Trump ba zai taɓa samun nasara a kan Canada ba - Carney

Mark Carney

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Mutumin da ya lashe zaɓen firaiministan ƙasar Canada, Mark Carney ya bayyana cewa Canada ba za ta lamunci matsin lamba daga Shugaban Amurka, Donald Trump ba.

A cikin jawabinsa ga taron masoya a Nepean, Ontario bayan lashe zaɓen, Carney ya faɗa musu cewa, "Shugaba Trump na kokarin ganin bayanmu domin Amurka ta mallake mu. Wannan ba zai taba faruwa ba."

Carney ya gargadi magoya bayansa cewa Amurka na son mallakar filayen ƙasarsu, da albarkatunta, da kuma ƙasar baki daya,"

Jawabinsa ya nuna tsamin dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu da kuma kudirinsa na tsayawa tsayin daka.

Duk da cewa bai taba riƙe wani mukami ta hanyar zaɓe ba a baya, Mark Carney ya jagoranci Jam'iyyar Liberal zuwa babbar nasara, inda ya lashe kashi 64% na kuri'un da aka kada.

Ɗan takarar jam'iyyar Conservative, Barbara Bal, ita ce ke biye masa baya da kashi 33%, yayin da Shyam Shukla na NDP ya samu kashi 2%.