Me ya janyo saɓani tsakanin CAN da gwamnati kan sace ɗaliban Neja?

Asalin hoton, BBC/Umaru Bago/X
Kwanaki huɗu bayan sace ɗaliban makarantar St Mary da ke Papiri a jihar Neja, an riƙa samun saɓani tsakanin ƙungiyar CAN wadda ta mallaki makarantar da kuma gwamnti kan sace ɗaliban.
A ranar Juma'a ne aka wayi gari da labarin sace ɗaliban makarantar 303 da wasu malamai 12 a makarantar da ke yankin ƙaramar hukumar Agwara.
Tun da farko gwamnatin jihar ta ce sai da ta umarci rufe makarantun duka yankin da abin ya faru, sakamakon samun rahoton barazanar tsaro, amma makarantar ta yi gaban kanta wajen sake buɗe karatu ba tare da neman izinin gwamnati ba.
Sai dai cikin wata hira da BBC shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN reshen jihar, Bishop Bulus Dauwa Yohanna ya musanta iƙirarin gwamnan.
''Ba wanda ya ce mana mu rufe makaranta saboda barazanar tsaro, ba inda aka taɓa faɗa mana haka'', in ji shi.
Me ya janyo musayar yawun?
An fara samun saɓanin ra'ayi tsakanin gwamnati da ƙungiyar CAN, tun bayan da ƙungiyar ta ce ɗalibai 50 daga cikin waɗanda aka sacen sun kuɓuta.
Bayan da CAN ta fitar da sanarwar da a ciki ta ce tuni aka mayar da ɗaliban wajen iyayensu, ƴansanda suka ce suna da shakku game da labarin kuɓutar ɗaliban.
Ƴansandan sun ce sun buƙaci ƙungiyar ta ba su hujjar kuɓutar ɗaliban, amma ba su samu ba, don haka rundunar ta ce, "ba mu da tabbacin alƙaluman yaran da suka tsere da ma inda sauran suke a yanzu.".
Shi ma gwamnan jihar Umaru Bago ya bayyana cewa babu adadi a hukumance na yawan ɗaliban da aka sace a makarantar.
To amma mamallakin makarantar ya ce adadin haka nan yake.
Shi ma kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya nanata wannan batu cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Arise ranar Litinin.
Onanuga ya ce har yanzu ba tabbas game da adadin ɗaliban da aka sace a Neja.
"A yanzu da nake maka magana, an bar hukumomi cikin duhu kan adadin mutanen da aka sace. Kun ce an sace ɗalibai, to ku fito da sunayensu, ya kamata mu san abin da muke nema,'' in ji shi.
To sai dai shugaban CAN reshen jihar Neje, Bishop Bulus Dauwa Yohanna ya ce sun tattara adadin ɗaliban ne bayan da suka tantance ɗaliban da suke makarantar da waɗanda ba sa nan bayan faruwar harin.
'Gwamnati ba ta yi mana ƙoƙari'
Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Neja, Bishop Bulus Dauwa Yohanna ya zargi hukumomin ƙasar da rashin kataɓus a ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban.
A tattaunawarsa da BBC, Bishop Yohanna, wanda shi ne mamallakin makarantar, ya ce zuwa yanzu hukumomi ba su ɗauki wani 'matakin a zo a gani' ba kan batun ceto yaran da aka sace.
Bishop Yohanna ya shaida wa BBC cewa matakin da hukumomi suka ɗauka zuwa yanzu shi ne karɓar sunayen yaran da ƴanbindigar suka yi awon gaba da su.
''Zuwa yanzu ban san wani ƙoƙari da hukumomi ke yi fiye da karɓar sunayensu'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa kawo yanzu ba shi da masaniyar tura jami'an tsaro domin ceto ɗaliban.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Neja da gwamnatin tarayya su haɗa ƙarfi wurin guda domin ceto ɗaliban makarantar.
Ba mu samu bayanan da muke buƙata ba - Ƴansanda
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rundunar ƴansandan jihar ta shaida wa BBC cewa ba ta samu cikakkun bayanan da take neman kan batun sace ɗaliban daga jhukumar makarantar ba.
Cikin wata hira da BBC, kwamishinan ƴansandan jihar, CP Adamu Abdullahi Elleman ya shaida wa BBC cewa bai samu cikakkun bayanan da yake buƙata daga makarantar ba.
CP Elleman ya ce ya yi ƙoƙarin samun bayanai daga makarantar, ya yi magana da Shugabar makarantar kan adadin yaran da aka sace, amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.
''Sai ta ce ba za ta iya magana ba, amma in yi magana da Bishop ɗinsu na Kwantagora, kuma na yi aƙalla kwana biyu ina nemansa, amma ban same shi ba'', in ji shi.
Kwamishinan ƴansandan ya ce adadin da aka fitar, hukumomin makarantar ne suka fitar, amma rundunarsa ba ta iya tabbatar da adadin ba, sannan makarantar ba ta tuntuɓe shi domin sanar da shi a hukumance ba.
Dangane da labarin kuɓutar da ɗalibai 50 kuwa, kwamishinan ƴansandan ya ce nan ma ba shi da masaniya, saboda ba a yi masa cikakken bayanin yadda aka kuɓutar da su ba.
''Na tambaye su wa ya kuɓutar da su, ba amsa, yaushe aka kuɓutar da su, nan ma ba amsa, wa ya haɗa yaran da iyayensu bayan kuɓutar da su, nan ma dai babu amsa'', in ji shi.
Sai dai CP Elleman ya ce hakan ba zai hana rundunar yin iya baƙin ƙoƙarinta na ceto ɗaliban ba.
To amma shugaban CAN na jihar Neja, wanda ya mallaki makarantar, ya ce sun samu bayanan dawowar ɗaliban ne bayan da iyayensu suka riƙa kiransu suna faɗa musu cewa yaransu sun dawo.












