Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An rantsar da mace ta farko shugabar ƙasar Namibia
An rantsar da sabuwar shugabar ƙasar Namibia a ranar Juma'a domin jagorantar ƙasar wadda ke fuskantar ƙalubale na rashin aikin yi da kuma talauci.
Hadi kuma da wani ƙalubalen na kasancewa mace ta biyu da aka taɓa zaɓa a matsayin shugabar ƙasa a nahiyar Afirka, kuma ta farko a Namibia.
"Idan komai ya tafi daidai, wannan zai zami kyakkyawan misali," kamar yadda Netumbo Nandi Ndaitwah ta shaida wa shirin Podcast na BBC Africa. "Amma idan wani abu ya faru, kamar yadda zai iya faruwa ga kowace gwamnati ko da a ƙarƙashin namiji ne, akwai waɗanda za su ce: 'saboda mace ce!'"
Matar, mai shekara 72 a duniya ta lashe zaɓe ne a watan Nuwamba inda ta lashe kashi 58% na ƙuri'un da aka kaɗa.
Nandi-Ndaitwah ta kasance daɗaɗɗiyar ƴar jam'iyyar South West Africa People's Organisation (Swapo) – wadda take kan mulki tun lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai a shekarar 1990, bayan kwashe tsawon lokaci tana fafutukar ƙwatar kanta daga Afirka ta Kudu mai fama da mulkin wariya.
Ta shiga jam'iyyar, wadda a wancan lokacin ƙungiyar neman ƴanci ne daga hannun gwamnatin mulkin wariya ta tsiraru fararen fata, lokacin tana da shekara 14 a duniya.
Duk da cewa jam'iyyar ta kawo sauye-sauye da bunƙasa rayuwar baƙaƙen fata masu rinjaye, har yanzu ana iya ganin tasirin mulkin wariya ta hanyar la'akari da waɗanda suka fi dukiya da kuma mallakar filaye.
"Tabbas, batun mallakar filaye babbar matsala ce a ƙasar nan," kamar yadda ta shaida wa BBC, gabanin rantsar da ita.
"Har yanzu akwai fararen fata ƴan asalin ƙasar nan da kuma mutanen da suka mallaki filaye waɗanda ba za a iya ganin su a ƙasa ba."
Ta bayyana cewa ta yarda da tsarin "mai son ya sayar, ya sayar wa mai son saye" tsarin da ke nufin babu wanda za a tursasa wa sayar da filinsa.
Namibia ƙasa ce mai faɗin ƙasa sai dai al'ummarta ba su da yawa, miliyan uku kacal.
Alƙaluman gwamnati sun nuna cewa fararen fata manoma su ne suka mallaki kashi 70% na filayen noman ƙasar. Jimillar mutum 53,773 ne a Namibia suka bayyana kansu a matsayin fararen fata a ƙidayar al'umma ta shekarar 2023, wanda hakan ke nufin kashi 1.8% na yawan al'ummar ƙasar.
Namibia na daga cikin ƙasashen da ke fama da wagegen giɓi tsakanin masu kuɗi da talakawa, in ji Majalisar Dinkin Duniya.
Rashin aikin yi a ƙasar ya tashi zuwa kashi 36.9% a 2023 daga kashi 33.4% a 2018, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta tabbatar.