Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lookman ya kawo karshen Leverkusen bayan wasa 51 a jere ba a doke ta ba
Atalanta ta lashe Europa League na bana, bayan da ta ci Bayern Leverkusen 3-0 ranar Laraba a Dublin.
Kungiyar da ke buga Serie A ta ci dukkan ƙwallayen ta hannun ɗan Najeriya Ademola Lookman, wanda ya ci biyu kan hutu ya kara daya a zagaye na biyu.
Da wannan ƙwazon Lookman ya zama na shida da ya ci ƙwallo uku rigis a wasan karshe a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai tun bayan Jupp Heynckes na Borussia Monchengladbach a1975 UEFA Cup.
Haka kuma Lookman ya zama na uku ɗan Najeriya da ya zura uku rigis a raga a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai, bayan Alex Iwobi a 2019 a Europa League da kuma Joe Aribo a 2022 a dai Europa League.
Atalanta ta lashe babban kofi a karon farko a gasar zakarun Turai tun bayan shekara 61, wato tun daga 1963.
Ƙungiyar da Xabi Alonso ke jan ragama ta yi wasa 51 a jere a dukkan karawa ba tare da rashin nasara ba, wadda ta dauki Uefa Cup a 1988 da kuma German Cup a 1993.
Leverkusen ta lashe Bundesliga na bana a karon farko a tarihi, bayan da ta kafa bajintar kammala gasar ba tare da rashin nasara ba.
Ranar 25 ga watan Mayu Leverkusen za ta buga wasan karshe a German Cup da Kaiserslautern, watakila ta lashe kofi biyu a bana, bayan da ta yi harin uku rigis.
Ƙungiyoyi biyun sun kai wasan karshe a kakar nan, bayan da suka fitar da wadanda ke buga Premier League tun daga zangon daf da na kusa da na karshe.
Bayern Leverkusen ce ta yi waje da West Ham United, yayin da Atalanta ta yi nasarar fitar da Liverpool
Atalanta ta kai wasan karshe bayan da ta doke Marseille ta Faransa, ita kuwa Leverkusen ta yi waje da Roma ce.
Sevilla ce ta lashe kofin bara a bugun fenariti da cin 4-1, bayan da suka tashi 1-1.
Jerin wadanda suka lashe Europa League a tarihi:
- Sevilla FC 7
- Atletico Madrid 3
- Liverpool 3
- Inter Milan 3
- Juventus FC 3
- Eintracht Frankfurt 2
- Chelsea 2
- Porto 2
- Feyenoord Rotterdam 2
- Parma Calcio 1913 2
- IFK Goteborg 2
- Real Madrid CF 2
- Tottenham 2
- Borussia Monchengladbach 2
- Villarreal CF 1
- Manchester United 1
- Shakhtar Donetsk 1
- Zenit St. Petersburg 1
- CSKA Moscou 1
- Valencia C.F 1
- Galatasaray SK 1
- Schalke 04 1
- Bayern Munich 1
- Ajax Amsterdam 1
- Napoli 1
- Bayer 04 Leverkusen 1
- Anderlecht 1
- Ipswich Town FC 1
- PSV Eindhoven 1