Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jihar Katsina: Ƴan bindiga sun sace mutum shida a Bakori, biyu a Ɗanja
Al’ummar wasu kauyuka a Jihar Katsina ta Najeriya sun ce suna cikin fargaba da rashin tabbas saboda ƙaruwar hare-haren ‘yan fashin daji a cikin ƙarshen mako abin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.
Hari na baya-bayan nan har cikin garin Bakori inda ‘yan fashin dajin suka sace mutum shida cikinsu har da ƙananan yara.
Bayanai daga wasu ƙauyukan Jihar ta Katsina cikin kananan hukumomin Bakori da Danja na cewa, ‘yan bindigar sun shiga cikin garin Bakori, inda suka sace iyalan wani mutum su shida mata da maza.
Sa'annan suka nausa zuwa kauyen Barebari inda can ma suka ci karensu ba babbaka tare da kashe wani mutum daya.
Wani da ya ga lamarin ya ce a kan idonsa ‘yan bindigar suka kashe mutumin.
A cewarsa, 'yan bindigar sun harbi mutumin a ƙirji a lokacin da ya je rufe ƙofar gidansa wanda harbin bindigar ya yi sanadin mutuwarsa.
Wanda ya ga harin ya ce yana bayan garken mutumin a lokacin da aka harbe shi, kuma ba damar ya fito ya kai ɗauki saboda tsoro.
Mutumin ya ce da zarar magariba ta yi su da matansu da ƴaƴansu suke barin garin sai da safe su koma saboda fargaba.
A garin Majema cikin karamar hukumar Danja ma, ‘yan bindigar sun kashe wani mutum.
Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa mutumin ya rasa ransa ne lokacin da ya yi yunkurin kai dauki.
Ya bayyana cewa akwai wasu matasa biyu da ƴan bindigan suka sace suka tafi da su.
BBC ta tuntuɓi kakakin rundunar yan sanda reshen Jihar Katsina SP Gambo Isah kan wannan lamari, sai dai ya ce zai yi bincike kan waɗannan lamura.
A Jihar Zamfara mai makwaftaka da Jihar Katsinar, jami’an tsaron hadin gwiwa ne suka fatattaki gungun ‘yan fashin daji waɗanda suka tare hanyar Gusau zuwa Sokoto a ranar Asabar, a dai-dai Dogon Awo.
Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya ce sun bi ƴan bindigar har cikin daji inda suka yi musu lugudan wuta, amma ya ce ba shi da alkaluman waɗanda aka kashe cikin ƴan fashin kawo yanzu.
To sai dai duk da irin wannan kokari, a iya cewa lamarin ‘yan fashin daji da masu satar mutane don neman kudin fansa a arewa maso yammacin Najeriya na ɗaukar wani sabon salo saboda yadda a baya-bayan na ake samun rahotannin da ke cewa ‘yan bindigar na cin zarafin mata.