Mece ce gaskiya kan zargin sauya dokar haraji ta Najeriya?

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
Tuni dai ƴan najeriya suka fara musayar yawu bisa rahotanni da ke yawo dangane da zargin sauya ko kuma yin cushe a dokar haraji ta Najeriya da ake sa ran za ta fara aiki a ranar 1 Janairu 2026.
Ɗan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Sokoto Abdulsammad Dasuki ne dai ya ja hankalin majalisar kan abin da ya bayyana da bambance-bambance da ya ce ya gano a tsakanin ƙudurin dokar haraji da majalisar ta amince da shi, da kuma wanda aka sanya wa hannu ya zama dokar da za a yi amfani da ita.
A watan Yunin 2025 ɗin ne dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin dokokin haraji huɗu a wani mataki na sauya fasalin tsarin karɓa da tattara haraji na ƙasar.
Gwamnatin ta ce sabbin dokokin za su sauƙaƙa tsarin, da rage wahalhalun haraji kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni, da kuma taimakawa wajen inganta karɓar haraji.
To sai dai wannan zargin na cushe da ya kunno kai a yanzu haka ka iya jefa shakku a zukatan ƴan Najeriya musamman dangane da aniyar gwamnatin.
Me Dasuki ya ce?
Ɗanmajalisar daga jihar Sokoto, Abdulsammad Dasuki ya ce an take masa haƙƙinsa na ɗan majalisa, inda ya nanata cewa abin da aka rubuta a takardun dokar da aka fitar sun bambanta da abin da 'yan majalisar suka tattauna, sannan suka kaɗa ƙuri'ar amincewa.
Ya ce ya yi wannan ƙorafin a ƙarƙashin damar da yake da ita ta haƙƙin ƴan majalisa da kundin dokokin majalisar ya tanada.
Ya ƙara da cewa bayan amincewa da dokokin haraji ne ya ɗauki kwana uku yana nazarinsu, inda ya ce a hakan ne ya gano akwai bambanci da wanda majalisa ta amince da su.
"Ina nan lokacin da aka yi tattaunawar, kuma na kaɗa ƙuri'a a kan lamarin, amma yanzu ina ganin wani abu daban da abin da muka amince da shi."
Da gaske an samu cushe?
Ɗanmajalisar tarayya daga jihar Kano, Kabir Alhassan Rurum ya ce bincike ne kawai zai iya tabbatar da hakan inda ya ce tuni majalisar wakilan ta kafa kwamiti na musamman domin gano gaskiyar al'amarin.
"Ba za mu ce gaske ne ba kuma za mu ce ƙarya ne ba. Majalisa ta kafa ƙwaƙkwaran kwamitin da zai binciki zarge-zargen da ɗnmajalisar ya yi da ma waɗanda suke yawo a kafafen watsa labarai. Za a yi bincike na gaskiya kuma za a shaida wa ƴan ƙasa sakamakon bincike."
Danmajalisar na Kano ya kuma ƙara da cewa kwamitin na ƙunshe da mutane masu nagarta a majalisar da suka hada da Ahmed idris Wase da Sada Soli Jibiya da Alasan Ado Doguwa da dai sauran dattawan majalisa ƙarkashin jagoranci Hon Mukhtar Betara.
Me kafafen watsa labarai ke rawaitowa?
Jaridun Najeriya da suka yi iƙrarin samun karanta takardun dokokin harajin da kuma abubuwan da majalisar dokoki ta amince da su sun lissafa wasu sassan dokar da suka ce an yi wa cushe da suka haɗa da sassan da ke ƙasa:
- Sashen na 64 (1)
- Sashe na 3 (1) (b)
- Sashen na 29 (3) da (4)
- Sashe na 39 (3)
- Sashe na 41 (8) da (9)
- Sashe na 60 (1)
Su wa ake zargi da yin cushe?
Hon Alasan Rurum ya ce "bincike ne kawai zai iya tabbatar da hakan. Ba za mu yi riga malam masallaci ba."
To sai dai tuni hukumar tattara haraji ta Najeriya, FIRS musanta cewa ta yi sauyi ko kuma cushe a dokar harajin ta Najeriya.
"Mu ba yin dokoki. Mu muna aiwatar da dokoki ne waɗanda aka ba mu daidai da ayyukanmu a matsayinmu na hukumar tarayya," in ji Dare Adekanbi wanda mai magana da yawun shugaban hukumar ne ya shaida wa Daily Trust.
Martani daga ƴan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Tuni dai ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun ƴan Najeriya suka fara kiraye-kirayen a yi bincike inda wasu ma suke kiran da a dakatar da batun fara aiwatar da doka.
Majalisar Ƙoli ta Shari'ar Musulunci a Najeriya ta ce ta yi takaici dangane da zargin da ake ta yaɗawa cewa akwai banbanci tsakanin dokar haraji da ake son aiwatarwa a watan Janairun 2026 da wadda ƴan majalisar ƙasar suka amince.
A wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta ce idan dai har hakan ya tabbata to babu abin da zai haifar illa janyo yanke ƙauna da raini daga al'ummar ƙasa.
Majalisar ta ƙara da cewa dalilin da ya sa al'amarin ya ba ta takaici shi ne sakamakon irin gudunmowar da ta bayar ga kundin na dokar harajin ƙasa.
Daga ƙarshe majalisar ta nemi ɓangarorin biyu na zartarwa da majalisar dokoki da su yi bincike domin gano yadda aka yi aka samu sauye-sauyen.










