Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsayar Hamas kan daftarin zaman lafiya a Gaza
Hamas ta amince ta saki dukkan ƴan Isra'ila da ta yi garkuwa da su, amma ta bayar da sharaɗin cimma yarjejeniyar zaman lafiya da ke kunshe a daftarin da Amurka ta gabatar.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta amince ta saki dukkan mutanen da ta ke riƙe dasu, masu rai da kuma gawarwakin waɗanda suka mutu, kamar dai yadda shirin sasanci na shugaba Trump ya yi tanadi.
Amma da alama sabuwar matsayar ƙungiyar Hamas na nufin za a shiga ƙarin tattaunawa, musamman a kan makomawar Zirin Gaza da kuma ƴancin Falasɗinawa.
Sanarwar na zuwa ne sa'oi bayan shugaba Trump na Amurka ya bai wa ƙungiyar wa'adin zuwa ranar Lahadi ta amince da yarjejeniyar zaman lafiya ko kuma ta fuskanci mummunar azaba.
Hamas ta ce har yanzu ana ci gaba da neman yadda za a cimma matsaya game da makomar Gaza idan an kawo ƙarshen yaƙin.
Me ƙungiyar Hamas ta ce a sanarwarta?
Sanarwar da Hamas ta fitar a matsayin martani ga tayin zaman lafiya da Amurka ta yi mata ta ce ƙungiyar ta amince ta ''Saki dukkan mutanen da ta ke tsare da su, masu rai da kuma gawarwakin waɗanda suka mutu, kamar yadda shugaba Trump ya buƙata. Amma za ta yi hakan ne kawai idan aka cika sharuɗɗan musayar fursunonin da aka gindaya''.
Ta ƙara da cewa ta ''Sabinta amincewar ta kan bai wa wata tawagar Falasɗinawa damar tafiyar da madafun iko a Zirin Gaza, amma a bisa amincewar Falasɗinawa da kuma tallafin ƙungiyar ƙasashen Larabawa da na musulmai''.
A game da makomar Gaza kuwa, Hamas ta ce wannan batu ne mai alaƙa da daftarin dokar ƙasa da ƙasa, wanda kuma ta ke neman a ci gaba da tattauna shi tare da wakilanta.
Hamas ta shirya ƙulla zaman lafiya - Trump
Shugaba Trump ya fitar da wata sanarwa mai nuna gamsuwa da matsayar da Hamas ta ɗauka.
Sanarwar ta shugaban Amurkan ta ce: "Ta la'akari da sanarwar da Hamas ta fitar, na gamsu cewa sun shirya rungumar zaman lafiya. Dole Isra'ila ta daina kai harin bamabamai Gaza domin mu samu a sako mutanen da ake tsare dasu cikin gaggawa kuma da lafiya!
"A yanzu dai akwai haɗari sosai a ci gaba da kai hare-hare Gaza. Tuni muka fara tattauna yadda za a aiwatar da shirin zaman lafiya. Muna magana ce ta wanzar da zaman lafiya na dindindin ba saboda Gaza kaɗai ba, harma ga dukkan yankin Gabas ta Tsakiya.''
Netanyahu ya yi martani ga Hamas
Ofishin Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya fitar da wata sanarwa inda ya ce ƙasar za ta yi aiki da Amurka wajen aiwatar da shirin zaman lafiya na shugaba Trump.
"Biyo bayan sanrwar Hamas, Isra'ila za ta aiwatar da zangon farko na yarjejeniyar zaman lafiya ta Trump domin gaggauta sakin mutanen da Hmas ta yi garkuwa da su,'' in ji sanarwar Netanyahu.
Ta ƙara da cewa "Za mu ci gaba da aiki tare da shugaban Amurka da tawagarsa wajen kawo ƙarshen yaƙin, amma a bisa tsarin da Isra'ila ta gindaya, wanda ya zo daidai da muradun Amurka.''
Dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da luguden wuta kan Gaza ne bayan wani hari da Hamas ta kai cikin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda aka kashe mutane aƙalla 1,200, aka kuma yi garkuwa da wasu 251.
Bayanan da hukumar lafiya a Gaza ta fitar sun nuna cewa mutane aƙalla 66,288 aka kashe tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza.