Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iyalin Ali Khamenei: Su wa aka kashe, su wane ne ke raye?
- Marubuci, Neda Sanij
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Lokacin karatu: Minti 5
Labarin kisan da aka yi wa wasu daga cikin iyalan tsohon jagoran addinin Iran, Ali Khamenei ya haifar da tambaya game da waɗanda suka rage a dangin.
Surukai maza da mata nawa jagoran addinin ke da su, kuma waɗanne ne danginsa na kusa-kusa?
A tsawon lokacin mulkinsa, Ali Khamenei ya naɗa da yawa cikin iyalansa manyan muƙaman siyasa ko wasu ma'aikatun gwamnati.
Kuma da dama cikin dangin nasa daga baya sun koma masu adawa da shi, inda aka ɗaure wasunsu a gidajen yari ko suka tafi gudun hijira ƙasashen ƙetare.
Wannan muƙala ta tattaro wasu bayanan da ake da su game da iyalan tsohon jagoran addinin.
Su wa aka kashe a harin gidan Ali Khamenei?
Baya ga jagoran addinin da aka kashe a harin, an kuma kashe mai ɗakinsa, Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh, wadda ta rasu kwana uku bayan harin.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun tabbatar da labarin, suna masu cewa ta ji mummunan rauni a harin wanda ya jefa ta cikin mayuwacin hali.
Tun bayan zaman Khamenei jagoran addinin Iran, ba kasafai ake wallafa hotunan mai ɗakin nasa ba.
A cewar rahotonni da dama akwai wasu iyalansa da dama da aka kashe a harin da suka haɗa da surukarsa, Zahra Haddad Adel, wadda ita ce matar Mojtaba Khamenei, (sabon jagoran addinin na yanzu), da surukinsa Misbah-ul-Hada Bagheri Kani, mijin ƴarsa Hoda Khamenei da jikarsa mai wata 14, Zahra Mohammadi Golpayegani, ƴa ga ɗansa Bashar Khamenei.
Mahaifi da mahaifiya da magabata
Hossein Tafreshi Khamenei (a) , Malamin addini daga yankin Tabriz, shi ne kakan Ali Khamenei tare da matarsa Hossein Mousavi.
Hossein Mojtahid Khamenei, wanda shi ne kakan Ali Khamenei ya auri wata ‘yar Turkiyya mai suna Mah Khanun.
A sakamakon haka ne suka samu Javad Hosseini Khamenei, wato mahaifin Ali Khamenei.
An haifi Javad ne a garin Najaf, kafin daga nan suka koma Tabriz, daga baya kuma suka koma Masshad da zama.
Javad Hosseini Khamenei ya kasance limamin masallacin Turkawa da ke Masshad.
Da farko Javad ya auri wata mata ce da ke jin harshen Turkanci, mai suna Razieh, kuma sun haifi ‘yaya mata uku tare da ita, wato Alawieh, da Bato da kuma Fatemeh Soltan.
Daga nan ne sai Razie ta rasu, inda Javad Hosseini Khamenei ya auri wata matar daga wani gida na malamai, sunanta Khadija Mirdamadi.
Baya ga harshen Larabci da Fashanci, Khadija Mirdamadi ta kuma koyi magana da harshen Turkanci a Masshad.
Ita da mahaifin Ali Khamenei sun haifi yara biyar, hudu mata da daya namiji, wato Mohammad, da Ali, da Badr al-Sadat, da Hadi da kuma Hassan.
Ƴan'uwa maza da mata
Mohammad Khamenei shi ne babban ɗa a gidan nasu, kuma ya girmi Ali Khamenei da shekara huɗu.
An haife shi a shekarar 1935, sannan ya karanci fannin shari'a a Jami'ar Tehran.
A lokacin mulkin Khomanei, Mohammad Khamenei ya kasance ɗaya daga cikin mambobin majalisar dokokin ƙasar 99.
Rubabeh ko Badr Sadat Khamenei da aka haifa a 1942, ita ce ƴa ta uku a gidan nasu, kuma ƙarama a matan gidansu, kuma ita ce ƴar danginsu ta farko da ta yi digiri.
Mijinta shi ne Ali Moradkhani Aranga, da aka fi sani da Sheikh Ali Tehrani.
Hadi Khamenei , da aka haifa a 1947, shi ne autan su ɗakinsu Ali Khamenei, wanda ya kasance cikin ƙungiyoyin masu alaƙa da Ayatollah Ruhollah Khomeini.
Hassan Khamenei , da aka haifa a1950 shi ne autan gidansu gaba ɗaya, kuma ɗan'uwan Khamenei ɗaya tilo da ba malami ba.
Ali Khamenei na da ƴan'uwa mata uku waɗanda suka haɗa mahaifi, Fatemeh Soltan da Hamidreza Shamsollahi, da wata da ba a bayyana sunanta ba.
Dangin mahaifiyarsa
Khadija Mirdamadi , mahaifiyar Ali Khamenei, na da da ƴan'uwa da suka haɗa mahaifi su tara ƴaƴan Aniseh, matar mahaifinta ta biyu da suka haɗa: Mohammad da Hamid da Ali da Safiyeh.
Sauran sun haɗa da Hassan da Hussein da Fatemeh da Hamideh da kuma Zahra Mirdamadi Najafabadi.
Dangin mahaifi
Mahaifin Mir Hossein Mousavi , firaministan ƙasar lokacin yaƙi, shi ne ɗan'uwa ga mahaifin Ali Khamenei.
Mahaifin. Mir Hossein Mousavi ya ziyarci gidansu su Ali Khamenei a garin Mashhad.
Hadi Khamenei ya bayyana su da ''manyan mutane masu amana''.
Mahaifin Khamenei na da ƴar'uwa mai suna Zahra Mousavi.
Dangin matarsa
Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh, ƴa ce ga Mashhad wani hamshaƙin ɗan kasuwa, ta auri Ali Khamenei, tana da shekara 17, lokacin yana da shekara 25.
Ali Khamenei ya taɓa faɗa cewa surikinsa ne ya biya sadakin auren nasu.
Mansoureh Khojasteh na da ƴan'uwa shida da suka haɗa da: Hassan, Mohammad, Javad, Hossein, Marzieh, da kuma Mehdi.
Mansoureh Khojasteh, wadda ke tare da mijinta lokacin harin da ya kashe mijin nata ta rasu kwana uku bayan harin.
Ƴaƴa da surukan Khamenei
Kafofin yaɗa labaran Iran sun jaddada cewa saɓanin sauran ƴansiyasar Iran, Ayatollah Khamenei ya haramta wa ƴaƴansa shiga harkokin tattalin arziki ko riƙe manyan muƙaman gwamnati.
A maimakon haka sun riƙa kula da manyan hukumomin da ma'aikatun ƙasar.
Mostafa , da aka haifa a 1965, shi ne babban ɗan Ali Khamenei.
Shi ne ya auri Saeideh Khoshvak, ƴar Azizollah Khoshvak, wani fitaccen masoyin Khamenei.
Mojtaba Khamenei (sabon jagoran addini) , da aka haifa a 1960, shi ne ɗa na biyu ga Ali Khamenei, kuma ya kasance mai ƙarfin faɗa aji a gwamnatin mahaifinsa.
Zahra Haddad Adel da aka kashe a harin Amurka ce matar Mojtaba.
Zahra ta kasance ƴa ga Gholam Ali Haddad Adel, tsohon kakakin majalisar dokokin Iran.
Ta kuma riƙe muƙaman siyasa da dama a ƙasar ciki har da wakiliya a majalisar dokoki.
Massoud Khamenei, da aka haifa a 1972, wanda aka fi sani da Mohsen, shi ne ɗa na uku ga Ali Khamenei.
Kamar sauran ƴan'uwan Mohsen ya kasance malami. Ya auri matarsa mai suna Susan Kharrazi, ƴa ga Mohsen Kharrazi, malamin makarantar horas da manyan malamai ta Qom.
Meysam ne autan ɗan jagoran addinin ƙasar Ali Khamenei wanda aka haifa a 1977.
saɓanin sauran ƴan'uwansa bai auri ƴar gidan malamai ba, sai dai ya auri ƴar ɗan kasuwa kuma attijiri Mahmoud Lolavachian,
Ƴaƴansa mata da mazajensu
Bashar al-Khamenei, ɗaya da cikin ƴaƴanta da Ali Khamenei biyu mata an haife ta a 1980.
Mijinta shi ne Mohammad Javad, ɗa ga Mohammad Mohammadi Golpaygani, shugaban ma’aikatan fadar jagoran addinin.
Mohammad Javad Mohammadi Golpaygani malami ne da ke koyar da ilimin fiqihu a birnin Qom.
An bayar da rahoton cewa an kashe ƴaƴan Bashar biyu a ranar da aka kai hari gidan jagoran addinin, inda aka kashe su tare.
Hoda Khamenei, ce ƴar Ali Khamenei, mace ƙarama da aka haifa a 1988.
Mijinta shi ne Misbah-ul-Hada Bagheri Kani , ɗa ga Mohammad Bagheri Bagheri Kani.
Misbah-ul-Hada Bagheri Kani farfesa ne a Jami'ar Imam Sadeq da ke ƙasar.