Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa wasu ƙasashe ba su amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa ba?
Yayin wata sanarwar haɗin gwiwa ranar Laraba, ƙasashen Sifaniya, da Norway, da Ireland suka bayyana shirinsu na amincewa da ƙasar Falasɗinawa mai cin gashin kanta a ranar 28 ga watan Mayu.
Shugabannin Falasɗinu sun yi maraba da wanna mataki, har ma hukumar Falasɗinwa ta PLO ta siffanta shi da "lokaci mai cike da tarihi".
Ƙasashen da suke goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinawa na da imanin cewa hakan zai taimaka wajen ciyar da tattaunawar zaman lafiya gaba tsakanin Isra'ila da Falasɗinawan.
Sai dai kuma, Isra'ila ta mayar da martani cikin fushi tana mai cewa za ta gayyaci jakadun ƙasashen uku don ta nuna musu bidiyon hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba da mayaƙan Hamas suka kai cikin ƙasarta.
"Tarihi ba zai manta ba cewa Sifaniya, da Norway, da Ireland sun yanke shawarar saka wa mayaƙan Hamas da kyautar zinariya," a cewar Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Israel Katz.
Isra'ila ba ta amince da kafa ƙasar Falasɗinawa ba kuma gwamnatin da ke mulki a yanzu na adawa da yin hakan a yankun Gaza da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan. Tana iƙirarin cewa bai wa Falasɗinawa ƙasa mai 'yanci barazana ce ga tsaronta.
A watan Afrilu ne Kwamitin Tsaro na MDD ya kaɗa kuri'a kan buƙatar Falasɗinawa ta zama mamba na Majalisar Ɗinkin Duniya.
An buƙaci majalisar mai wakilai 15 da ta kaɗa kuri'a kan daftarin kudurin da Aljeriya ta gabatar, wanda ya ba da shawarar ga mambobi 193 na MDD cewa "a amince da ƙasar Falasɗinu a matsayin mamba a Majalisar".
Ƙasashe biyar ne ke da wakilci na dindindin a Kwamitin Tsaron, kuma kowannensu yana da 'yancin kaɗa kuri'a. Suna aiki tare da ƙasashe 10 da ba na dindindin ba.
Idan da kwamitin tsaron ya zartar da wannan kuduri, to da majalisar ta kaɗa kuri'a a kansa, kuma da kashi biyu bisa uku zai bai wa Falasdinu damar zama mamba.
Amurka, wadda ta kasance ƙawa ga Isra'ila na tsawon lokaci, ta ki amincewa da matakin a kwamitin tsaron.
Za a iya zartar da kudurori na MDD ne kawai idan babu ɗaya daga cikin ƙasashe biyar na dindindin - Amurka, Burtaniya, Faransa, Rasha ko China - wanda ya ki amincewa da su.
Bayan da aka kaɗa kuri'ar, mataimakin jakadan Amurka a MDD, Robert Wood ya shaida wa majalisar cewa: Amurka na ci gaba da bayar da cikakken goyon baya ga samar da ƙasashe biyu. Wannan kuri'ar ba ta nuna adawa da ƙasar Falasɗinu ba, a maimakon haka wata amincewa ce kawai za ta zo daga tattaunawa tsakanin ɓangarorin."
Wane matsayi yankunan Falasɗinawa suke da shi a MDD?
Falasɗinawa dai na rike da matsayin ƙasar da ba mamba ba a Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
A shekara ta 2011, Falasɗinu ta gabatar da buƙatar zama cikakkiyar mamba a MDD, amma hakan ya ci tura saboda rashin goyon bayan kwamitin tsaro na MDD kuma ba a taɓa jefa kuri'a ba.
Sai dai a shekara ta 2012, babban taron MDD ya kaɗa kuri'ar ɗaukaka matsayin Falasɗinawa zuwa matsayin "ƙasa mai sa ido", wanda ke ba su damar shiga muhawarar majalisar, ko da yake ba za su iya kaɗa kuri'a kan kudurori ba.
Shawarar ta 2012 - wadda aka yi maraba da ita a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Zirin Gaza, amma Amurka da Isra'ila suka yi suka - ta kuma ba wa Falasɗinawa damar shiga wasu ƙungiyoyin kasa da kasa, ciki har da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, wadda suka yi a shekarar 2015.
"Zama cikakken mamba na MDD zai bai wa Falasɗinawa ƙarin karfin diflomasiyya, wanda ya kunshi ikon ɗaukar nauyin kudurori kai-tsaye, kuri'a a zauren Majalisar (a matsayin 'kasa ba mamba' ba, wanda ba su da shi a halin yanzu) daga karshe yiwuwar samun kujera ko kaɗa kuri'a a kwamitin tsaro," in ji Khaled Elgindy, darektan shiri kan Falasɗinu da Isra'ila a cibiyar nazarin Gabas Ta Tsakiya da ke Washington.
Ya ƙara da cewa "Amma babu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da za su samar da mafita ta ƙasashe biyu - wanda zai iya faruwa ne ta hanyar kawo karshen mamayar Isra'ila."
Ko da a ce zaɓen na ranar Alhamis ya tafi yadda ya kamata, "Hukumar Falasɗinu ba za ta cimma wani abin da ya fi haka ba", in ji Gilbert Achcar, farfesa a fannin nazarin raya kasa da hulɗar ƙasa da ƙasa a Makarantar Nazarin Gabas da Afirka da ke Landan.
"Zai kasance babban alama ta nasara: amincewa da 'Ƙasar Falasɗinu' da gaskiyar 'Hukumar Falasɗinu' mara ƙarfi a kan ƙaramin yanki na yankunan da aka mamaye a 1967 kuma sun dogara da Isra'ila gaba-ɗaya," in ji shi.
Su wane ne suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa?
Wasu ƙasashe 140 ne suka amince da ƙasar Falasdinu, ciki har da mambobin ƙungiyar Larabawa a Majalisar Ɗinkin Duniya, ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Musulmi, da kuma mambobi masu zaman kansu.
Amma wasu ƙasashe da yawa - ciki har da Amurka, Birtaniya, Faransa, Jamus da Ostiraliya - ba su amince ba.
Duk da haka, a makon da ya gabata, Ostiraliya ta ce za ta iya amincewa da ƙasar Falasɗinu, don "ba da dama ga samar da ƙasashe biyu" da aka kulla da Isra'ila.
Kuma a watan da ya gabata, shugabannin ƙasashen Sifaniya, Ireland, Malta, da Slovenia, sun fitar da wata sanarwa a gefen taron shugabannin ƙungiyar Tarayyar Turai, inda suka ce, za su yi ƙoƙarin ganin an amince da ƙasar Falasɗinu, a lokacin da “alamura suka yi daidai”.
"Duk da haka, wannan zai zama tambaya," a cewar Hugh Lovatt, babban jami'i a shirin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka a Majalisar Turai kan Harkokin Waje.
"Idan har yanzu Amurka ta toshe hanyar MDD, shin wasu mambobi, musamman ma ƙasashen Turai, za su ci gaba ta hanyar ɓangarorin biyu don amincewa da Falasɗinu?" Ya tambaya.
Me ya sa wasu ƙasashe ba su amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa ba?
Ƙasashen da ba su amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa ba gaba-ɗaya ba sun yi haka ne saboda babu wata yarjejeniya da Isra'ila.
"Duk da cewa ta yi watsi da buƙatar kafa ƙasar Falasɗinu, amma Amurka ta dage kan yin shawarwari kai-tsaye tsakanin Isra'ila da Falasɗinu, wanda hakan ke nufin bai wa Isra'ila kuri'ar kin amincewa da buƙatar 'yancin kai," a cewar Fawaz Gerges, farfesa a fannin hulɗar ƙasa da ƙasa da siyasar Gabas ta Tsakiya a Makarantar Tattalin Arziki ta London.
Tun a shekarun 1990 ne aka fara tattaunawar zaman lafiya, inda daga baya aka tsara manufar samar da ƙasashe biyu, inda Isra'ila da Falasɗinawa za su zauna kafaɗa da kafaɗa a ƙasashe daban-daban.
Duk da haka, tsarin zaman lafiyar ya fara raguwa a hankali tun farkon shekarun 2000 tun kafin 2014, lokacin da tattaunawar ta ƙasa samun nasara tsakanin Isra'ila da Falasɗinu a Washington.
Batutuwan da suka fi ɗaukar hankali har yanzu ba a warware su ba, waɗanda suka haɗa da iyakoki da yanayin ƙasar Falasɗinu a nan gaba, matsayin birnin Kudus, da makomar 'yan gudun hijirar Falasɗinawa daga yaƙin 1948-1949 da ya biyo bayan ayyana kafa ƙasar Isra'ila.
Isra'ila ta yi kakkausar suka ga yunkurin Falasɗinawa na zama mamba a Majalisar Ɗinkin Duniya.
Jakadan Isra'ila a MDD Gilad Erdan ya faƊa a farkon watan Afrilu cewa tattaunawar da ake yi ta riga ta zama nasara ga ta'addancin kisan kare dangi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito, ya kuma ƙara da cewa yunkurin da aka yi cikin nasara zai zama tukuicin ta'addanci a harin rnar 7 ga Oktoba da Hamas ta kai.
Ƙasashen da ke da niyyar ci gaba da kyakkyawar alaƙa da Isra'ila za su san cewa amincewa da ƙasar Falasdinu zai fusata ƙawayen nasu.
Wasu, ciki har da masu goyon bayan Isra'ila, suna jayayya cewa Falasɗinawan ba su dace da mahimman ka'idojin ƙasa da ƙasa da aka ayyana a cikin yarjejeniyar Montevideo na 1933 ba - yawan jama'a na dindindin, yanki da aka ayyana, gwamnati da kuma ikon shiga dangantaka da wasu ƙasashe.
Amma wasu sun yarda da ma'anar da ta fi dacewa, tare da ƙarin girmamawa ga amincewa da wasu ƙasashe.