Ko 'yan Namibia za su zaɓi mace ta farko a matsayin shugabar ƙasarsu?

    • Marubuci, Frauke Jensen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Windhoek
  • Lokacin karatu: Minti 6

Idan al'amura suka daidaita kamar yadda jam'iyyar da ta daɗe tana mulkin Namibiya ke fata, ƙasar za ta zaɓi shugabar ƙasa mace ta farko a ranar Laraba.

Sai dai wani yanayi na rashin jin daɗi da ƙungiyoyin neman ƴancin kai a kudancin Afirka ke da shi, tare da rashin tagomashi da jam'iyyu masu mulki da dama ke samu a sassa daban-daban na duniya, na iya yin barazana ga abin da zai zama nasara mai cike da tarihi.

Mataimakiyar shugaban ƙasa Netumbo Nandi-Ndaitwah mai shekaru 72, ita ce ke riƙe da tutar takarar jam'iyyar Swapo, wadda ta jagoranci ƙasar tun bayan samun ƴancin kai daga gwamnatin mulkin wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu a shekarar 1990.

Samia Suluhu Hassan ta Tanzaniya, ita ce shugabar ƙasa mace ɗaya tilo a Afirka, don haka Nandi-Ndaitwah za ta shiga wani jerin mutane na musamman idan ta yi nasara.

Jam'iyyarta, wadda ta yi kane-kane kan shigabancin ƙasar na tsawon shekaru 30 ta samu raguwar goyon baya a babban zaɓen da ya gabata. Za ta fafata a zaɓen na ranar Laraba tana fuskantar matsalar rashin aikin yi da ya kai kashi 19 cikin 100 - kusan daidai da yadda yake shekaru 30 da suka gabata, ga matsalolin kuɗaɗen gwamnati da badaƙalar da ta shafi cin hanci da rashawa.

Nandi-Ndaitwah za ta fafata ne da babban abokin hamayyarta a cikin sauran ƴan takara 14 - Panduleni Itula na jam'iyyar Patriots for Change (IPC).

Wani cikas da za ta iya samu kuma shi ne takararta ta ci karo da al'adun siyasa na gargajiya inda maza ne ke sheƙe ayar su.

Amma ta kasance shugabar da aka amince da ita a wannan kasa da ba ta da yawan al'umma kuma ake zaman lafiya. Ta yi aiki a babban ofishin gwamnati na tsawon shekara 25.

"Na yarda da butun aiikin haɗin gwiwa, abin da ya sa na cimma nasaraorin da na samu ke nan ya zauwa yanzu ," in ji ta.

Mataimakiyar shugaban wadda aka san ta da salon tafiyar da al’amuranta na gaskiya da rikon amana, ta kuma kasance mai tsananin biyayya ga jam’iyyar da ta shiga tun tana matashiya.

Tana da shekaru 14 ta shiga wani ɓangare na ƙungiyoyin da ke adawa da mulkin gwamnatin Afirka ta Kudu, wadda ke mulkin ƙasar - a lokacin da ake kiran ta South West Africa - tun ƙarshen yakin duniya na ɗaya kuma daga baya ta shigo da tsarin mulkin mai cike da wariyar launin fata.

Ta yi fice ne saboda jajircewarta da hazakar iya tafiyar da jama'a a matsayin ta ta shugabar ƙungiyar matasa ta Swapo, wadda ta zama matakalar siyasarta, wanda ya haɗa da matsayin ministar harkokin ƙasashen waje da na yawon bude ido da na jin daɗin yara da kuma yaɗa labarai.

Ta samu ilimi mai tarin yawa da gogewar da za ta taimaka mata matuƙa idan ta samu hayewa kan karagar mulki.

"Da alama tana da hikima da kirki da kuma tausayi, ko da yadda take ƙoƙarin yin bayanin abubuwa ta hanyar da har mutane iri na ma za su iya fahimta," wata mai kaɗa ƙrui'a mai suna Laimi, ta shaida wa BBC a babban birnin ƙasar, Windhoek.

"Itula yana da yanayi da sabon kayan ado, sanye da tabarau ne da tabarau, da kayanasa masu kyau da k,uma yadda ya ke tafiya cike da ƙwarin gwiwa amma watakila ya makantar da kai da haskensa," in ji kawarta Maria.

Dukansu matasa ne waɗanda suka kasa samun ayyukan yi.

Ƙwararren likitan hakori, Itula, mai shekaru 67, ya taba zama jigo a jam'iyyar Swapo amma an kore shi daga jam'iyyar a shekarar 2020 bayan ya tsaya takara a matsayin ɗan takara mai zaman kansa inda ya fafata da shugaba Hage Geingob a zaɓen 2019.

Ya kuma kasance shugaban matasa kuma ya shafe wani lokaci a gidan yari kafin ya tafi gudun hijira a Burtaniya a farkon shekarun 1980. Ya koma Namibiya a shekarar 2013.

Shekaru shida bayan haka, cikin kwarjini ya zo ya shiga sahun gaba na siyasar Namibiya, inda ya ƙalubalanci Geingob a zaɓen shugaban ƙasa bayan ya ce tsarin Swapo na zaɓen ɗan takarara na cike da kura-kurai.

Shigar Itula a wancan zaɓen ya sa Swapo ta samu mafi karancin kaso - na 56% - a zaɓen shugaban ƙasa sannan kuma ta rasa kashi biyu bisa uku na rinjaye a majalisar dokoki.

A matsayinsa na wanda ya taɓa rayuwa a wajen fagen siyasa, yana samun tagomashi a tsakanin kashi 50 cikin 100 na masu kaɗa ƙuri'a miliyan 1.5 waɗanda ba su kai shekaru 35 ba, wadanda da yawa daga cikinsu suna buƙatar sauyin tattalin arziki, da aikin yi ko kuma wani abu dai da zai bunƙasa kuɗaɗen da suke samu.

Jajircewarsa da a wasu lokuta salon jarumtakarsa, da kin amincewa da maganganun siyasa na Nandi-Ndaitwah, ya sa ya sami goyon baya a tsakanin ƴan kasuwa da kuma manyan ƴan boko da ke zaune a birane.

Amma yayin da Itula ke da ƙwarewar iya magana, mataimakiyar shugaban ƙasar tana zaɓar kalamominta cikin hikima, kuma ana magana a hankali.

Nandi-Ndaitwah tana neman tabbatar da jituwa da kuma aiki tare, tana dagewa kan abubuwan da suka shafi al'umma don haka, tana samun karɓuwa a zukatan masu ƙaramin ƙarfi.

Kuma a matsayinta na mace ta farko da ke da damar zama shugabar ƙasar, tana ɗauke da fatan wasu matan da ke son sauyi daga yadda ake gudanar da al'umma, inda maza en ke sheƙe ayarsu.

Duk da haka, Nandi-Ndaitwah tana wakiltar ƴan gwagwarmayar samun ƴanci na Namibia "da aka gwada aka kuma amince da su", yayin da Itula ke wakiltar yiwuwar samun "guguwar sauyi" a cikin yanayin siyasa da ke buƙatar gyaran fuska.

A cewar mai sharhi kan al'amuran siyasa Henning Melber, hamayyar da ke tsakanin manyan ƴan takarar biyu na iya nufin cewa zaɓen shugaban ƙasar zai iya kai wa ga shiga zagaye na biyu, lamarin da ba a taɓa ganin irinsa ba, wanda za a bukaci yin haka ne idan babu wanda ya samu fiye da rabin ƙuri'un da aka kaɗa.

A makwabciyarta Afirka ta Kudu, an tilastawa jam'iyyar African National Congress, da ke mulki tun 1994, shiga kawancen jam'iyyu bayan babban zaɓen watan Mayu. Yayin da a Botswana - da ke gabas - Jam'iyyar Demokradiyar Botswana, wadda ta shafe kusan shekara sittin ta na mulki, ta sha mummunar kaye a ƙarshen watan jiya.

Swapo na so ta guje wa fuskantar irin wannan lamarin.

Ɗan takarar da za a fi amincewa da shi a kan batutuwan da suka shafi rashin aikin yi na matasa da cin hanci da rashawa da kiwon lafiya da ilimi da inganta ababen more rayuwa, tare da samun damar bunƙasa tattalin arziki, tabbas shi ne wanda zai lashe zaɓen na ranar Laraba.

Za a buƙaci hakan ya faru ba tare da sayar da ɗimbin albarkatun ƙasar ga ƴan kasuwa na ƙasashen waje ba – kamar iskar gas da ke bakin teku da kuma lithium da sauran muhimman karafa.

Jam'iyyar IPC ta Itula ba ta cikin zaɓukan 2019, amma ta taka rawar gani sosai a zaɓukan ƙananan hukumomi tun daga lokacin kuma an fara yi ma ta ganin wani zaɓi na daban a fagen siyasar ƙasar. Ta samu yabo kan yadda ta tafiyar da wasu ƙananan hukumomi.

Babban abin da zai iya taimakawa Nandi-Ndaitwah na iya kasancewa, kamar yadda jami'in diflomasiyyar Namibia Tuliameni Kalomoh ya taɓa cewa, ana ganinta a matsayin "Mai gaskiya, ta fannin ɗabi'a da kuma ma'amalla".