Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wasu ke fafutukar kai agaji Gaza duk da barazanar Isra'ila
- Marubuci, Ethar Shalaby
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- Lokacin karatu: Minti 5
"An kawo mana hari da sinadarai masu guba - cikin sa'a bai faɗo cikin jirginmu ba saboda na fara zille masa bayan mun ji ƙarar jirgi maras matuƙi," a cewar Youssef Samour, wani ɗan gwagwarmaya da ke cikin jirgin da ke shirin kai kayan agaji Gaza.
"Ya faɗo ne a farfajiyar jirgin kuma ya feso min abubuwa a fuska, abin da ya sa min ƙaiƙayi tsawon daƙiƙa 30, amma da na wanke da ruwa komai ya wuce."
Jirgin da yake ciki mai suna Yulara ɗaya ne daga cikin rukunin Global Sumud Flotilla (GSF) - tawagar jiragen ruwa kusan 50 da ke ɗauke da kayan agaji da 'yan gwagwarmaya fiye da 300 da ke fatan shiga Zirin Gaza.
GSF ya ce jirage da yawa sun ce an kai musu hare-hare da abubuwa yayin da suke tafe a tsakiyar teku kusa da tsirin ƙasar Girka mai suna Crete.
Akan ji ƙarar jirgi maras matuƙi a kodayaushe tare da katse layukan sadarwa, in ji GSF suna masu zargin Isra'ila da kai hare-haren.
Rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba game da zargin hari kan jiragen ruwan GSF, amma jami'in ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Eden Bar Tal ya ce "Isra'ila ba za ta ƙyale wani jirgin ruwa ya shiga filin yaƙi ba".
"Babbar manufar rukunin jiragen ita ce tsokana da kuma taimaka wa Hamas, ba wai kai kayan agaji ba," in ji Bar Tal.
Ƙasashen Italiya da Sifaniya sun tura jiragen ruwa na yaƙi domin taimaka wa 'yan gwagwarmayar da ke kan hanyar zuwa Gaza.
Mene ne rukunin jiragen ruwa na Global Sumud Flotilla?
Kalmar Sumud ta Larabci ce da ke nufin juriya da haƙuri.
Global Sumud Flotilla (GSF) wani rukunin jiragen ruwa ne da aka cika da kayayyakin abinci da na sauran buƙatu kuma suke ɗauke da fasinjoji 'yan gwagwarmaya daga ƙasashe daban-daban.
GSF ya ce burinsu shi ne "karya shingen da Isra'ila ta ƙaƙaba wa Gaza ta ruwa domin kai kayan agaji, da kuma kawo ƙarshen kisan ƙare-dangi Isra'ila ke yi a Gazan".
Jiragen sun taso ne daga gaɓar ruwan Sifaniya, da Girka. da Tunisia bayan wani rahoton kwamatin Majalisar Ɗinkin Duniya ya tabbatar cewa Isra'ila ta jefa Birnin Gaza cikin bala'in yunwa.
Jiragen GSF ne na 38 da suka kama hanyar shiga Gaza domin tsallake shingen na Isra'ila ta ruwa, wanda ta saka tun shekaru masu yawa. GSF ne rukuni mafi girma tun bayan fara yunƙurin a 2008.
Rukunin na haɗin gwiwa ne tsakanin ƙungiyoyin Freedom Flotilla Coalition, da Gaza Free Movement, da Maghreb Sumud Flotilla, da kuma Sumud Nusantara, wanda ƙasashe Malaysia da saura wasu guda tara suka tsara.
Ko GSF za su iya kaiwa Gaza?
A 2008, aƙalla jirgi ɗaya ya iya kaiwa Gaza. Amma tun daga nan babu wani jirgi da ya sake kaiwa.
A 2010, dakarun sojin Isra'ila sun dira a kan wani jirgin Turkiyya mai suna Mavi Marmara, ɗaya daga cikin rukunin jirage shida da suka kai nisan kilomita 130 daga gaɓar ruwan Isra'ila.
Sojojin sun buɗe wa fasinjojin wuta suna masu cewa su aka kai wa hari da wuƙaƙe da bindiga, inda suka kashe mutum 10 'yan ƙasar Turkiyya.
A watan Mayun da ya wuce Isra'ila ta tare wani jirgin agajin, sannan ta sake tare wani a Yuni.
An yi zargin cewa wani jirgi maras matuƙi ne ya kai wa jirgi farko hari a kusa da tekun Malta.
Na watan Yunin kuma ya tashi ne da mutum 12, cikinsu har da 'yar gwagwarmayar nan Greta Thunberg. An tare jirgin ne daga nisan kilomita 185 daga zuwa Gaza.
A watan Yuli ma wani jirgin mai suna Handala ya nufi Gaza ɗauke da mutum 21, amma dakarun Isra'ila ska tare shi daga nisan kilomita 75 zuwa Gaza.
Harin da aka kai kan GSF ranar Laraba ba shi ne na farko ba, suna masu cewa an kai musu hari a Tunisia ma.
Abdel Rahman Ghazal - ɗan ƙasar Kuwait da ke cikin jirgin Spectre - ya faɗa wa BBC cewa tazararsa da wani bam da aka jefo kan jirginsu ba ta wuce rabin mita ba a ranar Laraba.
"Bamabamai uku aka jefo mana. Na ukun ya faɗo kan gaban jirgin kuma ya gangara cikin ruwa. Ina lokon da ya faɗo. Abu ne mai ɗauke da wani gas mai wari, mai sarƙe nimshafi. Da kyar na dinga nimfashi tsawon lokaci."
Yanzu Ghazal da abokan tafiyarsa na bin dokokin kare kai masu tsauri. Su daina barci a buɗaɗɗen wuri, kuma suna riƙe da rigar tsira a kodayaushe.
Su wane ne fasinjojin?
Daga 'yansiyasa zuwa fitattu, jiragen GSF cike suke da mutane daga ƙasashe da yawa.
Jikan Nelson Mandela mai suna Mandla Mandela, da tauraruwar finafinan Amurka Susan Sarandon, da tauraruwar fim a Faransa Adele Haenel, da 'yansiyasa kamar La France Insoumise da 'yarmajalisar Tarayyar Turai Emma Fourreau, da tsohon magajin garin Barcelona Ada Colau, duka na cikin fasinjojin.
GSF ya ce kowane jirgi na wakiltar "wani rukunin al'umma da ke yaƙar rufe wa mutane baki yayin da ake aikata kisan ƙare-dangi".
Greta Thunberg ma cikin rukunin a wannan karon. Thunberg ta ce harin da aka kai musu "dabarar tsoratarwa".