Akwai yiwuwar an aikata laifukan yaƙi a Gaza - Amnesty

Wani gini mai hawa hudu inda aka lalata mutane 42 daga dangin Nabhan a wani harin da Isra'ila ta kai ranar 13 ga Mayu.

Asalin hoton, Reuters

Akwai yiwuwar an aikata laifukan yaƙi a faɗan da aka gwabza tsakanin Isra`ila da Falasdinawa a Zirin Gaza a watan da ya gabata, in ji Amnesty.

Wani rahoto da ƙungiyar kare haƙƙin bil'adam ta fitar ya kammala da cewa sojojin Isra'ila sun kai hare-hare ta sama wanda ga dukkan alamu sun kashe Falasɗinawa fararen hula.

Har ila yau, ta ce ta harba makamin roka na ƙungiyar Jihad islami ta palasdinawa (PIJ) ta kashe fararen hular isra`ila da falasdinawa.

Amnesty na kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ta yi bincike.

Dakarun tsaron Isra'ila (IDF) ta ce tana gudanar da ayyukanta ne bisa ka'idojin da dokokin ƙasa da ƙasa suka tanada, kuma ta yi kokarin rage cutar da fararen hula da doka ba ta bukata ba.

Kakakin PIJ ya ce kungiyar ta yi maraba da rahoton na Amnesty.

Falasdinawa 34 da Isra'ila daya ne aka kashe a sabon fadan kan iyaka, wanda ya barke a ranar 9 ga watan Mayu kuma ya kawo karshe bayan kwanaki biyar da Masar ta tsagaita wuta.

Ya fara ne lokacin da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai hare-hare cikin dare inda suka kashe manyan kwamandojin reshen soja na PIJ uku a gidajensu da kuma fararen hula 10 da suka hada da 'yan uwa da makwabtan mutanen.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amnesty International ta ce jefa bama-bamai a wuraren da jama'a ke da yawa a lokacin da iyalai ke barci ya nuna cewa "wadanda suka shirya hare-haren da kuma wanda suka ba da izinin kai hare-haren sun yi tsammanin kai harin ba tare da kula da illar da zai ma fararen hula ba." "Kai hari da gangan, laifin yaƙi ne," yayi gargadi.

Rundunar ta IDF ta ce a yayin fadan da ya biyo baya, jiragenta sun kai hari sama da 400 na soji na PIJ tare da kashe wasu manyan kwamandojin reshen sojinta guda uku, wadanda ta daura ma alhakin harba rokoki da dama kan Isra'ila a makon da ya gabata.

Amnesty ta binciki hare-hare tara, ciki har da wadanda aka kaiwa kwamandojin PIJ uku a gidajensu.

Rundunar ta IDF ta ce "ta yi kokari da dama don rage cutar da fararen hula a Zirin Gaza, ciki har da jinkirtawa da ma soke hare-haren da aka shirya yi a lokacin da aka gano fararen hular da ba zato ba tsammani."

"Hukumar ta IDF ta kai hare-hare ne bayan tantance hakikanin lokaci kafin harin cewa barnar da ake sa ran za a yi wa fararen hula da dukiyoyin jama'a ba za ta wuce gona da iri ba dangane da fa'idar da sojoji ke da shi a harin, a cewar bayanan da ta samu a halin da ake ciki. " ya kara da cewa.

Wani harin da aka kai a ranar 9 ga watan Mayu a wani gida a birnin Gaza ya kashe kwamandan kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinu Tareq Ezzedine da wasu fararen hula biyar

Asalin hoton, Reuters

Amnesty ta kuma ce ta gano wani nau'in barna mai yawa a Gaza sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai wanda "ta kasa cika abin da ya kebanta da kai hari kan gidaje da sauran kayayyakin fararen hula".

Ya ba da misali da harin da aka kai a ranar 13 ga watan Mayu na wani gini mai hawa hudu a sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya wanda ke da mutane 42 daga dangin Nabhan.

Amnesty ba ta sami wata shaida da ke nuna cewa an yi amfani da ginin wajen adana makamai ko wasu kayan aikin soja ba, ko kuma an harba rokoki a kusa.

"A binciken da muka yi, mun ji labarin bama-bamai da ke lalata gidaje, na ubannin da ke tono 'ƴaƴan su mata daga cikin ɓaraguzai, na wata matashiya da ta ji rauni a lokacin da take kwance riƙe da wani teddy bear," in ji darektan Amnesty a Gabas ta Tsakiya Heba Morayef.

"Mafi firgita fiye da wannan shi cewa, sai dai idan ba a hukunta masu laifi ba, za a sake maimaita wadannan munanan al'amuran."

Rundunar ta IDF ta ce: "Jihad na Islama yana gano cibiyoyinsa a cikin gine-ginen fararen hula kuma yana amfani da fararen hula a matsayin garkuwar dan adam.

"Sa'o'i da yawa kafin a kai hare-haren, IDF sun tabbatar da cewa an kwashe fararen hula daga gine-ginen ta hanyoyi daban-daban, kamar kiran tarho. Wadannan gine-ginen ba a kai hari ba har sai dai aka kwashe fararen hula da dama daga wuraren."

Kungiyar ta PIJ dai ta mayar da martani ne kan harin da Isra'ila ta kai inda ta harba rokoki sama da 1,400 zuwa Isra'ila, lamarin da ya tilastawa dubun-dubatar fararen hula fakewa a matsugunan bama-bamai.

Rundunar ta IDF ta ce 1,139 ne suka tsallaka zuwa cikin ƙasar Isra'ila gaba daya, kuma kusan 430 ne suka nufi yankunan da ke da yawan jama'a, ta hanyar kariya daga makamai masu linzami.

An kashe wata mata ‘yar Isra’ila da wata ‘yar aikin Falasdinu da ke aiki a Gaza sakamakon makamin roka da suka kai a wani gida a Rehovot da wani gini a Shokeda.

Wata ‘yar Isra’ila ta mutu a lokacin da wani makamin roka na Falasdinawa ya afkawa wani gini a birnin Rehovot na Isra’ila a ranar 11 ga watan Mayu

Asalin hoton, EPA

Amnesty ta ce rokokin da suka yi kasa a Gaza sun kashe Falasdinawa fararen hula uku, ciki har da kananan yara biyu.

Rahoton ya ambato 'yan uwan ​​yaran na cewa sun mutu ne a lokacin da wani makamin roka ya afkawa titin al-Sahaba a birnin Gaza da yammacin ranar 10 ga watan Mayu.

A lokacin dai kungiyar ta PIJ ta musanta cewa wani makamin roka ya afkawa yankin tare da dorawa Isra'ila harin, amma shaidu sun shaidawa wani mai bincike cewa wasu mutane da ke da alaka da kungiyar sun cire ragowar roka bayan afkuwar lamarin.

Ms Morayef ta ce "Sanin rashin ingancinsu, ƙungiyoyin Falasdinawan suna kai hare-haren rokoki barkatai; dole ne a binciki wadannan hare-haren a matsayin laifukan yaƙi domin a gaggauta ba da agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa."

Kakakin PIJ Tariq Salmi bai ce komai ba game da wannan zargi.

Sai dai ya shaida wa BBC cewa rahoton na Amnesty "ya tabbatar da cewa mamayar [Isra'ila] ce ta fara kai hare-hare ta hanyar aikata manyan laifuka".

Ya kara da cewa, "makiya suna amfani da makaman da suke da su wajen kashe fararen hula Falasdinawa, kuma muna yin namu bangaren don kare kanmu daga laifukan da Isra'ila ta aikata kan al'ummar Palasdinu.