Tarihin yadda rikicin Falasɗinawa da ƴan Isra'ila ya faro

Wani sojan Birtaniya riƙe da bindiga ranar 1 ga Mayun 1948

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani sojan Birtaniya riƙe da bindiga ranar 1 ga Mayun 1948
Lokacin karatu: Minti 11

Ana ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar Balfour da ke goyon bayan ginawa Yahudawa matsugunai a yankunan Falasɗinawa yayin da Firaiministan Birtaniya ya yi wani alƙawari mai sharaɗi ga Falasɗinawa, shekaru 77 bayan da Birtaniya ta fice daga Falasɗinu.

A ranar 29 ga Yuli, Starmer ya sanar cewa ƙasarsa, wadda ke da muradi kan yankin, har da filayen da ke tsakanin Kogin Jordan da Bahar Rum, za ta amince da "ƙasar Falasɗinawa" a watan Satumba sai dai idan Isra'ila ta ɗauki wasu muhimman matakai a Gaza ciki har da amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ga jerin abubuwan tarihi game da muhimman abubuwan da suka faru lokacin da Birtaniya ke da iko da Falasɗinu.

Rashin adalci da saɓa alƙawari

Wani sojin Birtaniya na yin ƙasa-ƙasa da tutar ƙasarsa a karo na karshe ranar 30 ga Yunin 1948 a tashar jirgin ruwa ta Haifa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani sojin Birtaniya na yin ƙasa-ƙasa da tutar ƙasarsa a karo na karshe ranar 30 ga Yunin 1948 a tashar jirgin ruwa ta Haifa

Tarihin na nuna Birtaniya na da wani nauyi na goyon bayan maslahar kafa ƙasa biyu, in ji Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy kamar dai yana uni da zamanin da Birtaniyar ke jan ragamar yankin.

Da yake jawabi a wani taron Majalisar Ɗinkin Duniya game da samar da ƙasar Falasɗinu da kuma aiwatar da maslahar samar da ƙasa biyu, in ji Lammy. An bankaɗo rashin adalcin da ya faru a tarihi saboda yarjejeniyar Balfour na kunshe da wani alƙawari da yake a fayyace cewa babu abin da za a yi da zai murƙushe haƙƙokin farar hula na Falasɗinawa da kuma kare addininsu, wanda shi ma ba a mutunta ba.

Julie Norman, wata Farfesa a jami'ar University College da ke London, ta shaida wa BBC cewa matakin Starmer na amincewa da ƙasar Falasɗinu ya dogara ne kan halin da ake ciki; yanayin cin zarafi a yankin Gaza, da ta'azzarar tashin hankali a Gaɓar Yamma da kuma shirin tsugunar da mutane da kuma ƙwace yankin.

"Birtaniya ta daɗe tana alƙawarin goyon bayan maslahar samar da ƙasa biyu kuma tana son ta tabbatar da hakan kafin ya gagara," in ji Noman, wata ƙwararriya kan manufofin Gabas ta Tsakiya sai dai ta bayyana daɗaɗɗen tarihin kasancewar Birtaniya a Falasɗinu tsawon ffiye da shekara 100.

Me ƙudirin Birtaniya ke nufi?

Sojojin Birtaniya na ficewa daga tashar ruwa ta Haifa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin Birtaniya na ficewa daga tashar ruwa ta Haifa

Ƙudirin shi ne wanda ƙungiyar ƙasashe suka gabatarwa ɗaya daga cikin mambobinsu don jan ragamar ƙasashen da ke ƙarƙashin ikon Jamus ko mulkin Daular, na wani ɗan lokaci, a cewar kundin bayanai na Encyclopedia Britannica da nufin bunƙasa su ta fannoni daban-daban a wani ɓangare na shirin samun ƴancin kai.

Bayan ƙarshen yaƙin duniya na ɗaya, an raba kudirin zuwa mataki uku - bisa la'akari da matsayinsu da matakin siyasa da ci gaban tattalin arziki sannan aka miƙa su ga ƙasashen da suka yi nasara.

Rukuni na farko ya kunshi ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin Daular Ottoman kamar Iraƙi da Syria da Lebanon da Falasɗinu, kamar yadda yake ƙunshe a kundin Encyclopedia Britannica.

Ana ganin waɗannan yankunan sun samu wani mataki na ci gaba da ke buƙatar a ba su ƴancinsu amma za su ci gaba da kasancewa bisa ikon ƙasashen da suke da iko kansu har sai sun samu cikakken ƴancin cin gashin kai, a cewar kundin bayanan.

Duka yankunan da ke rukuni na farko sun samu ƴanci a 1949, ban da "ƙasar Falasɗinu".

Ina Falasɗinu take a taswirar Sykes-Picot?

Taswirar Sykes-Picot ta 1916

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Taswirar Sykes-Picot ta 1916, inda aka miƙa yankunan da ke rukunin A ga Faransa, yankunan runkunin B ga Birtaniya

A 1916, lokacin yakin duniya na ɗaya, an kammala yarjejeniyar Sykes-Picot da aka ƙulla a asirce tsakanin Birtaniya da Faransa kan raba yankunan da ke ƙarƙashin mulkin Daular Ottoman. Wakilan gwamnatin Faransa, François Georges-Picot da na gwamnatin Birtaniya, Mark Sykes, sun amince a sanya Falasɗinu a ƙarƙashin ikon ƙasashe ciki har da Birtaniya da Faransa, a cewar kundin bayanai na Encyclopedia Britannica.

Bayan ƙarshen yakin duniya na ɗaya, Firaiministan Faransa Georges Clemenceau da Firaiministan Birtaniya David Lloyd George sun gana domin yin garambawul a yarjejeniyar ta Sykes-Picot, a lokacin ne Faransa ta miƙa "Falasɗinu" da yankin Mosul, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Wasiƙa mai kalmomi 67

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Falasɗinu na karƙashin daular Ottoman har zuwa 1917 lokacin da sojojin Birtaniya suka kutsa yankin bisa jagorancin kwamanda Edmund Allenby.

A ranar 2 ga Nuwamban 1917, Sakataren harkokin wajen Birtaniya Arthur Balfour ya aika wata wasika da aka buga zuwa ga Walter Rothschild, wani jagoran Yahudawa a Birtaniya, wadda gwamnatin Birtaniya ta amince da ita kuma take buƙatar sa ya gabatar da bayanan da ke kunshe cikin wasiƙar ga ƙungiyar Zionist Federation da ke fafutukar ganin an samar da matsugunni na dindindin ga Yahudawa.

Wasiƙar ta ce: "Gwamnatin mai alfarma na kallon batun kafa matsugunni ga Yahudawa a yankin Falasɗinawa kuma za ta yi duk mai yiwuwa wajen cimma wannan muradi."

Wasiƙar ta yi alƙawarin ba za ta take "haƙƙokin gudanar da addini ga al'umomin da ba Yahudawa ba, ko haƙƙoƙi da matsayin siyasar da Yahudawa ke cin gajiya a wasu ƙasashen."

Wasikar mai kalmomi 67, ba wai kawai tana aikewa da saƙo ba ne, amma ta kasance wani lamari da ya sauya tafiyar Falasɗinawa da Yahudawa da kuma Gabas ta Tsakiya.

Kwafin wasikar da aka fi sani da "Yarjejeniyar Balfour"

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kwafin wasikar da aka fi sani da "Yarjejeniyar Balfour"

Wannan takaitaccen rubutun :gagarumar nasara" ce ga jagoran masu kare aƙidun Yahudawa a Birtaniya, Chaim Weizmann, wanda daga bisani ya zama shugaban farko na ƙasar Isra'ila inda kuma ya yi koƙari sosai na cika wannan alƙawarin.

Falasɗinawa da Isra'ilawa sun yi hannun riga a hangensu game da yarjejeniyar. Isra'ila na yaba matakin a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da suka taimaka aka kafa ta a 1948 inda kuma ta ƙarfafa wa Yahudawa gwiwar komawa wajen da zama. Sai dai Falasɗinawa na ganin yarjejeniyar ta ba da gudummawa ga ƙwace filayensu, lamarin da ya ɗaiɗaita Falasɗinawa a 1948 da tserewar Falasɗinawa 760,000.

A 2021, wata kotun Falasɗinawa ta ce yarjejeniyar Balfour "ta daƙile wa Falasɗinawa haƙƙoƙinsu na shari'a da siyasa da na bil adama tare da hana su damarsu ta samun ƴancin ƙasarsu."

Da yake magana da BBC, Julie Norman ya bayyana cewa Yarjejeniyar Balfour na da matsaloli kasancewar ta amince da tabbatar da ƴancin addini ga Falasɗinawa ba wai haƙƙoƙinsu na ƙasa ko siyasa ba (daidai lokacin da ta yi alƙawarin samar dawuri ga Yahudawa).

Norman na ganin Lammy na bisa turba cewa Birtaniya ta ƙi cika alƙawurranta, a cewar Yrajejeniyar Balfour, domin kare ƴancin Falasɗinawa.

Bayanan ƙudirin

Taron San Remo da aka yi a Italiya cikin 1920 ya amince da ƙudirin da ya kamata ya shirya wa ƴancin kai wanda kuma aka danƙa shi ga Birtaniya (Falasɗinu da Gaɓar Gabashin Kogin Jordan da Iraƙi) da kuma Faransa (Syria da Lebanon).

A 1922, bayan murƙushe juyin juya hali a Falasɗinu da Syria da Iraƙi, ƙungiyar ƙasashe ta amince da sanya waɗannan yankunan a ƙarƙashin Faransa da Birtaniya.

Wasiƙar Balfour ta samar da doro na ƙudirin Birtaniya ga Falasɗinawa, wanda ya samu amincewar ƙungiyar ƙasashe a 1922.

Ƙungiyar ta amince da "ƙudirin" wanda a ƙarƙashinsa Birtaniya ta soma aiwatar da muradunta kan Falasɗinu, da ikon kafa wani yanayi na siyasa da mulki da tattalin arziki da zai ba da damar kafa matsugunni ga Yahudawa," a cewar AFP.

Abubuwan da suka faru a 1929

A 1929, Falasdinu ta gamu da tashin hankali da ya kai ga zub da jini. Bayanan abubuwan da suka janyo tashin hankalin sun janyo zanga-zanga da kuma taƙaddama kan damar shiga muhimmin wajen ibada na Western Wall.

Tashin hankalin ya bazu zuwa wurare da dama da ke wajen birnin Ƙudus har da birnin kuma ya ƙunshi Larabawa da Yahudawa da sojojin Birtaniya. Lamarin ya janyo mutuwar Yahudawa 133 da Larabawa 116.

Waɗannan lamura da suka faru ana kiransu da Juyin Juya Hali na Buraq.

Wajen ibadar na Western Wall tsarkakakke ne a wurin Yahudawa da Musulmai saboda yana da alaƙa da tarihin tafiyar Isra'i da Mi'iraji a tarihin Islama yayin da Yahudawa na kallonsa a matsayin wurin da ya rage na wurin ibadar da Solomon ya samar.

Bangon yana nan ta ɓangaren yammacin wurin da ke harabar masallacin Ƙudus da ke da muhimmanci ga Musulmi da Yahudawa.

Gagarumin Juyin Juya Halin Falasɗinu

Sojojin Birtaniya tare da Falasdinawa lokacin juyin juya halin da Falasɗinawa suka yi don adawa da Ƙudirin Birtaniya a Disambar 1938

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin Birtaniya tare da Falasdinawa lokacin juyin juya halin da Falasɗinawa suka yi don adawa da Ƙudirin Birtaniya a Disambar 1938

A 1921, zanga-zanga ta ɓarke a birnin Jaffa tsakanin Larabawa da Yahudawa. Larabawa sun kara da sojojin Birtaniya kuma rikicin ya bazu zuwa biranen Falasɗinawa. Rikicin ya shafe kusan mako biyu inda a lokacin aka kashe Larabawa 48 da Yahudawa 47, a cewar kamfanin dillancin labarai na Wafa.

A lokacin ne Gwamnatin Birtaniya ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan abin da ya janyo rikicin.

A 1925, Balfour ya ziyarci birnin Ƙudus domin ƙaddamar da Jami'ar Hebrew lamarin da ya janyo yajin aikin Falasɗinawa da kuma zanga-zanga.

An gudanar da taron farko na matan Falasɗinawa da suka yi fatali da ƙudirin a birnin Ƙudus a 1929.

A 1935 kuma, aka kashe Izz ad-Din al-Qassam, da ke fafatawa tare da wata ƙungiya kan kudirin Birtaniya, kusa da birnin Jenin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Wafa ya wallafa.

Ƙudirin na Birtaniya ya fuskanci juyin juya hali tsakanin 1936 da 1939, bayan da al'amura da dama suka fusata Falasɗinawa ciki har da ƙara tuɗaɗar Yahudawa da kisan Al-Qassam.

Masana tarihi sun ce fiye da Falasɗinawa 5,000 aka kashe, yayin da aka raunata kusan 15,000 a yayin juyin juya halin. Rahotanni sun kuma ce lamarin ya shafi ɗaruruwan Yahudawa da ƴan Birtaniya.

Wasiƙar neman kawo ƙarshen mulkin Birtaniya

Bayan juyin juya halin, an tilasta wa Birtaniya sake nazartar manufarta a Falasɗinu. Haka ne ya sa ta shirya taro a birnin London tare da gabatar da wata takarda a 1939 wadda ta taƙaita sayar da filaye ga Yahudawa a Falasdinu da kuma taƙaita ficewarsu na tsawon shekara biyar da aka fara ranar 1 ga Afrilun 1939.

Birtaniya ta yi alkawarin kafa ƙasar Falasɗinawa mai cin gashin kanta cikin shekara 10 - idan da yiwuwar hakan - yayin da Falasdinawa da Yahudawa za su riƙa karɓa-karɓa a batun tafiyar da gwamnati.

Wani Ba-Yahude yana jiran zuwan jirgin ƙasa ranar 1 ga Disambar 1933 a tashar jirgi ta Tel Youssef

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani Ba-Yahude yana jiran zuwan jirgin ƙasa ranar 1 ga Disambar 1933 a tashar jirgi ta Tel Youssef

Takardar ta ɗan yi magana kan shirye-shiryen kawo ƙarshen kudirin Birtaniya.

A Yulin 1946, mambobin ƙungiyar da ke kare aƙidun Yahudawa Irgun ta ƙaddamar da hare-hare tare da jefa bama bamai kan sojojin Birtaniya har da kai hari kan otal ɗin King David da ke birnin Ƙudus. An kashe gomman sojojin Birtaniya da jami'ai.

An kashe mutane 91 a harin da ƙungiyar kare muradun Yahudawa ta kai a birnin Ƙudus ranar 22 ga Yulin 1946

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kashe mutane 91 a harin da ƙungiyar kare muradun Yahudawa ta kai a birnin Ƙudus ranar 22 ga Yulin 1946

Hijirar Yahudawa

Tun ƙarni na 19, Falasɗinu ta ga shige da ficen Yahudawa ƙalilan amma lamarin ya ƙaru a karshen ƙarni na 19 da kuma farkon ƙarni na 20 bayan da aka kafa ƙungiyar masu kare aƙidun Yahudawa wadda ta mayar da hankali ajen ganin an samar wa Yahudawa ƙasarsu a yankin Falasɗinawa.

Nuna son kai ga Yahudawa a Turai da Rasha ya ƙara janyo tuɗaɗar Yahudawa zuwa Falasɗinu.

Adadin Yahudawa da ke Falasɗinu ya kai 47,000 a 1895 idan aka kwatanta da 24,000 a 1882, a cewar AFP.

An kuma sake ganin zugar Yahudawa tsakanin 1904 da 1914 inda a jumulla, yawan Yahudawa daga Rasha da suka isa wajen ya kai tsakanin 35,000 da 40,000.

Yahudawa na barin Poland domin zuwa Falasdinu a1922

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yahudawa na barin Poland domin zuwa Falasdinu a1922

Tasowar ƴan Nazi a Jamus da kuma kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa a can lokacin yaƙin duniya na biyu ya janyo ƙaruwar zuwan Yahudawa zuwa Falasɗinu.

Yarjejeniyar Balfour ta ƙarfafa wa Yahudawa gwiwar su yada zango a Falasɗinu, inda tsirarun Yahudawa ke zaune tare da Larabawa kafin 1917.

A 1917, Yahudawa ba su wuce fiye da kashi 7 cikin 10 ba na yawan al'ummar da ke Falasɗinu.

Lokacin da aka gabatar da tsarin raba Falasɗinu a 1947, Falasɗinawa miliyan 1.3 da Yahudawa 600,000 ne ke zaune a wajen. A cewar tsarin, Yahudawa sun samu kashi 54 cikin 100 na filin duk da cewa sun ƙunshi kashi 30 cikin 100 na al'ummar, a cewar AFP.

Yawan Yahudawa a Falasɗinu ya zarce 700,000 a 1948, a cewar Wafa.

Dokar kome ta bai wa Yahudawa shaidar zama ƴan Isra'ila musamman waɗanda suka je da burin zama a Isra'ila.

Raba ƙasar Yahudawa da Falasɗinu

A 1947, zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da ƙudirin 81 wanda ya buƙaci a kafa ƙasar Yahudawa da Larabawa a yankin Falasɗinu."

Ƙudirin ya samu goyon bayan ƙasashe 33, ciki har da Amurka da Ƙungiyar Soviet da Faransa yayin da ƙasashe 13 suka yi adawa da shi ciki har da ƙasashen Larabawa sai kuma ƙasashe 10 ƴan ba ruwanmu har da Birtaniya.

Jagororin Yahudawa sun amince da tsarin da ya ba su kashi 56 na filin amma ƙungiyar ƙasashen Larabawa suka yi fatali da shi.

An ayyana kafa ƙasar Isra'ila ranar 14 ga Mayun, 1948.

Kwana guda bayan nan, yaki ya ɓarke tsakanin ƙasashen Larabawa da Isra'ila inda kuma yaƙin ya ƙare Isra'ila tana da iko da kashi 77 cikin 100 na filin.

Kashe-kashe da azabtarwa

A 2022, wani ƙorafi mai shafuka 300 ya nemi a amince tare da neman yafiyar take dokokin da aka yi yayin mulkin Birtaniya a Falasdinu.

Lauyan Birtaniya Ben Emmerson KC, tsohon wakili na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya kan ƴancin bil adama da yaƙi da ta'addanci, ya shaida wa BBC cewa tawagar masana shari'a ya bankado shaidu na irin miyagun laifukan da sojojin Birtaniya suka aikata kan Falasɗinawa."

An kai wasu Falasɗinawa da aka ɗaurewa hannaye da ankwa gidan yari a Birnin Ƙudus lokacin da sojojin Birtaniya suka sanya dokar hana fita ranar 26 ga Oktoban 1938

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kai wasu Falasɗinawa da aka ɗaurewa hannaye da ankwa gidan yari a Birnin Ƙudus lokacin da sojojin Birtaniya suka sanya dokar hana fita ranar 26 ga Oktoban 1938

Wani nazari da BBC ta yi kan abubuwan tarihin da suka faru ya haɗa da batun kashe-kashe da azabtarwa da amfani da mutane a matsayin shinge da rusa gidaje a matsayin ladabtarwa. Akasarin waɗannan ta'annatin sun faru ne a lokacin da Birtaniya ke Falasdinu.

Abin da Birtaniya ta yi a Falasɗinu ya kasance na "tashin hankali" a cewar masanin tarihi Farfesa Mathew Hughes, wanda ya ce dabarun Birtaniya ba su kai matakin cin zalin da aka gani ba a wasu yankunan.

Gidan ajiye kayan tarihi na Imperial War da ke London na ajiye da tarihin sojojin Birtaniya da dama da ƴansanda a Falasdinu.

Wasu bayanan tarihin sun bayyana samamen da aka yi da kuma azabtarwa da amfani da bil adama a matsayin kariya.

Ma'aikatar tsaro ta Birtaniya, cikin wata sanarwa ta ce ta san da zarge-zargen da aka yi wa sojoji a tsukin lokacin kuma duk wata hujja da aka gabatar sai an yi cikakken nazari a kai.

"Dole Birtaniya ta fuskanci hukunci kan ta'annatin da ta tafka a baya."

An sabunta wannan maƙala inda ta ƙunshi muhimman bayanai ranar 11 ga Agustan 2025.