Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugaban Amurka na son tattaunawa da Rasha don dakatar da yakin Ukraine
Shugaba Joe Biden na Amurka ya ce a shirye yake ya tattauna da Shugaba Vladimiri Putin na Rasha amma a karkashin wasu sharudda.
Shugaban na Amurka ya bayyana haka ne a taron manema labarai da suka yi da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron inda shugabannin biyu suka sha alwashin ci gaba da mara wa Ukraine baya a yakar mamayen da Rasha ta yi mata.
Shugabannin biyu sun jaddada karfin kawancensu wajen tunkarar mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine din.
Kuma sun tabbatar da cewa za su ci gaba da nuna rashin amincewarsu a kan matakin na Rasha.
A nasa jawabin, Shugaba Eammanuel Macron na Faransa ya ce duk wata tattaunawa da za a yi da Moscow dole ne ta hada da Kyiv:
Ya ce, '' ba za mu taba sa 'yan Ukraine su yi sassaucin da ba su amince da shi ba, saboda ba zai taba gina zaman lafiya mai dorewa ba.''
Shugaban ya yi watsi da duk wata rashin jituwa tsakaninsa da takwaransa na Amurka game da matsa wa Ukraine lamba ta amince da yarjejeniyar zaman lafiya.
''Idan muna son mu samu zaman lafiya mai dorewa to ya zama dole mu mutunta lokaci da sharuddan da 'yan Ukraine za su tattauna kan batutuwan da suka shafi yankin da kuma makomarsu.'' in ji shi.
Shugaban ya kara da cewa zai yi magana da Shugaba Putin a kwanaki masu zuwa, sai dai shugaba Biden ya bar yunkurin sulhu ta hanyar amfani da kafar diflomasiya ga takwaran aikin nasa yana mai cewa a shirye yake ya yi magana da Biden idan ya nuna aniyar a kawo karshen yakin.
Ya ce, ''a shirye nake na yi magana da shugaba Putin idan ya nuna alamun yana son ya kawo karshen yakin amma ya zuwa yanzu bai yi hakan ba.''
Kalaman shugabanin biyu na zuwa ne a dai dai lokacin da wani babban jami'i a gwamnatin Ukraine ya bayyana cewa sojojin Ukarine dubu 13 ne suka rasa rayukansu tun bayan da aka fara yakin.