Mece ce manufar shirin Putin?

Wannan tambaya ce da mutane da dama ke neman amsarta, tun ma kafin mamayar da Rasha ke yi a Ukraine.

Shin mece ce manufar shirin Putin?

Tsohon shugaban Amurka George W Bush ya taba cewa ya san abin da ke cikin zuciyar Mista Putin. Sannan kuma yadda a yanzu dangantaka ke kara tsami tsakanin Rasha da kasashen Yamma, don haka sanin hakikanin abin da ke ran Shugaba Putin abu ne mai matukar wahala.

To amma yana da kyau a yi kokarin sanin hakan, idan ma bai zama wajibi ba, yanzu da shugaban ya kaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan wasu yankunan Ukraine.

Akwai shakku game da maganganun da ke cewa shugaban na fuskantar matsin lamba, a mamayar da yake yi wa Ukraine wadda ya kira 'Atisayen soji na musamman' na fuskantar koma baya, dalilin da ya sa a 'yan kwanankin shugaban ya sake shiri da fasalin yakin.

Kawo yanzu dai yakin na kusantar wata takwas da fara shi, kuma babu alamun kawo karshensa nan kusa. Rasha dai ta bayyana asarar sojoji masu yawa a yakin, inda a 'yan makonnin baya-bayan nan take rasa iko da wasu yankuna da a baya ke hannunta.

Domin karfafa dakarunsa da ke yakin na Ukraine, a watan da ya gabata Mista Putin ya bayyana sake tattara dakaru, wani abu da a baya ya kafe cewa ba zai yi ba. A yayin da tarin takunkumai ke ci gaba da yi wa tattalin arzikin kasar kafar ungulu.

Idan muka koma abin da ke zuciya Putin, shin yana ganin hakan a matsayin wani gazawa a gare shi, kuma yana kallon matakinsa na mamayar Ukraine a matsayin kuskure?

Konstantin Remchukov edita kuma mai jaridar Nezavisimaya Gazeta a kasar Rasha ya ce ''Kar ma ku yi tunanin haka, domin kuwa yadda yake kallon yakin ne ya kawo dukkan halin da ake ciki a yanzu, domin kuwa shugaba ne mai kama-karya da ke da karfin makamin nukiliya''

''Shugaba ne da babu mai tanka masa a kasarsa. Yana da wasu manufofi masu karfi wadanda suke sa ka shi yin abubuwa marasa kyau. Yana kallonsu a matsayin abubuwa masu matukar kayu a gareshi'', in ji mista Remchukov.

Ba ga shi ba, ga makomar kasar Idan wannan yakin na da muhimmanci yaya shugaban ya kamata ya shirya domin samun nasarsa?

A 'yan watan nin baya-bayan nan manyan jami'an kasar ciki har da mista Putin sun yi ta barazanar cewa masu kula da makaman nukiliyar kasar su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.

To sai dai shugaban Amurka Joe Biden ya shaida wa gidan talbijin na CNN cewa ba ya tunanin Putin zai yi amfani da makaman, kuma bai kamata ya rika irin wannan barazanar ba.

To amma luguden makaman nukiliya a kan Ukraine da Rasha ta kaddamar wanan makon ya nuna yadda kasar ke son dagula al'amura a Kyiv.

Shin zai yi yaki da kasashen Yamma?

"Yana kokarin kauce wa yaki kai-tseye da kasashen Yamma, to amma a shirye yake game da yin hakan'', in ji Grigory Yavlinsky wani mai ra'ayin sassauci ya kara da cewa "Ina fargaba game da barkewar yakin nukiliya''.

Haka kuma ya ce abu na biyu ''Ina fargabar barkewar yakin da ba zai kare ba, yakin kuwa da ba zai kare ba, yana bukatar tanadi mai yawa. Wannan kuma shi ne abin da Rasha ba za ta iya jure wa ba.

Kaddamar da harin makamai masu linzami kan wasu biranen Ukraine alama ce da ke nuna yadda Rasha ke da karfin soji, to amma zuwa wane lokaci Rasha za ta dauka tana kai wadan nan hare-hare?

Shin za ta ci gaba da harba irin wadannan makamai? cikin kwanaki ko makonni ko watanni ?

''Masana da dama suna da shakku game da haka saboda a ganinsu kasar ba ta da isassun makaman da za ta iya yin hakan'', in ji Mista Remchukov.

Ta bangaren soji, kowa ana ganin hakan a matsayin wata alama ta nasarar yakin da kasar ke yi. Shin mene ne alamar nasara?

Ban sani ba, ba ka sani ba, kuma babu tabbaci ko shi ma Putin ya sani. A cikin watan Fabrairu dakarun Rasha sun yi ta samun nasara a yakin inda suka rika korar sojojin Ukraine tare da mamaye wasu yankunan kasar.

Lissafi ne ya bace masa

Da fari ya raina karfin sojin Ukraine da al'umar kasar, tare da daukar cewa sojojin kasarsa na da karfin da za su ci nasarar yakin cikin 'yan makonni.

To yanzu mene ne tunaninsa?

Shin shirinsa na yanzu game da yakin shi ne kwace iko da wasu yankunan Ukraine, tare da mayar da su karkashin ikonsa ko kuwa so yake ya mallake ilahirin kasar ta dawo karkarshin ikonsa?

Mista Medvedev ya ce na yi amanna cewa makomar kasarmu shi ne yadda muka yi kokarin wargaza mulkin Ukraine a yanzu.

Idan dai kalaman Mista Medvedev na bayyana manufar Putin game da yakin ne, to shakka babu akwai jan aiki a gaba game da yakin.

Mista Yavlinsky ya ce ''Ina tunanin Putin a kan wannan matsayin yake, ya kwashe skerau masu yawa yana shirya wa wannan yaki, alal misali ruguza kafafen yada labarai masu cin gashin kansu, ya faro wannan tun shekarar 2001.

''Ya faro shirin wargaza harkokin kasuwanci masu cin gashin kansu a shekarar 2003. Sannan a 2004 ya shirya wa abin da yanzu ya faru ga yankunan Crimea da Donbas.

Bai kamata mu manta wannan ba. Matsalolin Rasha sune suka haifar da manufarmu, kuma manufarmu a nan ita ce ta haifar mana da samun Putin yanzu'', in ji Mista Yavlinsky.

To Amma tambayar anan ita ce mene ne matsayin kasashen yamma game da faruwar wannan lamari?

''Matsalar ita ce wannan tsari ba zai haifar da da mai ido ba. Akwai mutane masu kima da mutunci a Rasha, to amma babu kungiyoyin kare 'yancin dan adam a kasar. Wannan shi ne dalilin da ya sa ba za su iya bijirewa ba'', in ji Mista Medvedev.