Shin gwamnatin Najeriya za ta dakatar da sabon haraji bayan zargin cushe?

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
A yanzu da ya rage saura mako ɗaya kafin sabuwar dokar haraji ta fara aiki a hukumace a Najeriya, kallo ya fara komawa sama ne kan ko aiwatarwar za ta yiwu ko kuma za a dakatar.
Wannan na zuwa ne bayan muhawarar da ta kaure a ƙasar bayan an yi zargin samun sauye-sauye a dokar daga ƙudurin dokar da aka gabatar a majalisar ƙasar, aka tattauna tare da tafka muhawara kafin amincewa.
Zargin dai ya haifar da muhawara mai zafi a tsakanin ƴan Najeriya tun bayan da ɗan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Sokoto Abdulsammad Dasuki ya ja hankalin majalisar kan abin da ya bayyana da bambance-bambance da ya ce ya gano a tsakanin ƙudurin dokar haraji da majalisar ta amince da shi, da kuma wanda aka sanya wa hannu ya zama dokar da za a yi amfani da shi.
A watan Yunin 2025 ɗin ne dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin dokokin haraji huɗu a wani mataki na sauya fasalin tsarin karɓa da tattara haraji na ƙasar.
Gwamnatin ta ce sabbin dokokin za su sauƙaƙa tsarin, da rage wahalhalun haraji kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni, da kuma taimakawa wajen inganta karɓar haraji.
Tun bayan zargin da ɗan majalisar ya yi ne ake ta muhawara, inda manyan ƙungiyoyi da ɓangarorin siyasa da na al'umma na ƴan siyasa da ma ɗaiɗaikun mutane suka tofa albarkacin bakisu.
Bai kamata a dakatar ba - Kwamitin Tinubu
Sai dai zuwa yanzu gwamnatin Najeriya ba ta ce uffan ba kan zargin cushen, amma shugaban kwamitin tsara dokar da aiwatarwa, Taiwo Oyedele ya bayyana a ranar Litinin da ta gabata cewa bai kamata a dakatar da aiwatar da dokar ba a 1 ga Janairu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da tashar Channels, inda ya ce ɗage fara amfani da harajin zai shafi da dama daga cikin ƴan ƙasar.
Ya ce, "kusan kashi 98 na ƙananan ma'aikata da sabuwar ta ɗauke w haraji za su ci gaba a biyan haraji, haka ma ƙananan ƴan kasuwa za su ci gaba da biyan haraji daban-daban da bai kamata ba."
Shugaban kwamitin ya ce akwai harajin VAT da ke ɓoye a cikin kayayyakin buƙatu da yau a kullum da lafiya da ilimi da sabuwar dokar ta musu tanadi na musamman za su ci gaba a hauhawa.
Ya ce maimakon a riƙa kiraye-kirayen a soke sabuwar dokar baki ɗaya, "kamata ya yi a duba wuraren da ake magana. Don haka ya kamata mu fayyace abubuwan da muke buƙatar fahimta a game da dokar."
"Don haka idan ma akwai sauyi daga abin da majalisa ta amince, ina ganin zai fi kyau a gano su, sai a fara aiwatar da ɓangarorin da majalisar ta amice da su, sannan a gefe guda kuma a ci gaba da tattaunawa kan wuraren da ake da matsala a kansu."
Ya ce ko a kwamitinsa akwai abubuwan da su ke so su koma wajen shugaban ƙasa, "mu buƙaci a yi gyara."
Majalisa Ƙoli ta Musulunci
A nata ɓangaren, Majalisar Ƙoli ta Shari'ar Musulunci a Najeriya ta ce ta yi takaici dangane da zargin da ake ta yaɗawa cewa akwai banbanci tsakanin dokar haraji da ake son aiwatarwa a watan Janairun 2026 da wadda ƴan majalisar ƙasar suka amince.
A wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta ce idan dai har hakan ya tabbata to babu abin da zai haifar illa janyo yanke ƙauna da raini daga al'ummar ƙasa.
Majalisar ta ƙara da cewa dalilin da ya sa al'amarin ya ba ta takaici shi ne sakamakon irin gudunmowar da ta bayar ga kundin na dokar harajin ƙasa.
Daga ƙarshe majalisar ta nemi ɓangarorin biyu na zartarwa da majalisar dokoki da su yi bincike domin gano yadda aka yi aka samu sauye-sauyen.
Cin amanar ƴan Najeriya - Atiku
Shi ma tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP, kuma a jigo a ADC, Atiku Abubakar ya bayyana ra'ayinsa kan batun, inda ya ce canjin da ake zargi an samu a ƙudurin haraji da takardun da aka sanya wa hannu cin amanar ƴan ƙasa ne, sannan karan-tsaye ne ga kundin tsarin mulkin ƙasar.
Atiku ya bayyana haka ne a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce sauye-sauyen da aka samu sun nuna cewa gwamnatin ta fi mayar da hankali ne kan tatsar ƴan ƙasar sama da jin daɗi da walwalarsu.
Jigon siyasar hamayyar ya yi kira da a dakatar da aiwatar da ƙudurin harajin, wanda ake sa ran farawa a watan Janairun domin gudanar da cikkaken bincike.
Ya kuma buƙaci majalisar dokokin ƙasar ta yi gaggawar gyara sauye-sauye da aka yi ba bisa ƙa'ida ba, sannan a hukunta masu hannu a yi wa kundin tsarin mulki zagon ƙasa, sannan hukumar EFCC ta gudanar da bincike a kansu.
Ƙungiyar tuntuɓa ta arewa (ACF)
A nata ɓangaren, ƙungiyar tuntuɓa ta arewa wato ACF, ta yi kira ga gwamnatin ne da ta dakatar da aiwatar da sabuwar dokar harajin, sannan ta bayyana dokar a matsayin wadda ta saɓa da ƙa'ida.
A wata sanarwa da jaridar Daily Trust ta kalato daga sakataren watsa labaran ƙungiyar, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ƙungiyar ta ce zargin cushen ne ya sa dokar ta zama wadda ba za a yi amfani da ita ba a ƙa'ida.
"Ba za ka gina doka ba a kan abin da yake na ƙarya ba. Takardun da aka yi cushe a ciki ba za su iya zama doka ba," in ji shi.
Ya yi kira ga majalisar dokokin Najeriya ta janye ƙudurin dokar, sannan ta sake nazarinsu kafin sake amincewa.
Ƙungiyar Yarbawa da Igbo
Ita ma ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere tsagin Cif Ayo Adebanjo ta yi kira da a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar harajin.
A wata sanarwa da jagoran ƙungiyar, Oladipo Olaitan da babban sakataren yaɗa labaran ƙungiyar, Justice Faloye suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta yi Allah-wadai da zargin cushen da ake yi.
Ta ce canjin da ake zargi kuskure ne babba, "da kuma yi wa kundin tsarin mulkin Najeriy karan-tsaye," in ji ta, sannan ta ƙara da cewa da a ce ƙasashen da aka ci gaba ne, ba ƙaramin laifi ba ne cushe irin wannan.
A nata ɓangaren, ƙungiyar dattawa ta Igbo, shugaban ƙungiyar Charles Nwekeaku ya buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar da sabuwar dokar ta haraji saboda wannan zargin na cushe.
Ya ce cushen da ake zargi an samu bai dace ba, "don haka ya kamata shugaban ƙasa ya sake nazarin dokokin tare da tantance na ainihi."
"Idan gwamnati ta aiwatar da sabuwar dokar, hakan zai nuna cewa ta fi mayar da hankali kan tatsar ƴan ƙasar, kuma hakan ba mulki mai kyau ba ne," in ji shi.
Ƙungiyar lauyoyi
Ita ma ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya NBA ta yi kira da a dakatar da aiwatar da dokar ba tare da ɓata lokaci ba har sai an yi nazari tare da tabbatar da babu zargin cushen.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, shugabanta Afam Osigwe (SAN) ya ce zargin cushen ya saka alamar tambaya kan gaskiya da amana da zargin ɓoye-ɓoye da ake yi wa hukumomi.
Osigwe ya ce zargin cushe-cushen da sauye-sauyen da ake zargi tsakanin dokar da aka gabatar a majalisa, da wadda aka saka wa hannu, ya nuna buƙatar sake nazari.
"Ya kamata a dakatar da aiwatar da dokar harajin har sai an duba tare da tabbatar babu abin da ake zargi a ciki."











