Har yanzu babu wata alama da ke nuna cewa an raunana duk da tsammanin da wasu a Amurka suka yi cewa kashe jagoran addinin ƙasar a ranar farko ta yaƙi zai haddasa rikicewa cda rushewar gwamnatin kasar in ji masu sharhi.
Masu sharhin sun ce wasu a Washington sun yi tunanin cewa bayan mutuwar Ali Khamenei, tsarin mulkin Iran zai iya rugujewa cikin sauri. Amma har yanzu babu wata shaida da ke nuna hakan, domin tsarin mulkin ƙasar ba ya dogara da mutum guda kawai.
Shugaban Amurka Donald Trump mutum ne da ke yawan magana kan muhimmancin shugabanci mai ƙarfi. Wata kila wasu a Amurka sun yi tunanin cewa bayan mutuwar Khamenei za a samu irin abin da ya faru a Venezuela, inda rikicin siyasa ya iya jawo sauyin gwamnati cikin gaggawa.
Amma irin wannan tunani na iya nuna rashin fahimtar yadda tsarin mulkin Iran yake in ji masu sharhi.
Tsarin gwamnatin ƙasar ya rarraba iko tsakanin manyan cibiyoyi na addini da gwamnati da kuma rundunar juyin juya halin Ira, wanda ke da ƙarfin iko sosai.
Iran kuma na da dogon tarihi na ƙin amincewa da Amurka da Isra’ila, lamarin da ke sa gwamnati da al’ummar ƙasar su haɗa kai lokacin da ake ganin akwai barazana daga waje.
A halin yanzu, Isra’ila ta bayyana cewa za ta yi ƙoƙarin kashe sabon jagoran Iran Mojtaba Khamenei. Sai dai har yanzu babu tabbacin ko ya ji rauni ko a’a.
Haka kuma ana mamakin cewa duk da ƙoƙarin da Tehran ke yi na gina martabar sabon jagoran, har yanzu ba a fitar da hotuna ko saƙonni da yawa daga gare shi ba.