Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda masu safarar mutane suka ja hankalina da daɗin baki'
Rikicin Rohingya: Dalilin da ya sa masu gudun hijira suke kasadar aukawa hannun masu safarar jama`a da tafiya ta teku da yake da hadarin gaske.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce masu gudun hijira `yan Rohingya su kusan 350 ko dai aka kashe su ko suka bace bata ko sama ko kasa ba a san inda suke ba, a shekarar 2022 a lokacin da aka yi safarasu zuwa Maleshiya.
Duk da wannan hadari da suke aukawa ciki a kullum, masu son rungumar wannan tafiya mai cike da kasada sai karuwa suke ci gaba da yi kamar wasa. Ina dalili? Ga tsananin duhu, ga kadaici ga tsananin sanyi.
Faizal Ahmed (an sakaya sunansa ne) dan shekara 24 kuma ba shi da mata. Bayan ya zauna a sansanonin `yan gudun hijira na Rohingya na Bangladesh na fiye da tsawon shekara goma.
Ya yanke shawarar barin wajen ta hanyar biyan masu safarar jama`a.
Cikin taka-tsantsan ya nufi kogin da ya raba Bazaar ta Cox daga jihar Rakhine ta Myammar.
“Na san mutane da dama sun rasu a hanyar, sai dai har ila yau ina sane da mutane da dama da suka yi nasarar isa Maleshiya.
Ba zan ci gaba da da tafiyar da rayuwa haka ba,” Ahmed ke shaida wa BBC.
Hukumar Kula da `Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce `yan Rohingya su a kalla 348 suka rasu ko suka bace ba a san inda suke ba, a teku a 2022.
Hakan ya sanya ta zama daya daga cikin shekaru mafiya hadari daga shekarar 2014.
Duk da haka Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kullum yawan mutanen da suke yin wannan tafiya mai hadari ta teku zuwa Maleshiya sai karuwa suke .
Mene ne yake jan hankalin masu gudun hijiran watsi da wannan hadari?
Yanke kauna
Ahmed yana da kanni mata uku da kanni maza biyu. Iyayensa sun rasu, shi ne a yanzun iyalan suke karkashinsa. Yana son kyautata rayuwarsu.
“A Bangladesh babu mai kare mana rayuwarmu. Ba mu da wata dama ta yin aiki,” in ji shi.
Ahmed yana fatan rayuwarsa za ta sauya ya ji dadi da zaran ya isa Maleshiya.
Shekaru masu yawa Musulmin Rohingya da suke gudun hijira suna ta tserewa zuwa Bangladesh. Kasarsu kuma garinsu Myammar ta ki su, ta ki daukarsu a matsayin su ma `yan kasa ne.
Sojojin Myammar sun kaddamar da wani gagarumin aiki a jihar Rakhine a 2017 da Majalisar Dinkin Duniya ta kwatanta da “misalin littafin kare-dangi”
`Yan Rohingya su wajen miliyan daya suka fake a Bangladesh.
Ahmed da iyalansa suna cikin wadanda suke zaune a sansanonin `yan gudun hijira na Rohingya da ke Bangaladesh kafin lokacin.
“Mun fid-da-ran cewa Myammar za ta mayar da mu,” kamar yadda ya yi bayani.
Ahmad ya sadu da wani eja da ya masa alkawarin zai kai shi Maleshiya a wajen Dala 4,400. Har ya biya Dala 950 a matsayin somin tabi.
Iyalansa ne za su biya sauran da zai danganta da nasararsa.
Kanninsa mata da suke matsayin `yan aikin gida a gidajen jama`a, suka tara wasu daga cikin kudaden.
Sauran za a same su ne, ta hanyar sayar da gwalagwalan iyalan.
Mutanen da suka bace
Hukumar UNHCR ta ce `yan Rohingya masu gudun hijira su 3,500 ne suka yin kokarin tsallake tekun da yake da hadarin gaske a bara, idan aka kwatanta das u 700 da suka yi wannan yunkuri a shekarar 2021.
Wasu kananan jiragen ruwa sun nitse ba tare da wata alama ta iya gano su ba. Majalisar Dinkin Duniya ta ce wani ƙaramin jirgin ruwa, da ake tunanin ya bar Bazar ta Cox (Cox`s Bazar) ranar 2 ga watan Disamba na shekarar 2022 da`yan gudun hijira na Rohingya su wajen 180 a cikinsa, ya nitse a Tekun Andama.
Tun lokacin da `yan Rohingya suka zama ba su da kasa da za su iya cewa tasu ce, suka dukufa ga tafiya ta hanyoyin da ba su kamata ba,da suka saba wa doka, kuma babu wani abin da dangi za su iya yi sosai domin gano wadanda suka bace.
Sharifa Khatun mace ce mai shekara 33 da mijinta ya rasu, take zaune a sansanin `yan gudun hijira tun 2016. Hudu daga cikin iyalanta sun bace a teku.
“`Yar uwata ta tafi Maleshiya da `ya`yanta uku – mata biyu namiji guda,” kamar yadda ta bayyana.
Tun shekarar 2013 sirikinta ya tsere zuwa Maleshiya daga Myammar ta wani karamin jirgin ruwa tafiyar da take da hadari.
`Yar uwar Khatun da `ya`yanta daga nan suka hau jirgin sama zuwa Bangladesh a 2016 domin tsere wa tashin hankali.
Ta dade tana son tarar da mijinta a Maleshiya.
“Masu safarar mutanen suka sa mata rai.
`Yar uwar tawa ta biya wajen Dala 2,500 a matsayin somin tabi, ta ba ni umarnin in biya sauran da zaran ta isa can,” Kamar yadda Khatun ta yi bayani.
“Ta tafi ranar 22 ga watan Nuwamba kuma bayan wajen mako biyu, ta kira ni daga garin Rathedaung, da ke gabar teku a jihar Rakhine da ke Myammar.”
Tun daga lokacin, Khatun ba ta kuma ji daga `yar uwarta ba.
“Sai da na fada wa `yar uwata kada ta tafi, amma masu safarar mutanen suka yaudareta da dadin baki.”
Karuwar safarar jama`a
Sansanin `yan gudun hijira na Katupalong da ke yankin Bazar ta Cox (Cox`s Bazar) – da akan kwatanta shi da mafi girma a duniya – akwai mutane masu yawan gaske irin su Khatun da ba su san me ya auku ga `yan uwansu ba.
“Safarar mutane sai karuwa take yi a kullum. Ban san yadda za a kawo karshensa ba,” in ji ohammed Aziz, wani mai fafutukar kare hakki na Rohingya daga Cox`s Bazar.
“A kwanakin karshen watan Janairu, kananan jiragen ruwa a kalla uku suka tafi Maleshiya.
Daya a ranar 16 ga watan Janairu, na biyun ranar 20, sai na karshe ranar 27.”
Ya ce fiye da mutum 350 ya hau wadannan kananan jiragen ruwa, kuma babu mamaki akwai wasu.
Wasu majiyoyi da suke sansanonin na `yan gudun hijira na `yan Rohingya, tuni suka sanar da BBC cewa wani jirgin dauke da mutane 200 ya bar Tankaf da ke Bangladesh ranar 17 ga watan Fabrairu.
Tunda ba a barin `yan Rohingya da suke gudun hijira su yi aiki, Aziz ya ce yawancin `yan gudun hijiran, `yan uwa da danginsu da suke kasashen ketare ne, suke aiko musu da kudaden yin tafiyar.
Masu safarar mutanen sukan yi amfani da kananan jiragen ruwa na kamun kifi wajen dibar mutane su yi wannan tafiya, jiragen da ba a yi su domin daukar mutane masu yawa, su yi dogon zango da su ba.
Sukan kuma cika matafiyan da karairayin abubuwan jin dadi da za su tarar a can idan sun je.
“eja-ejan suna fada wa `yan gudun hijiran cewa bayan sun isa Maleshiya, za su iya samun mafaka a Amurka, da Canada/Kanada, da Turai,” kamar yadda Aziz ya yi bayani.
‘Duk karya ce”
Ba sauran sa rai da kuma neman mafita ido rufe
Sai dai ga `yan Rohingya da dama, zama a Bangladesh, daya daga cikin kasashen duniya da suka fi cincirindon mutane, nan ma ba wata abar sha`awa ko jin dadi ba ce.
“Babu yadda za a yi ka kwatanta sansanonin `yan gudun hijira da gida. Sa ransu tana ci gaba da raguwa, tare da neman mafita ido rufe.
Shi ya sa suke kokarin auka wa wannan tafiya da take cike da kasada,” In ji Mohammed Mizanur Rahman, wani jami`in a wata kungiya da ba ta gwamnati ba a Cox`s Bazar.
“A shekarar da ta gabata, mun tattara bayanai guda 12 na safarar bil`Adama.
Mun kuma kama mutane da suke da hannu tare da kwace kananan jiragen ruwan nasu, da suke amfani da su, wajen safarar mutane,” kamar yadda Rahman ya yi bayani.
Hukumomin Bangaladesh da Majalisar Dinkin Duniya sun ce su biyun suna daukar matakai na yin gardagadi a kan hijira ba bisa ka`ida ba,.
Sai dai, tunda yawancin irin wadannan tafiye-tafiye suna yin su a boye ne, Majalisar Dinkin Duniya ta ce, tana kokarin sa ido a kan wane ne ya tafi.
“UNHCR ba ta da karfin iya gano mutane a teku.
Idan an sanar da mu cewa ga wani jirgin ruwa can, za mu iya ankarar da Majalisar Dinkin Duniya ko sauran kungiyoyi na jinkai da suke kurkusa,” in ji Regina De La Portilla, wata jami`ar Sadarwa ta UNHCR a Cox`s Bazar.
A lokutan da suka gabata, Majalisar Dinkin Duniya ta yi nasarar samun taimako ga kananan jiragen ruwa ruwa da suka shiga wani mawuyacin hali a teku.
Daya daga cikin irin wadannan kananan jiragen ruwa da ke dauke da `yan Rohingya masu gudun hijira su fiye da 100, a karshe ya isa Sri Lanka a watan Disamba.
Fata
Idan muka koma sansani kuwa, har yanzun Khatun tana cikin yanayi na tana kasa tana dabo.
Ba ta jin dadin halin yanayin rayuwar da take ciki, sai dai wacce mijin nata ya rasu da take da `ya`ya uku ta kudiri aniyar zama wuri guda.
Ba ta da tabbacin wa zai taimaka mata samun bayani a game da `yar uwarta da ta bace.
“Ina matukar bakin ciki. Ba ni da wani labari a game da su. Magana ta karshe da na yi da su, ita ce ranar 14 ga watan Disamba,” in ji Khatun.
“Ina fatan wata rana zan kuma ganin `yar uwata da `ya`yanta”
Tafiya cike da tausayi
Sa`a daya bayan magana da mu, Fazal Ahmed ya samu kira daga masu safarar mutanen. Ba zai tsaya jira ba.
Ahmed ya cire takalminsa sandal, na nade bujensa. Yana kaiwa gaban ruwan, sai tausayi.
“`Yan uwana maza da mata sun ce mun kada in tafi. Ba ni da wani aiki a nan,” ya cem a lokacin da ya soma shassheka.
Ya sa ran yin aiki a matsayin lebura tunda bai iya karatu ko rubutu ba.
“Zan je Maleshiya domin samar wa `yan uwana kudi. Zan taimaka wa `yan uwana maza da mata su yi karatu. “
Ahmed ya san cewa tafiya ce da za ta sauya masa rayuwa.
Ya shiga ruwa cikin duhu, ya nufi karamin jirgin ruwan da yake fatan zai dauke shi, ya kai shi, ya kai shi ga gacin kyakkyawar rayuwa.