Ƴanbindiga sun hana mu girbe amfanin gona - Al'ummar Zamfara

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da ake shirin bankwana da damina da shiga kaka a wurare da dama a Najeriya, daruruwan manoma na fargabar yadda za su girbe da kuma kwashe amfanin gonarsu a wasu garuruwa na yankin karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Wannan na faruwa ne sakamakon hare-haren da ƴanbindiga ke kaiwa garuruwan, inda suke sace dabbobi da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Yanayin ya jefa al'ummomin garuruwan cikin mawuyacin hali na fargabar rashin tabbacin abin da zai iya faruwa da su.

Yanzu haka dai jama'ar garuruwan da matsalar hare-haren 'yan bindiga ta addaba, har ta hana su girbin kayan amfanin gona, a yankin karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara, suna cikin wani yanayi irin na 'ga koshi ga kwanan yunwa', kuma matsalar sai dada ta'azzara take, in ji wani mutumin yankin: ''muna cikin hali wand aba mu ma taɓa shiga tai ba a wannan ƙaramar hukuma, wanda amfanin gona ya kai, kowa na son zuwa ya ɗebe abunai, amma babu mai iya zuwa daji.

In ka je, za a kame ka a kai daji a ɗaure, a ce sai an kai kuɗin fansa''.

Mutumin ya ce abin da ƴanbindigar ke nema a biya kuɗin fansar ya wuce hankali, domin a kan mutum ɗaya sai su nemi a biya kuɗin da suka fi kuɗin da manomi zai samu idan ya girbe amfanin gonar nasa.

Ya ce ''Wata ɗaya zuwa yau kullum muna cikin wannan tashin hankali a ƙaramar hukumar mulki ta Shinkafi.''

Ya yi zargin cewa gwamnati daga matakin matakin tarayya zuwa jiha da ƙaramar hukuma duk sun zura ido ana yi wa al.'ummar yankin abin da aka ga dama.

''Waɗannan matsaloli suna faruwa ne a Birnin Yero da Jangeru da Shanawa da kuma ita kanta Shinkafi. Ko a jiya Talata da safe sun kawo harin, sun kama manoma, babu wanda zai iya fada maka ga iya mutanen da suka kama,'' in ji mutumin yankin.

Ya ce yanzu haka manoma sun fara asarar amfanin gonarsu saboda tsoron kada su je girbi su faɗa a hannun ƴanbindiga, inda ya ce sun koma suna bin dare domin shiga gonaki da samo ''ɗan abin da mutum zai kai a ci a gidan shi.''

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce tana sane da halin da jama'ar yankin Shinkafin ke ciki kuma tana ɗaukar matakan magance matsalar, in ji Mustafa Jafaru Kaura, babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Zamfara kan harkokin kafafen yada labarai ''Gwamnati tana yin duk mai yiyuwa domin ganin cewa an sharewa jama'a hawayen su,''

Ya kuma nanata iƙirarin da gwamnati ta sha yi cewa tana samun nasara a kan ƴanbindigar ''kusan ma in banda ita ƙaramar hukumar mulkin ta Shinkafi, yanzu ya zama tsohon labari a jihar Zamfara ka ji barazanar ƴanbindiga a kan manoma.''

Mustafa Jafaru Kaura ya ce gwamnatin jihar ta bayar da umarni ga jami'an tsaro da kuma shugaban ƙaramar hukuma domin bincike da kuma ɗaukar mataki na gaske a kai.

Mutanen garuruwan da wannan matsala ta tsaro ta yi wa katutu, a yankin na Shikafi a jihar Zamfara dai, shi ne kada wannan tabbaci da gwamnatin ke bayar wa ya zamo ''irin wanda aka saba a baya ne.''