Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tambayoyi 7 da bai kamata namiji ya yi wa mace ba
Kana tsaye kusa da mace, wataƙila ma a cikin danginku take ko kuma a'a, kana jin cewa ya kamata ku zanta, sai zuciyarka ta fara raya maka wasu tambayoyi da za ka mata.
To kafin ka buɗe baki ka fara magana, ka tambayi kanka, shin wannan tambayar da zan yi tana kan layi kuwa, ko kuwa tambayar za ta iya tayar da ƙura?
Ko ma dai mene ne, ga tambayoyi 7 da ba su kamata ka yi mata ba.
Shekarunki nawa?
Amma wannan ba mummunar tambaya ba ce ga macen da shekarunta ba su zarce 25 zuwa 27 ba, wadda kuma har yanzu jikinta ke da alamun yarunta.
Amma idan ka yi wa mace wadda shekarunta suka zarta 30 zuwa 40, to akwai yiwuwar za ka sa ta ji babu daɗi, ko kuma ta ga kamar ka kunyata ta.
Kin taɓa haihuwa?
Wannan ba abu ne mai sauƙi ba, domin idan har ba ta da juna biyu kuma ba ta taɓa haihuwa ba, hakan na nufin kana cewa tana da ƙaton tumbi ke nan ko kuma ta cika ƙiba.
Ko kuma, ƙila tana matuƙar son samun haihuwa amma Allah bai ba ta ba, watakila rashin haihuwa na cikin abin da ya hana ta bacci a daren da ya gabata, ka ga ke nan tambayar da ka yi mata zai iya ƙara sosa mata zuciya da jefa ta cikin tunani.
Idan har kana son ka san ko tana da ciki ne, za ka iya jan ta da hira kawai, ƙila ta fada maka da kanta.
Za ki ara min kuɗi?
A al'adance maza ne ke ɗawainiya da mata, kuma mata sun saba da karɓar abubuwa ne daga maza, amma ba su bayar ba.
Saboda haka daidai ne, kuma abu ne da aka saba ka ga mace tana neman wanda zai ba ta, ba wani ya nema daga wurinta ba.
Mene ne nauyinki?
Sau da yawa mata ba sa son ana yi musu irin wannan tambayar, ko da suna da ƙiba ko kuma a rame, za ka iya karya musu gwiwa idan ka musu wannan tambaya, kuma ba lallai ne su fada maka gaskiya ba, ko da ma sun amsa tambayar.
Baya ga haka ma, ai namiji bai da wani dalilin da zai sa ya yi wa mace irin wannan tambaya.
Kina so na?
Idan ka yi wa mace wannan tambaya za ka iya saka ta cikin tsaka-mai-wuya, kuma idan ba ka yi hankali ba za ta iya cewa 'A'a', ko da kuwa tana son ka a cikin zuciyarta, kuma hakan zai iya kawo ƙarshen alaƙar da ke tsakanin ku.
Haka nan irin wannan tambayar za ta sa ta riƙa maka kallon kamar ba ka da ƙwarin gwiwa kai karan kanka ko kuma ka fiye azarɓaɓi.
Za ka iya ganewa idan budurwarka ko kuma matarka na son ka, ko da ba ka tambaye ta ba.
Me ya sa har yanzu ba ki yi aure ba?
Yin wannan tambaya kuskure ne domin ba ka san me ya sa ta ƙi yin aure ba. Yana iya yiwuwa tana da wata lalura ce ta lafiya ko kuma ba ta samu mijin aure ba, saboda haka ba ka san illar da wannan tambayar za ta mata ba.
Wannan tambayar za ta iya jefa ta cikin damuwa.
Za ki biya kuɗin?
Idan ka ɗauki mace zuwa wurin cin abinci ko ƙwalama, kada ka yi tsammanin ita ce za ta biya abin da ta ci.
Amma idan ta ga dama ta biya da kanta, to shi ke nan, kana da dama ka amince ko kuma ka ce ta bar shi.
Amma dai kada ka ce mata ta biya.
Ya kamata ka zama mutumin kirki mai nazari da sanin ya kamata, kuma ya kamata ka koyi ɗaukar ɗawainiya.