun 'yan Baha'i mafi yawa a Indiya da Afirka da Latin Amurka da wani gwaggwaban adadi a Amurka da Kanada.
Duk da fadin bazuwar Addinin Baha'i, har yanzu yana fuskantar kalubale wajen samun karbuwa a shari'ance a wasu kasashen Musulunci.
Bukukuwan 'yan Baha'i

Asalin hoton, Getty Images
Shekarar addinin Bahá'í ta kunshi wata 19, kowanne wata na dauke da kwana 19 da sabanin kwana hudu ko biyar, wadanda aka fi sani da "Kwanakin Hā'i," da akan kara don karrama baki da ayyukan jin kai da kuma bukukuwa.
Nan kasa ga jerin ranakun bukukuwan Baha'i:
Biki mafi girman daraja shi ne kwana 19 na azumin da akan fara daga 2 ga watan Maris.
Sai bikin Nowruz a ranar 21 ga watan Maris
Eid al-Ridwan daga ranar 21 ga watan Afrilu zuwa 2 ga watan Mayu
Sallama gida - gida 22 zuwa 23 ga watan Mayu
Hawan Bahá'u'lláh ranar 29 ga watan Mayu
Shahadar Báb ranar 9 ga watan Yuli
Haihuwar Báb ranar 20 ga watan Oktoba











