Abubuwan da ba su kamata a faɗa wa mace mai ciki ba

Asalin hoton, Getty Images
Shin abu ne mai kyau a yi wa mata masu juna biyu hirar da ta shafi ciki da yadda ake haihuwa, ko kuwa hakan zai iya janyo masu fargaba da tsoro?
Lokacin da ƴar jarida, Rose Stokes ta samu cikinta na farko, ta sha fama da labarai masu ban tsoro da tayar da hankali da suka shafi yadda ake haihuwa da kuma rainon ƴaƴa, daga ƙawaye da abokan arziki da ma baƙi.
Ƙwararriya, Anna Mathur ta bayar da shawara kan abubuwan da ya kamata a faɗa wa masu ciki da kuma waɗanda ya kamata a kiyaye.
Labarin Rose

Asalin hoton, Getty Images
Rose ta bayar da labarin ta tana cewa: "Na je shagon wanke kai gabanin hutun kirsimati.
Ɗaya daga cikin masu kula da wajen ta fara tambaya ta ko cikina ya kai wata nawa, ko na fara fuskantar wasu ƙalubale.
Daga nan sai ta fashe da dariya sannan ta bani labarin yadda nata cikin da haihuwar takasance, cewa haihuwa tana da wahala da zafin gaske. Ta kuma bada labarin dukkan azabar da ta sha daki-daki.''
Rose ta ce wannan labari ya tayar mata da hankali kuma ya matuƙar tsorata ta.
Amma ta yaya za mu bayar da shawara ga masu ciki ta yadda ba za mu jefa su cikin tsoro da fargaba ba?
A tambaya ko suna cikin ƙoshin lafiya kafin bayar da wata shawara
Rose ta ce "Kamar yadda mata suka sani, wannan lokaci ne mai sarƙaƙƙiya sosai, yanayin mu yana sauyawa sosai cikin ƙanƙanin lokaci,''
Ta ƙara da cewa "Bincike ya nuna cewa daga uwa mai ciki har zuwa jaririn da take ɗauke da shi duk suna buƙatar natsuwa da kwanciyar hankali a lokacin da mace ke da juna biyu.
Don haka saboda me za a faɗa masu labari mai tayar da hankali? Zai fi dacewa a tambayi hali da suke ciki kuma a saurare su sannan a tambaya ko suna buƙatar wata shawara.
Wannan zai bai wa mai ciki damar tsayawa ta yi tunani kuma ta fahimci ko lokacin da ake maganar ya dace ta saurari zancen.''
A mutumta zaɓin su, idan suka ce basu buƙatar jin labarin da za a basu
"Ina da wasu shawarwari ga mata masu ciki,'' in ji says Anna, "Za su iya fuskantar masu neman ba su labari marar daɗi da irin nasu salon.
A misali za su iya cewa 'kin kyauta da kika bani labarin yadda ta kasance da ke, amma zan fi so in mayar da hankali ga abubuwan da za su taimaka mani da kuma fata nagari.''
Bayar da labarin wahala da tayar da hankali ga macen da ke cikin natsuwa da walwala zai iya ƙarfafa mata gwiwa, amma ga macen da ba ta cikin natsuwa sauraron irin wannan labarai zai jefa tsoro da rashin tabas a zuciyarta. Irin wannan labari yana janyo tsoro.
"Idan ana magana da mace mai ciki, to ki tuna da yanayin da kika shiga a lokacin tai haihuwar. A madadin faɗa masu labari mai ban tsoro, sai a kawo labarin da zai ƙarfafa masu gwiwa da kuma kwantar masu da hankali.''
A fahimce wadda ake magana da ita
"A lokuta da dama idan ana bayar da labari mai ban tsoro game da haihuwa, ko kuma ana gargaɗi kan abubuwan da ake yi da waɗanda ba su kamata a yi ba, masu bayar da labarin ba su cika la'akari da mai sauraron su ba; su dai kawai suna bayar da labarin halin da suka tsinci kansu a lokacin nasu cikin kuma haihuwa,'' in ji Rose.
"Yana da kyau mu bayar da labarin abin da ya faru da mu, musamman ga sabon shiga, amma yana da muhimmanci sosai a yi la'aƙari da halin da wadda ake ba labarin za ta iya shiga.''
"Kowacce haihuwa tana da irin nata yanayin da take zuwa da shi. Wannan ne abu mai muhimmanci da ya kamata mu sani kafin bayar da shawara ga mai ciki.''

Asalin hoton, Getty Images
Kafin furtawa ko wallafa kalamanku, ku tabbata ba za su yi illa ga mai sauraro ko karatu
"Wayar da kai abu ne mai kyau, amma ba kowanne lokaci ba,'' in ji Anna.
Saboda wannan dalili, babu kyau mu riƙa bayar da labari mai sanya tsoro da fargaba ga masu ciki, kuma ko da za a yi hakan, kamata ya yi a bayar da labarin cikin tsari na tausayi da nuna an damu da halin da suke ciki da kuma ƙarfafa masu gwiwa.
An fi samun wannan matsala a kafafen sada zumunta inda ake bayar da labarin zafin haihuwa ƙarara ba tare da tattausa kalamai ba.
"Idan kika gane cewa irin wannan labari da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta suna tayar maki da hankali to kamata ya yi ki nisanta kanki da karanta su, don gudun kada su janyo maki tsoro da fargaba.''
A mayar da hankali kan bayar da labari mai daɗi da ƙarfafa gwiwa
Anna ta ce "Lokacin da nake da ciki, wata mata ta taɓa tsayar da ni a kan titi, ta kalli cikina ta ce 'ƴan uku ne?' Da kyau, abin sha'awa! Na yi mamaki kuma na yi farin ciki sosai da jin kalamanta na fatan alheri. Don haka yana da kyau a fadi abin alheri don ƙarfafa gwiwar mai ciki!''
Rose ta ce "Jin labari mai daɗi da fatan alheri daga mutane abu ne mai dadin gaske ga mace mai ciki, musamman a zangon ƙarshe da mace ta kusa haihuwa. Ya kamata mu san cewa bayar da labari mai daɗi yana sauya tunanin mace mai ciki da kuma sanya ta cikin kwanciyar hankali.''










