Mene ne harajin kashi 5 da gwamnati ke son ƙarawa kan man fetur

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A 'yan makonnin nan, gwamnati ta sake jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya bayan da aka sanar da batun ƙarin haraji na ƙashi 5 a kan man fetur.

Wannan ya sa mutane da dama suke tambayar: Shin sabon haraji ne? Yaushe za a fara aiwatar da shi? Kuma mene ne manufar gwamnati?

Ba sabon haraji ba ne

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa da ke tsare-tsare da yi wa tsarin haraji garambawul, Taiwo Oyedele, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X cewa ba sabon haraji bane gwamnatin Tinubu ta ƙirƙiro.

Ya ce wannan tanadi tuni yana cikin dokar hukumar da ke kula da gyaran tituna ta ƙasa wato FERMA tun daga shekarar 2007, kawai an sake haɗa shi ne cikin sabon dokar haraji ta Najeriya ta 2025.

A cewarsa, wannan ba yana nufin za a fara aiwatar da shi nan take ba, sai dai kawai gwamnati ta ƙara shi cikin sabuwar doka domin tsarin ya kasance a bayyane da kuma haɗe cikin tsari guda.

Yaushe za a fara aiwatar da harajin?

Da farko dai an sanar da cewa za a fara aiwatar da wannan ƙarin haraji a watan Janairun 2026, amma daga baya Oyedele ya ce ba a kammala tsayar da ranar da za a fara aiwatar da harajin ba tukunna.

Bisa ga sabuwar doka, ministan kuɗi ne kaɗai zai iya bayar da izinin fara aiwatar da harajin, kuma sai an wallafa a cikin shafin 'Official Gazette' kafin ya fara aiki.

Wannan tsari, a cewar Oyedele, na da muhimmanci domin ya bai wa gwamnati damar yin la'akari da yanayin tattalin arzikin ƙasa kafin ta ɗora sabon haraji kan al'umma.

Waɗanne kayayyakin makamashi ne harajin zai shafa?

Bisa ga bayanan gwamnati, man fetur da man gas na dizil ne kawai za a ɗora wa wannan ƙarin haraji.

Sauran muhimman kayayyaki da ake amfani da su a gidaje kamar su kalanzir da iskar gas da kuma iskar gas ta CNG ba su shiga cikin wannan ƙarin harajin ba.

Mene ne za a yi da kuɗin harajin da za a tara?

Gwamnati ta bayyana cewa duk kuɗin da aka tara daga wannan ƙarin haraji zai tafi ne cikin asusu na musamman da aka ware don gina hanyoyi da gyara su.

A cewar Oyedele, idan aka aiwatar da tsarin yadda ya dace zai:

  • Tabbatar da hanyoyi masu aminci
  • Rage ɓata lokaci da kuɗin tafiya
  • Rage kuɗin jigila da kula da motocin sufuri
  • Kuma zai kawo fa'ida ga tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya

Fiye da ƙasashe 150 a duniya suna aiwatar da irin wannan tsarin, inda ake ɗora haraji mai yawa a kan man fetur domin samun kuɗaden da za a yi amfani da su wajen ci gaba da zuba jari a hanyoyi.

Me ya sa ake buƙatar wannan ƙarin kuɗin?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duk da cewa kuɗin da gwamnati ta tara daga cire tallafin mai zai taimaka, Oyedele ya ce hakan ba zai wadatar ba wajen magance buƙatun hanyoyi da sauran manyan ayyukan gine-gine a Najeriya.

"Asusu na musamman zai bada tabbacin samun kuɗi na dindindin saboda gina sabbin hanyoyi da gyara waɗanda suka lalace kuima zai cike giɓi da kasafin gwamnati ke bari, kuma ya hana hanyoyi rasa kuɗin gyara," in ji shi.

A cewar gwamnati, waɗannan sauye-sauyen sun riga sun rage yawan haraji masu yawa da mutane ke fuskanta tare da cire ko dakatar da wasu kuɗaɗe da ke shafar gidaje da ƙananan 'yan kasuwa kai tsaye, kamar haraji kan mai da harajin sadarwa da harajin tsaron intanet.

Hakan, a cewar gwamnati, zai kawo sauƙaƙa da ingantaccen tsarin tattara haraji a ƙasar.

A watan Yunin 2025 ne gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan sabbin dokokin haraji da za a fara aiwatarwa daga watan Janairun 2026 wanda tun a watan Disambar 2024, shugaba Tinubu ya aika da su zuwa majalisar dokoki.

Sabbin dokokin sun haɗa da

  • Dokar haraji ta Najeriya (The Nigeria Tax Act), wadda ta tattara ƙananan tanade-tanaden haraji wuri guda, za ta kawo ƙarshen ƙananan tanadin haraji fiye da 50 a ƙasar. A cikin wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar ta ce rage yawan tanade-tanaden harajin masu cin karo da juna a wasu lokuta, zai ƙara sauƙaƙa harkokin kasuwanci a ƙasar
  • Dokar gudanar da haraji (The Tax Administration Act), wadda ta tsara dokokin bai ɗaya na yadda za a karɓi haraji a matakan gwamnatin tarayya da na jihohi da ƙananan hukumomi
  • Dokar kafa hukumar karɓar haraji (The Nigeria Revenue Service Act), wadda za ta maye gurbin hukumar karɓa da tattara haraji ta ƙasar (FIRS) kuma wadda aka bayayna da ''mai zaman kanta'', an sanya mata sunan ''Nigeria Revenue Service (NRS)
  • Dokar samar da hukumar haɗin gwiwa ta haraji (The Joint Revenue Board Act), wadda za ta inganta haɗin kai tsakanin matakan gwamnati da kula da harkokin haraji da samar da kotun kula da shari'o'in da suka shafi haraji

A cikin sabbin sauye-sauyen, an ƙuduri aniyar cewa ma'aikata masu samun ƙasa da Naira 800,000 a shekara ba za su biya haraji ba.