Saudiyya ta kama wanda ya taimaka wa Bayahude shiga Makka da hawa Dutsen Arfa

Asalin hoton, Channel 13
Hukumomi a Saudiyya sun ce sun kama wani ɗan ƙasar da ake zargi da taimaka wa wani Bayahude ɗan jarida shiga birnin Makka mai tsarki, har ma ya hau kan Dutsen Arafah.
Bisa doka, haramun ne wanda ba Musulmi ba ya shiga birnin na Makkah da ke Saudiyya, wanda Musulmai ke girmamawa.
Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya, SPA, ya ruwaito rundunar 'yan sandan ƙasar na bayyanawa a ranar Juma'a cewa, ta kama wani ɗan ƙasar da ya taimaka tare da ɗaukar nauyin wani ɗan jaridar da ba Musulmi ba shiga Makkah.
Rahoton ya ƙara da cewa za a ɗauki matakin shari'a kan mutumin ɗan Saudiyya.
Sai dai rahoton bai bayyana ƙarara ba ko ɗan jaridar ɗan Isra'ila ne, ko kuma ko an yaɗa balaguron nasa zuwa Makkah a kafofin yaɗa labarai na Isra'ila.
Gwamnatin Isra'ila ta yi tir da matakin na ɗan jaridar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Abin da ya fusata Saudiyya

Asalin hoton, Channel 13
Cikin rahoton nasa da aka yaɗa ranar 18 ga watan Yuli a tasharsu ta Channel 13, Gil Tamary - wanda shi ne editan tashar na ƙasashen waje - ya naɗi shigarsa Makkah.
Kafar talabijin ta Channel 13 - mai yaɗa shirye-shirye a harshen Hiburu - ta wallafa rahoton wakilin nata yana karakaina a kan Dutsen Arafah da ke birnin Makkah a lokaci mafi daraja ga al'ummar Musulmi wato Hajji.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
'Yan gwagwarmaya na Saudiyya sun yi ta yaɗa bidiyon ɗan jaridar lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Makkah, wanda shi ne abu irinsa na farko ga wani ɗan jaridar Isra'ila ya shiga ƙasa mai tsarki, bayan rahotannin wata tawagar Isra'ila da ta taɓa kai ziyara Masallacin Annabi Muhammadu S.A.W.
Bidiyon ya nuna ɗan jarida Gil Tamari a cikin mota tare da wani mutum da ke magana da harshen Ingilishi, wanda aka ɓoye fuska da muryarsa, yayin da yake tuƙa Tamari zuwa Masallacin Ka'aba.
Tamari bai bayyana wa direban cewa shi ɗan Isra'ila ba ne kuma ya yi ta yi masa magana cikin Ingilishi lokacin da suka kai ƙofar shiga Masallacin Harami na Makkah.
Lamarin bai tsaya a zagayen birnin Makkah ba. Direban ya kai Tamari har wajen aikin Hajji, inda ya kai shi kan Dutsen Arafah don su ɗauki ƙarin hotuna.
An disashe fuskar direban, wanda Tamari ya ce ya yi hakan ne saboda ya kare shi daga abin da ka iya biyo baya.
Ziyarar tasa ta gamu da suka sosai a kafofin labarai na Isra'ila da kuma faɗin yankin Larabawa.
Tamari ya nemi afuwa daga baya, yana mai cewa rahoton nasa "wata babbar nasara ce da ya cimma a aikin jarida".
End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
'Na je Makkah ne don ruwaito muhimmancin Makkah ga 'yan uwana Musulmai'

Asalin hoton, Channel13
Ɗan jaridar bai bayyana ko ya karɓi izini ba a hukumance daga Saudiyya, amma ya siffanta abin da ya aikata da cewa "mafarkina ne da ya zama gaskiya", kuma wannan ne ya fusata ma'abota dandalin Tuwita a Saudiyya.
Sai dai Tamari ya nemi afuwa daga baya cikin saƙon Tuwita, yana mai cewa ziyarar tasa a Makkah "bai yi ta don ɓata wa Musulmai rai ba".
"Hasali ma, dalilin yin wannan ziyara shi ne na fito da muhimmancin Makkah ga 'yan uwanmu Musulmai maza da mata da kuma al'umma baki ɗaya," in ji shi.
Ɗan jaridar na ci gaba da shan suka
Cikin martanin da ya biyo bayan kamen ɗan Saudiyyar - wanda ake tunanin direban Tamary ne - 'yan jaridar Isra'ila sun ci gaba da sukar ɗan jaridar na Channel 13 a shafukansu na Tuwita.
"A bayyane take ƙarara an saka rayuwar direban cikin haɗari. A kan me? Haka kawai. Mutum ya ce ga ni a Makkah, wurin da ake yawan saka wa ido," a cewar Noa Landau, ɗan jaridar Haaretz ta Isra'ila, a shafinsa na Tuwita.
Shi ma ɗan jarida David Verthaim ya wallafa hoton sanarwar ta Saudiyya, yana cewa: "Irin wannan gangancin, haka kawai sun lalata rayuwar mutum."
"Wannan rahoton ya nuna ƙarara yadda 'yan Isra'ila suka jahilci al'adun Larabawa," in ji ɗan jaridar Falasɗinu Sheren Falah Saab.
Zuwa lokcain haɗa wannan rahoton, Tamary bai yi wani martani ba game da sanarwar a shafinsa na Tuwita.
Shi ma gidan talabijin ɗin na Channel 13 ya ƙi ya ce komai, kamar yadda rahoton Haaretz ya nuna.











