Waiwaye : Fara murƙushe Lakurawa da jana'izar Janar Lagbaja

Lokacin karatu: Minti 5

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Ƙungiyar IPMAN ta cimma matsaya da Dangote kan sayen fetur

A ranar Litinin ne da ta gabata ne ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya mai zaman kanta IPMAN ta ce mambobinta sun kammala cimma matsaya domin fara siyan tataccen man fetur daga matatar man Dangote kai tsaye.

Sun bayyana haka bayan uwar ƙungiyar ta gudanar da taro da mambobinta domin bin bahasin yarjejeniyar da suka cimma da matatar da kuma hanyoyin samun man cikin sauki.

Alhaji Zarma Mustapha, wani jigo a ƙungiyar ta IPMAN ya shaida wa BBC shirin da suka yi bayan tattaunawar da suka yi da shugabannin matatar a ranar litinin, inda ya ce wannan mataki da suka ɗauka zai haifar da wadatar man fetur a duk faɗin ƙasar.

Mutum 10 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

A ranar Talata ta makon da ya gabata ne rundunar ƴansandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum 10 a wani hatsarin mota a ƙauyen 'Yanfari da ke karamar hukumar Taura na jihar.

Lamarin wanda ya afku a kan hanyar Kano zuwa Hadejia, ya kuma janyo jikkatar wani fasinja ɗaya.

A wata sanarwa da kakakin ƴansandan jihar DSP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, ya ce lamarin ya afku ne lokacin da wata motar ƙirar bas da ta fito daga jihar Kano zuwa Hadejia ɗauke fa fasinjoji 11, ta gwara wa wata tirela har ta kai suka jujjuya.

Tawagar sintiri ta ƴansanda reshen Taura sun garzaya wajen, inda suka ɗauki gawawwakin waɗanda suka mutu zuwa babban asibitin Hadejia.

An sake kama fursunoni 51 da suka tsere daga gidan yarin Maiduguri

Sojojin Najeriya sun soma fatattakar Lakurawa daga sassan jihar Kebbi

Haka kuma a ranar Talatar da ta wuce ne hukumar gidan gyaran hali ta Najeriya ta ce ta sake kama wasu fursononi cikin waɗanda suka tsere daga gidan yari a Maiduguri na jihar Borno lokacin ambaliyar ruwan da aka yi a watan Satumba da ya gabata.

Kakakin hukumar, Abubakar Umar ya shaida wa BBC cewa an samu nasarar sake kama 51 daga cikin mutanen 271 da suka tsere.

Ya kuma ce suna aiki haɗin gwiwa tsakaninsu da jami'an tsaro da dama, inda ya ce suna bai wa juna bayanan sirri da zai taimaka musu wajen gano sauran fursunonin

A ranar Alhamis ne rundunar sojin Najeriya ta ƙaddamar da hare-hare kan ƙungiyar 'yanbindiga ta Lakurawa da ta ɓulla a wasu sassan jihohin Kebbi da Sokoto na arewa maso yammacin ƙasar.

Rahotanni daga yankin ƙaramar hukumar Augie na jihar Kebbi, sun ce sojojin ƙasar sun shiga wuraren da 'yan ƙungiyar suka kakkafa sansanoni tare da lalata su.

Sojojin sun kuma kori Lakurawan a dazukan ƙaramar hukumar, tare da kuɓutar da wasu daga cikin dabbobin da masu gwagwarmaya da makaman suka sace.

Matakin na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya da 'yan ƙungiyar suka yi artabu da mutanen gari Mera na yankin ƙaramar hukumar, tare da kashe mutum 15 da sace shanu masu yawa.

An kashe mutum fiye da 1500 da sace fiye da 2000 a Najeriya - NHRC

A ranar Alhamis ta makon da ke ƙarewa ne hukumar kare haƙƙin bil-adama ta Najeriya, wato NHRC, ta bayyana cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na wannan shekara, an sami aukuwar sace-sacen jama'a kusan 2000, aka kuma hallaka wasu kusan 1500 a sassan ƙasar.

Jami'an hukumar ne suka bayar da wannan rahoto, a wajen wani taron tuntuɓa na ƙungiyoyin farar hula, kan halin da ake ciki game da batutuwan da suka shafi al'amuran kare hakkin bil'adama a ƙasar.

Hukumar ta shirya taron ne tare da hadin gwiwar ƙungiyar Tarayyar Turai, kuma aka gudanar a babban birnin tarayya, Abuja.

Rahoton ya ce an kuma sace mutum 1712 sannan an kashe mutum 1463 a wurare daban-daban na Najeriya, a tsawo lokacin.

'Yan bindiga suka sace ɗalibai a Katsina

Haka kuma a ranar Alhamis din da ta gabata ne aka samu rahoton cewa wasu ƴan bindiga a kan babur sun sace wasu yara maza ɗalibai guda biyu da ke kan hanyarsu ta zuwa ƙaramar makarantar sakandire da ke garin Babban Duhu a ƙaramar hukumar Safana da ke jihar Katsina.

Wani malamin makarantar wanda bai amince a bayyana sunansa ba ya shaida wa BBC cewa al’amarin ya faru ne da safiyar, Alhamis ɗin, inda ƴanbindigar suka yi awon gaba da yaran guda huɗu kafin daga bisani yara biyu su tsere.

Babu wani bayani da ya nuna cewa jami'an tsaro sun bi ƴanbindigar domin ceto yaran.

Jana'izar Janar Lagbaja : Shugaba Tinubu ya karrama marigayin da lambar CFR

A shekaran jiya Juma'a ne Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya karrama marigayi tsohon babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftana Janar Taoreed Lagbaja da lambar CFR, a lokacin jana'izar marigayin.

Bola Tinubu wanda ya halarci taron jana'izar a Abuja ya bayyana Taoreed da mutumin da ya zama manuniyar irin nagartar jagoranci a aikin sojin Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da mutuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ranar 5 ga watan Nuwamba yana da shekara 56 a duniya, bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

Tun da farko an yi ta raɗe-raɗin cewa babban hafsan ya rasu ne a sanadiyar cutar kansa a wani asibiti a ƙasar waje, inda masu yaɗa maganganun suka riƙa cewa an ɓoye rasuwar ne saboda masu rububin neman maye gurbinsa.