Muna gargaɗin gwamnan Kano da ka da ya gudanar da zaɓe - APC

Asalin hoton, Facebook/Alfindiƙi
Shugaban jam'iyyar APC mai adawa a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya gargaɗi gwamna Abba Kabir Yusuf da ka da ya kuskura ya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi "kamar yadda wata kotu bayar da umarni."
A wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ranar Juma'a a Abuja, Abdullahi Abbas ya ce ya kamata gwamna Kabir Yusuf ya san cewa idan har ya ci gaba da gudanar da zaɓen na to "tamkar ya gayyato rashin zaman lafiya ne a jihar ta Kano."
"Kawai gwamna ya bi umarnin kotu. A matsayinmu na masu son bin doka da oda da kuma son cigaban jiharmu ta Kano, dole ne gwamna ya guji duk abin da ka iya jefa jihar tamu cikin ruɗani." In ji Abdullahi Abbas.
Wata kotun ta umarci hukumar zaɓe ta Kano ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi

Asalin hoton, FACEBOOK
Babbar kotun jihar Kano ta umarci hukumar zaɓe ta jihar ta ci gaba da shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da ta shirya yi ranar Asabar, bayan wata kotun ta hana yin hakan.
Hukuncin kotun ta jiha na zuwa ne bayan na babbar kotun tarayya ƙarƙashin Mai Shari'a Simon Amobeda, wanda ya amince cewa shugabannin hukumar zaɓen Kano wato Kano State Independent Electoral Commision (Kansiec) ƴan jam’iyyar NNPP ne mai mulkin jihar.
Lauyan da yake wakiltar hukumar zaɓe, Muntari Garba Ɗandago, ya faɗa wa manema labarai cewa kotun ƙarƙashin Mai Shari'a Sanusi Ma'aji ta ce babu hujjar da ke tabbatar da cewa shugabannin Kansiec 'yansiyasa ne.
Kazalika, alƙalin ya umarci jami'an tsaro su shiga aikin zaɓen wajen ba da tsaro, saɓanin sanarwar da suka fitar cewa za su bi umarnin kotun farko.
Sai dai lauyan da ke kare jam'iyyar APC mai adawa ya ce hukuncin da kotun ta yi yanzu ba shi ne abin da suke ƙalubalanta ba da ma, yana mai cewa suna ƙalubalantar shugabancin hukumar zaɓe ne ba haƙƙinta na gudanar da zaɓe ba.
Ya ce za su koma su nazarci hukuncin domin ɗaukar mataki na gaba.
A cewar Mai Shari'a Ma'aji, tsarin mulki ne ya bai wa Kansiec damar gudanarwa, da saka ido, kan zaɓen ƙananan hukumomi, kuma duk wani yunƙuri na daƙile hakan ya saɓa wa doka.
Hukuncin kotun farko
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar Talatar da ta gataba ne wata babbar kotun tarayya a Kano ta rushe shugabancin hukumar zaɓen jihar bayan wani mai suna Aminu Tiga ya shigar da Kansiec da wasu 13 ƙara.
Alƙalin ya bayar da umarnin rushe shugabannin hukumar, sannan ya buƙaci a naɗa wasu kafin a gudanar da z
An samu irin haka a jihar Rivers da ke kudancin ƙasar, inda kotu ta ce a dakata da zaɓen, sannan ta buƙaci jami'an tsaro su guji shiga zaɓen.
Sai gwamnan jihar da hukumar zaɓen jihar sun gudanar da zaɓen, abin ya jawo rikice-rikice kafin da kuma bayan zaɓen - ciki har da musayar yawu tsakanin gwamnan jihar da ƴansanda, wanda ya sa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya saka baki.
Jam'iyyar adawa ta NNPP ce ke mulkin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, kuma ita ce kaɗai ce jihar da jam'iyyar take da kujerar gwamna a ƙasar da ta lashe a zaɓen 2023.
Tuni babbar jam'iyyar adawa a jihar ta APC ta sanar cewa ba za ta shiga zaɓen ba, inda take zargin gwamnatin NNPP da tsawwala kuɗin sayen fom ɗin takara.
Hukumar zaɓe Kansec ta sanar da naira miliyan 10 a matsayin kuɗin fom ɗin takara na shugaban ƙaramar hukuma, da kuma miliyan biyar ga duk wanda ke son yin takarar kansila.
Matakin jami'an tsaro kafin sabon hukuncin kotu

Asalin hoton, Abdullahi Haruna Kiyawa/Facebook
Tun da farko kakakin rundunar ƴansandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar da sanarwa cewa sun samu hukuncin kotu da ta buƙaci su koma gefe a ranar zaɓen.
Kiyawa ya wallafa wani hoto a shafinsa na Facebook, sannan ya rubuta cewa: “Ranar 23/10/2024 da jami'an tsaro suka kammala shirin bayar da tsaro, da tsara jadawalin jami'an da za a tura a kowacce akwati na zaɓen ƙananan hukumomi mai zuwa, sai ga umarnin kotu cewa kada mu shiga zaɓen. "To mun bi umarnin kotun, amma fa za mu fito domin tabbatar da tsaro."
A wani faifan bidiyo da ya fitar daga bisani, Kiyawa ya ƙara da cewa kwamishinan ƴansanda jihar Kano, Salman Dogo Garba, ya umarci ƴansanda su fito domin tabbatar da tsaro da rayuwa da dukiyar al’umma.
Hukumar zaɓen Kano ta ce zaɓe babu fashi

Asalin hoton, Sani Lawal/Facebook
Wasu kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun ruwaito hukumar zaɓen jihar Kano na jaddada matsayar da gwamnatin jihar ta ɗauka na gudanar da zaɓen ranar Asabar.
Rahotonnin sun ambato hukumar na cewa za ta yi amfani da ƴan jami'an hukumar kiyaye dokokin tuƙi ta Kano mai suna Karota, da na hukumar Hisba domin samar da tsaro a lokacin zaɓen.
Sai dai a nasa ɓangaren, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce "babu mutumin da ya isa ya hana mu gudanar da zaɓe a jihar Kano".
Gwamnan ya zargi wasu waɗanda ya bayyana da "maƙiyan Kano da ke son jawo tsaiko a gudanar da zaɓen".
Ya ce: "Gwamnatin Kano da hukumar zaɓe duka ba mu saɓa kowacce ƙa'ida ba, saboda haka muna kan turba kuma za mu yi zaɓe cikin lafiya da lumana."










