Paris 2024 Olympics: Argentina ta yi wa Brazil harambe

Asalin hoton, Getty Images
Mai rike da kofi, Brazil ba ta samu gurbin shiga wasan Olympic ba a fannin ƙwallon kafa, bayan da Argentina ta doke ta 1-0 a karshen mako.
Wannan shi ne karon farko da Brazil, wadda ta yi fatan lashe lambar yabo ta zinare karo na uku a jere ba za ta halarci gasar ta Olympic ba da za a gudanar a birnin Paris a 2024.
Tawagar Argentina ta matasa ƴan kasa da shekara 23 ta ci Brazil a minti na 77 ta hannun Luciano Gondou, inda hakan ya sa ta samu gurbin wakiltar Kudancin Amurka.
Brazil ta lashe lambar yabo ta zinare hudu a gasar tamaula a Olympic.
Argentina, wadda ta lashe lambar yabo ta zinare a Olympic a 2004 da kuma 2008 ta kammala a matakin farko da tazarar maki biyar a rukunin.
Yanzu saura gurbi daya ya rage da za a fafata tsakanin Paraguay da Venezuela ranar Lahadi, wanda zai fayyace ɗayar da za ta wakilci Kudancin Amurka a Olympic a fannin tamaula.
Birnin Paris din Faransa ne zai karbi bakuncin wasannin da za a gudanar a cikin 2024.







