Yaushe Ronaldo zai cika burinsa na zura ƙwallo 1000?

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cristiano Ronaldo ya koma taka leda a Al-Nassr ta Saudiyya ne a 2022
Lokacin karatu: Minti 3

Ƙyaftin ɗin tawagar Portugal, Cristiano Ronaldo ya ce ba zai yi ritaya daga buga tamaula ba, har sai ya zura ƙwallo 1,000 a raga.

Mai shekara 40 ya ci wa Al-Nassr biyu a wasan da suka doke Al Akhdoud 3-0 a gasar tamaula ta Saudiyya ranar Asabar, kenan jimilla ya zazzaga 956 a raga a wasan da ya buga wa ƙungiyoyi da kuma Portugal.

Wanda ya koma taka leda a Al-Nassr a 2022, ya saka hannu a cikin watan Yuli kan yarjejeniyar da zai ci gaba da wasa a ƙungiyar da ke buga gasar tamaula ta Saudiyya har zuwa lokacin da zai haura shekara 42 da haihuwa.

A wani jawabi da ya yi lokacin da aka bayyana shi fitatcen ɗan ƙwallon Gabas ta tsakiya na bana a ranar Asabar, Ronaldo ya ce:

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

"Sha'awata tana da yawa kuma ina so in ci gaba da taka leda. Ba komai a tare dani zan iya buga wasa, ko a Gabas ta Tsakiya ko a Turai. Kullum ina jin daɗin buga ƙwallon kafa kuma ina so in ci gaba da bugawa.

Kun san burina. Ina so in lashe kofuna, kuma ina so in ci ƙwallo 1,000 kamar yadda dukkanku kuka sani. Tabbas zan kai wannan adadi, muddin ban samu rauni ba."

A wata hira da ya yi da Piers Morgan a watan da ya gabata, Ronaldo ya ce yana shirin yin ritaya daga buga kwallon kafa "ba da jimawa ba".

"Na yi tunanin zan fara shir-shiryen ritaya. Abu ne mai wahala, tabbas. Wataƙila zan yi kuka a lokacin," in ji Ronaldo.

Ronaldo ya ci ƙwallo 13 a wasa 14 a bana a Al-Nassr, wadda take kan teburin babbar gasar tamaula ta Saudiyya da tazarar maki huɗu.

Duk da cewar ɗan wasan tawagar Portugal ya zura ƙwallo 112 a wasa 125, kofi ɗaya Al-Nassr ta ɗauka tare da shi - Gasar zakarun Turai ta Araba a 2023 tun bayan da ya koma ƙungiyar.

Ronaldo ne kan gaba a yawan ci wa tawagar Portugal ƙwallaye mai 143 a raga da cin 460 a Real Madrid, kuma shi ne ya fara zura ƙwallo sama da 100 a kowacce ƙungiya huɗu da ya haɗa da Manchester United da Real Madrid da Juventus and Al-Nassr.

A cikin watan Nuwamba Ronaldo ya sanar cewar gasar da za a buga ta cin kofin duniya a Amurka da Canada da kuma Mexico, ita ce ta karshe da zai halarta.

Shi ne ya yi wa Portugal ƙyaftin da ta lashe gasar cin kofin nahiyar Turai wato Euro 2016 a Faransa - babban kofin farko da kasar ta ɗauka a fannin tamaula kenan.

Yaushe zai cika ƙwallo 1000?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yanzu dai saura ƙwallo 44 ne Ronaldo ya cika ƙwallo 1000 da yake da burin samu kafin ritayar.

Tun bayan zuwansa Al-Nassr, Ronaldo ya zura ƙwallo 112 a wasa 125 da ya buga.

Idan ya ci gaba da zura ƙwallo haka, zai cika ƙwallo 1000 a cikin minti 4,303 da zai buga domin cike ƙwallo 44 da suke rage masa.

Idan aka yi la'akari da minti 4,303 da yake buƙata, ke nan zai buga wasa 48, wanda ake hasashen zai iya samu a kakar wasannin 2026 zuwa 2027.

Idan ya ci gaba da zura ƙwallo yadda yake zurawa a yanzu, sannan ya kasance lafiya ƙalau, zai iya ƙarasawa zuwa ƙwallo 984 kafin a fara gasar cin kofin duniya ta gaba.

Idan kuma ya ƙara yawan zura ƙwallo, zai iya samun cike sauran ƙwallayen da yake buƙata a gasar cin kofin duniya.

Sai dai yana buƙatar ya buga kusan dukkan wasannin da suke rage a kakar bana, sannan ya ci gaba da samun nasarar zura ƙwallaye kamar yadda yake yi a yanzu.

Amma abin da zai fi zama na tabbas shi ne Ronaldo zai samu nasarar cike ƙwallo 1000 ne a kakar 2026-2027, amma zai iya samun nasarar cika burinsa kafin lokacin.