Man United za ta tsawaita ƙwantriagin Evans

Jonny Evans

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United tana tattaunawa da mai tsaron baya, Jonny Evans kan tsawaita yarjejeniyar ya ci gaba da taka leda a ƙungiyar.

Mai shekara 36, ya sake komawa Old Trafford daga Leicester City, bayan shekara takwas da ya taka leda a ƙungiyar.

Tun farko ɗan kasar Ireland ta Arewa ya je ƙungiyar da yin atisaye a lokacin da ake shirin tunkarar kaka da aka kammala, amma sai aka ba shi yarjejeniyar kaka daya, bayan da Erik ten Hag ya ga ƙwazonsa.

Daga nan Evans ya buga wa United wasa 30 a kakar da ta wuce har da karawar da ya shiga canji a FA Cup da Manchester City a Wembley.

Haka kuma ƙungiyar ta sanar da shirin karawa mai tsaron raga, Tom Heaton sabuwar yarjejeniya ta kuma tuntuɓi Omari Ferson ko zai ci gaba da zama a Old Trafford.

Ferson mai shekara 19 ya fara buga wa United Premier League cikin Fabrairu a wasan da ta ci Wolverhampton 4-3, wanda ya bayar da ƙwwallon da Kobbie Mainoo ya zura na hudu a raga a Molineux.

Ɗan kasar Ingila ya buga wa United wasa shida, amma har yanzu bai nuna cewar zai ci gaba da taka leda a ƙungiyar ba, duk da sabon ƙunshin ƙwantiragin da aka yi masa tayi.

To sai dai Brandon Williams da Anthony Martial da kuma Raphael Varane za su bar ƙungiyar, wadanda yarjejeniyarsu za ta kare ranar 30 ga watan Yuni.

Williams ya buga wasanninj aro a bara a Ipswich, amma rabon da ya taka leda tun 29 ga watan Disamba, sakamakon raunin da ya ji da ta kai ya koma Old Trafford.

Rabon da mai tsaron bayan ya buga wa United tamuala tun cikin Satumabr 2022.