Yadda mutane ke fama da matsanancin ciwon son cin kasuwa

    • Marubuci, Nia Price
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ga wasu mutane yawan sayen abubuwa ne ke sanya su nishaɗi da jin daɗi.

Amma me zai faru idan kullum burinka shi ne yin sayayya.

Yayin da take tsaye zagaye da ledojin sayayya cike da riguna da kayan sa wa, Lucy ta ce za ta iya shafe tsawon sa'a 14 a rana tana sayen sababbin tufafi.

Mai shekara 37, rayuwarta tamkar mafarki, amma Lucy ta tabbatar da cewa sayayya fiye da ƙima ta ƙanƙane rayuwarta.

"Ni nakan ji a raina sayen tufafi ne kan gaba da komai a rayuwata,'' in ji ta.

Kawo yanzu Lucy ba ta san adadin tufafinta ba, amma za su iya cika ɗaki mai fadin sakwaya mita uku.

"Tufafi tamkar garkuwa ce a gareka, inda za su hana ka fuskantar ainihin rayuwa,'' in ji ta.

Lucy ta buɗe shafin Instagram inda take wallafa duka sayayyar da take yi, inda take kashe dala 930 a kowane mako, ciki har da cin bashin dala 16 a kowane mako.

''Ciwon sayayya'

Ta ce ganin masu amfani da shafukan sada zumunta da manyan tufafi na ƙara tsumata.

Ta ce ba ta fahimci hakan ba sai bayan da likitanta ya sanar da ita cewa tana da ciwon sayayya.

Ta ƙara samun bayani game da lalaurar tata a lokacin wani taron ɗabi'ar masu lalurar son sayayya.

Ciwon sayyayya shi ne mutum ya zaƙu wajen sayen wani abu ta yadda ba zai iya hana kansa sayen wannan abu ba, koda kuwa abun ba shi da amfani a gare shi.

Kawo yanzu babu wasu cikakkun alƙaluma na adadin mutanen da ke fama da wannan cuta.

Sai dai wani bincike ya nuna cewa kashi biyar ckin 100 na matasa na fama da ita, kodayake wani sabon bincike ya nuna cewa adadin zai ƙaru zuwa kashi 10 cikin 100, tun bayan annabar korona.

Natalie na da abin da ta kira "shagon kayayyaki," da ke ɗauke da abubuwan amfani fiye da 100,000 a wani ɗaki da ke gidanta a unguwar Rotherham a arewacin Ingila.

Ciwon sayayyar da matar mai shekara 40 ke da shi ya sanya ta sayen abubuwa da dama, ciki har da abubuwa masu launuka daban-daban.

Ɗakin nata cike yake da ɗaruruwan man goge baki da abubuwan wanke-wanke kusan 3,000.

"Ta kai lokacin da zan fita, ba kuma zan dawo ba har sai na cika motata da kayayyaki,'' in ji ta.

A lokacin da take kan ganiyarta a kowacce rana takan kashe kusan dala 4 ,000 kan sayen kayayyakin tsaftec jiki.

"Bana dakatawa ba kuma na tsayawa, duk abin da na gani a yanar gizo zan ji ina sonsa, koda kuwa ba zan yi amfani da shi ba,'' kamar yadda ta bayyana.

A baya-bayan nan matar - mai ɗa guda - ta kashe dala 1,300 kan turare, kuma ta bayyana cewa ana binta bashin na wasu turaruka kusan 400 da ta saya cikin sama da shekara biyu.

BBC ta tattaunada wasu mutum 15 da ke jin sun kamu da cutar sayayya.

Duka waɗannan mutane na ganin cewa shafukan sada zumunta sun taimaka wajen kamuwa da cutar.

Masana sun ce abubuwan da ake sayarwa a shafukan sada zumunta sun ƙaru fiye da ninki a cikin shekara 10 daga kashi 12 cikin 100 a watan Mayun 2015 zuwa kashi 27 cikin 100 a Mayun 2025.

hukumar kula da cinikayyar yanar gizo ta Birtaniya, ta bayar da rahoton cewa tallace-tallacen da ake yi a shafukan sada zumunta sun ƙaru da kashi 20 cikin 100 a shekarar da ta gabata.

Zaheen Ahmed, daraktan ƙungiyar likitocin kula da masu cutar sayayya da ke gudanar da cibiyoyin bayar da magungunan cutar a Birtaniya ya ce suna samun ƙaruwar masu ɗauke da ciwon.

Ya ce za a iya kwatanta lalurar da jarabtuwa da shaye-shaye.

Ahmed ya ce shafukan sada zumunta na da matuƙar tasiri wajen assasa cutar.

Alyce kuwa ta fara amfani da tsarin bashi tun tana da shekara 18 domin sayen abubuwa.

Kafin Alyce ta ankara ta tara wa kanta bashin dala 12,000, bayan kashe aƙalla dala 1,000 a wata, ciki har da sayen tufafi a yanar gizo.

"A duk lokacin da na ga wani sabu abu, sai na zaƙu don sayensa ta hanyar wannan tsari na bayar da bashi, amma idan na saye shi, ina buɗe shi sai in ji bai yi mini ba, dga nan sai haushi ya ƙume ni'', in ji ta.

Sai dai ta ce da zarar ta ske ganin wani tallen a shafukan sada zumunta sai ta sake zaƙuwa don mallakarsu.

Daga baya Alyce, ta samu nasarar rabuwa da ciwon sakamakon shawarwarin da likitocin cutar ke ba ta.

Kuma a halin yanzu ta samu nasarar rabuwa da bashin da ta ɗauki shekaru tana biya.

Hukumar Lafiya ta Birtaniya ta ce babu takamammen maganin wannan ciwo ya zuwa yanzu, sai dai shawarwari da likitoci kan bayar.

Ɗaya daga cikin dalilan hakan kuwa an samu saɓani fahimta tsakanin masana kan yadda za a karkasa cutar.

Yayin da wasu ke kallonta a matsayin matsalar ɗabi'a, wasu na kallonta a matsayin matsalar damuwa ko ƙwaƙwalwa.

Farfesa Ian Hamilton na Jami'ar York, ya ce cutar sayayya na mayar da mutane masu ''taɓin ƙwaƙwalwa."

Masanin ya ce fanin kasuwanci ya ɓullo da wasu dabaru na amfani da yanar gizo wajen ɗauke hankalin mutane.

Shi kuwa kakakin NHS ya ce hukumar ta ɓullo da wani shiri na bai wa masu ciwon sayayya shawarwari kan yadda za su rabu da ciwon.

Inda ya buƙaci duk wanda ke da lalurar ya tuntuɓi jami'an hukumar domi hada shi da ƙwararrun masu bayar da shawarwarin.