Yadda yaƙin Iran ke neman raba kan Amurka da ƙasashen Turai

Lokacin karatu: Minti 2

Shugabannin kasashen Turai sun yi kakkausar suka ga matakin da Amurka ta dauka na sassauta takunkumin da ta kakaba wa Rasha - suna masu cewa hakan zai kara rura wutar yakin da Vladimir Putin ke yi a Ukraine.

Fadar White House ta ce za ta ba kasashe lamunin kwana 30 su saye man kasar Rasha da ke fuskantar takunkumin kasashen yammaci, a wani yunƙuri na samar da sauki da kuma wadata kasashe da man.

Bayanai sun nuna cewa yanzu Rasha ce babbar mai cin ribar yakin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran.

Washington ta ɗauki matakin ne domin samar da sauƙi kan kasuwar mai sakamakon yaƙin da take yi da Iran.

Da yake sanar da sassauta takunkumin, sakataren baitul malin Amurka, Scott Bessent ya ce matakin ba zai samar da wata fa'ida ta kudi ga gwamnatin Rasha ba, wanda ke samun mafi yawan kudaden shigar makamashin da take samu daga harajin da aka tantance a lokacin da ake hako man

Kpler ya ce za kusan ganga miliyan 120 na danyen mai na Rasha na iya shiga kasuwa a halin yanzu.

Ga Mista Trump, abin da ya dame shi ne tsadar farashin man fetur a gida, inda yake ci gaba da tashi, kuma masu kada kuri'a za su yanke masa hukunci kan yadda jam'iyyarsa ta tafiyar da tattalin arzikin Amurka.

Gwamnatinsa ta ce sassaucin takunkumin na kwana 30 ne kawai. Amma yadda Amurka ke ci gaba da yaƙi da Iran, babu wanda ke da tabbas.

Farashin danyen mai na ci gaba da tashi a kasuwannin duniya, inda ake sayar da ganga samfurin Brent kan sama da dala ɗari.

A ranar Alhamis farashin man ya zarta dala 100 karon farko tun 2022 da tasirin yakin Rasha a Ukraine ya haddasa.

Tun tashin farashin a 2022, an shafe wata hudu da rabi farashin bai sauya ba. Ana tsoron shiga irin wannan yanayin, amma matsalar na ci gaba karya kasuwar hannayen jarin Amurka.

Wasu Rahotannin da ba a tabbatar ba sun nuna cewa wasu kasashe kamar Indiya da China na tattaunawa da Iran domin ta bude mashigin Hormuz.

Ba a dai san irin girman tasirin da hakan zai yi kan farashin mai ba a duniya ba a nan gaba.

Duk da kokarin wasu kasashe masu arzikin mai na fitar da rarar mai amma hakan bai hana tsadar danyen mai ba da ake fuskanta.

Rasha ta fara cin gajiyar tsadar ɗanyen mai bayan toshe babbar hanyar ruwa ta mashigin tekun Fasha da Iran ta yi a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kai mata.

Martanin kasashen Turai

Shugaba Zelensky na Ukraine ya ce matakin Amurka na sassauta takunkuminta kan Rasha wata hanya ce ta ba Moscow hanyar samun biliyoyin daloli a wata.

Mista Zelensky ya ce matakin ba zai taimaki zaman lafiya ba.

Tarayyar Turai da ba ta sassauta takunkumanta ba kan Iran ta bayyana adawa da matakin na Amurka.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce toshe mashigin Hormuz ba zai taɓa zama hujjar janye wa Rasha takunkumi ba.

Birtaniya ba ta nuna za ta amince ta sassauta takunkumin ga Rasha ba, inda Sakataren tsaron kasar, John Healey, ya nuna alaƙar da ke tsakanin Iran da Rasha.

Shugaban gmwantin Jamus, Friedrich Merz ya ce "sassauta wa Rasha takunkumi a wannan lokacin kan kowane irin dalili, kuskure ne.