Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waɗanne ƙasashe ne ke cin ribar yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran?
- Marubuci, Marina Daras
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Marubuci, Stephen Hawkes
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Takamaimai ba za a iya cewa akwai waɗanda suka yi nasara a yaƙi ba - amma a mafi yawan lokuta, mutanen gari su ke shan wahalar. Yayin da kasuwar makamashi da jigilar sa ya faɗa wani yanayi a duniya, wasu ƙasashe na ƙoƙarin daƙile matsin tattalin arzikin da za a shiga - amma wasu kuma dama ce ta buɗe musu domin cin ribar hakan.
Yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran yana jefa yankin da ma duniya cikin wani yanayi. Ya rikita ƙasashen yankin Gulf da kuma tilasta dubban mutane a Gabas ta Tsakiya barin muhallansu.
Baya ga yaƙi kuma, farashin mai ya yi tashin gwauron zabi da kuma tsaikon jigilarsa a yankin Gulf, musamman ta mashigar Hormuz, lamarin da ya sa ake fuskantar hauhawar farashin makamashi a duniya.
To amma, waɗanne ƙasashe ne za su ci ribar hakan ko asara a wannan rikicin?
Rasha
Iran babbar aminiyar Rasha ce musamman a fannin soji. Sai dai kisan jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sake haifar da koma baya ga Moscow tun bayan kifar da gwamnatin Basha al-Assad na Syria da kuma kama shugaban Venezuela, Nicolás Maduro da Amurka ta yi.
Amma kuma, yaƙin na Gabas ta Tsakiya zai iya taimaka wa Rasha a yaƙin da take yi da Ukraine, saboda akwai yiwuwar janye sojojin Amurka.
"Sauya akalar makamai masu lizami na na'urorin kakkaɓo makamai zai taimaki Rasha, saboda zai taƙaita taimakon da Ukraine ke samu," in ji Nicole Grajewski, mataimakin Farfesa a cibiyar nazarin ƙasa da ƙasa da ke Rasha.
Masana sun ce ƙaruwar buƙatar jirage marasa matuƙa samfurin Shahid da Iran ke da shi a yanzu, ba lallai ya yi wani tasiri ga Rasha kan faɗan ta da Ukraine ba.
"Rasha ta dogara da Iran kan haɗakar tsaro na wani lokaci a yaƙinta da Ukraine, bayan da Iran ta ba ta jiragen Shahid, da kuma fasahar ƙera shi a shekarar 2022 da 2023," in ji Hanna Notte.
"Yanzu an kai wani mataki da Rasha ba ta buƙatar Iran domin ci gaba da yaƙi da Ukraine. Rasha za ta iya ƙera jirage marasa matuƙa samfurin Shahed da kanta."
Kulle mashigar Hormuz da Iran ta yi, ya haifar da tsaiko wajen jigilar mai da iskar gas, lamarin da ya sa farashin ya tashi, kuma hakan zai iya ƙara samar da kuɗaɗen shiga ga Rasha wadda ta samu koma baya saboda yaƙin ta da Ukraine.
Kasafin kuɗi Rasha ya dogara ne da fitar mai a kan dala 59 ka kowace ganga - amma yanzu farashin ya tashi sosai zuwa dala 120 kan kowace ganga. A yanzu da aka katse jigilar man a yankin Gulf, Rasha za ta iya amfana da hakan ta hanyar kai shi ga kasuwannin duniya irin su China da Indiya.
Wani masanin tattalin arziki a kamfanin Argis da ke harkar makamashi da zuba jari, David Fyfe ya ce: "Amurka ta taɓa faɗa wa Indiya ta dakatar da sayen mai daga Rasha, amma yanzu ta samu damar yin hakan aƙalla nan da watanni shida masu zuwa"
China
Har yanzu yaƙin Iran ɗin bai shafi ƙasar China sosai ba - amma duk da haka za ta ji raɗaɗin.
Kusan kashi 12 na man da China ke shigarwa ƙasar ta daga Iran yake, a cewar Cibiyar Makamashi ta Duniya.
Bugu da ƙari, China tana da tarin mai da zai riƙe ta tsawon watanni, kuma cikin sauƙi za ta iya neman taimakon Rasha idan ya ƙare.
Amma kuma kuma yaƙin zai shafi fitar da kaya daga China, in ji Fyfe.
Tsaikon da aka samu ta mashigar Hormuz ba wata babbar matsala ba ce ga China, amma kuma bi ta tekun Atalantika yana da muhimmanci ga kayayyakin da ake kaiwa Yammacin duniya.
A gefe guda kuma daga yankin Larabawa, akwai mashigar Bab el-Mandeb, da ta haɗa nahiyar Asiya da Turai da kuma Afirka, inda su ma ake samun kai hare-haren ƴantawayen Houthi da ke Yemen da wasu ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran.
Fyfe ya shaida wa BBC cewa: "Akwai yiwuwar za a iya samun cunkoso a tekun maliya, saboda manyan jiragen ruwan dakon kaya daga nahiyar Asiya da ke bi ta tekun Atalantika zuwa kudanci Afirka.
"Hakan zai ƙara yawan kashe kuɗaɗe," in ji Neil Quilliam, wani mai sharhi kan Gabas ta Tsakiya a Chatham House da ke Landan.
"Za a samu ƙarin kwanaki 10 zuwa 14 a tafiyar. Kuma dogara da kaya da ke saman ruwa na tsawon wannan lokacin, wani ƙarin dala miliyan biyu ne."
Yaƙin da ake yi a Iran zai iya ba China damar hulɗar ƙasa da ƙasa, amma kuma tana ɗora kanta a matsayin abokiyar gogayyar Amurka, in ji Philip Shetler-Jones.
Shugaban China Xi Jinping, zai ci gaba da kallon kansa a matsayin jagora a shugabancin duniya kamar shugaban Amurka Donald Trump.
Yaƙin zai kuma iya ba China damar nazarin martanin Trump kan muhimman wurare irin su Taiwan da China ɗin take iƙirarin iko da ita.
Sauyawar tattalin arziki
Yaƙin da ake yi ya shafi ƙasashen kudu maso gabashin nahiyar Asiya, da suka dogara kacokan kan mai da iskar gas daga yankin Gabas ta Tsakiya. Wasu da dama sun ɗauki matakan rage raɗaɗin domin daidaita tattalin arzikinsu tun da wuri.
Farashin dizal a Vietnam ya tashi da kusan kashi 60% tun bayan fara yaƙin, inda gwamnati ta umurci ƴanƙasar su yi aiki daga gida idan da hali.
A ƙasar Philippines, da ke shigar da kusan kashi 95% na ɗanyen man ta daga Gabas ta Tsakiya, ma'aikata sun koma aiki sau huɗu a sati, amma ban da masu aikin ujula.
Haka ma an taƙaita irin wannan zirga-zirga a Pakistan, amma ban da bankuna. Tuni aka maida aiki daga gida a ma'aikatun da suka kamata, yayin da ake darussa a makarantu ta intanet.
A wani bayani da aka watsa a kafar talabijin na ƙasar, Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif, ya ce yana da matuƙar muhimmanci ƙasar ta yi tattalin man da take da shi.
A Bangladesh ma, mutane na rige-rigen yin sayayya abubuwa. An samu dogayen layuka a gidajen mai, inda aka ƙayyade adadin litocin man da masu ababen hawa za su iya siya; Masu mota lita 10, masu babur kuma lita biyu kacal.
Akwai yiwuwar wahalar da za a shiga sakamakon yaƙin za ta iya wuce ƙarancin makamashi.
Manoma a faɗin duniya sun dogara ne da takin zamani domin inganta ƙasa da abubuwan da take buƙata domin samar da abinci. Idan aka samu wani tsaiko kan hakan zai iya haifar da ƙarancin abinci a duniya.
Quilliam ya shaida wa BBC cewa: "Kashi 30 na takin zamani yana bi ne ta mashigar Hormuz. Ana samar da takin ne daga wasu sinadarai daga ɗanyen mai. To idan aka cire kaso 30 daga kasuwar duniya, ba ƙaramin ƙalubale hakan zai haifar ba."
Biyo bayan hare-haren da aka kai wa ma'aikatun ta, kamfani QatarEnergy, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ke fitar da takin zamani a duniya, ya sanya dokar ta ɓaci wajen sarrafa shi.
Quilliam ya ce, "Za a iya ganin tasirin hakan kan samar da abinci da hauhawar farashi nan da wasu watanni shida zuwa tara."
Ƙarin rahotanni daga sashen Hindi na BBC da Elizaveta Fokht, daga sashen BBC Rasha