Ƴan ƙwallon Afirka shida da suka bai wa duniya mamaki

Asalin hoton, Getty Images
An ware ranar 25 ga watan Mayu ne domin bikin Ranar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya domin girmama wasan mai tarin masoya, wanda ake ganin tana haɗa kan duniya baki ɗaya.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce, "ƙwallon ƙafa wasa ce da ta samu karɓuwa sosai a duniya, da kuma take da matsayi na musamman. Bayan nishaɗantarwa da ƙwallo ke yi, tana isar da saƙo da kusan kowane ƙabila yake fahimta ba tare da bambancin shekaru ba ko bambancin arziki ko al'ada ba. Wannan ya sa ake kallon wasan a matsayin mai haɗa kan ƙasa da sanya alfahari da farin ciki a zukata."
Haka kuma ƙwallon ƙafa na taimakon yunƙurin samar da daidaiton jinsi da jawo hankali kan muhimmancin kula da lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa.
Domin bikin wannan ranar ne BBC ta tattaro wasu ƴanƙwallo biyar da suka ba da mamako a duniya.
Nwankwo Kanu - Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
A lokacin da yake shekara 20 a duniya ne lashe kyautar Gwarzon ɗanƙwallon Afirka a shekarar 1996 bayan taimakon Najeriya ta lashe gasar Olympic a Atlanta.
Da wannan ne ya zama ɗanƙwallon da ya lashe kyautar mafi ƙanƙantar shekaru a tarihi.
A shekarar 2000 ce ya ba duniya mamaki, inda duk da cutar zuciya da ya yi fama da ita, ya wattsake ya cigaba da buga ƙwallo, sai ya kafa gidauniyar Kanu Heart Foundation domin kula da masu fama da ciwon zuciya.
Ƙananan yara, musamman marasa galihu a Afirka suna fama da ciwon zuciya.
Barbra Banda - Zambia

Asalin hoton, Getty Images
Banda fitacciyar ƴarƙwallon ƙafa ce da ta kafa tarihin zura ƙwallo uku rigis a wasa sau biyu a Olympic ɗin 2021 da ta 2024.
Kyaftin ɗin tawagar ƙasar Zambia ɗin ce ta fi zura ƙwallaye a cikin ƴan Afirka a gasar Olpympic a tsakanin maza da mata baki ɗaya, inda ta zura ƙwallo 10.
Sannan ita ce mace ta biyu da ta fi tsada a tarihi a Afirka bayan Racheal Kundananji wadda ita ma ƴar Zambia ce.
Didier Drogba - Ivory Coast

Asalin hoton, Getty Images
Ya lashe gasar Premier huɗu da Gasar Zakarun Turai a ƙungiyar Chelsea, sannan ya bar ƙungiyar a matsayin na huɗu wajen zura ƙwallaye.
Bayan ƙasar Ivory Coast ta samu gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya a shekarar 2006, sai Drogba ya yi wani bidiyo inda a ciki ya roƙi ƴanbindiga da suke addabar ƙasar su ajiye makami, sannan a kawo ƙarshen yaƙin basasar ƙasar. Wannan ne ya yi sanadiyar ƙulla yarjejeniyar tsagaita a makon.
Asisat Oshoala - Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Oshoala ta fara ƙwallo ne ba da son iyayenta ba, amma ta zama ƴarƙwallon Afirka ta farko a tsakanin maza da mata da ta zura ƙwallo a Gasar Cin Kofin Duniya guda uku daban-daban, sannan ta farko da ta lashe Gasar Zakarun Turai.
Ta buɗe gidauniyar horas da ƴanƙwallo a Legas domin ba matasan ƴanƙwallo damar cika burinsu.
Victor Osimhen - Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Daga tasowa cikin rashi da gwagwarmaya a Legas ne Osimhen ya fara tashe a ƙungiyar Charleroi da ke Belgium.
Ya taimaka wa ƙungiyar Napoli wajen gasar Seria A ɗinta bayan shekara 33 tana nema. Yana yawan ambaton wahalar da ya sha a lokacin da yake tasowa a cikin abubuwan da suka sa yake dagewa.
George Weah - Liberia

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu George Weah ne kaɗai ɗan Afirka da ya taɓa lashe kyautar Ballon d'Or, wanda ya lashe a shekarar 1995.
A shekarar 2018 ta sake kafa wani tarihin, inda ya zama shugaban ƙasar Liberia, inda ya zama tsohon ɗanƙwallon ƙafa na farko da ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a tsarin dimokuraɗiyya.










