Abin da muka sani kan Musulmin da ya hana kisan Yahudawa a Australiya

Hoton wani mutum sanye da farin riga lokacin da yake kokarin kwace bindiga daga mahari
Bayanan hoto, Mista Ahmed ya yi ta maza wajen ƙwace bindiga daga hannun maharin
    • Marubuci, Emily Atkinson
  • Lokacin karatu: Minti 4

An bayyana sunan Ahmed al Ahmed, wani "gwarzo" wanda aka naɗi bidiyonsa - a matsayin wanda ya ƙwace bindiga daga hannun wani mahari a bakin ruwa na Bondi da ke Australia.

Bidiyon wanda BBC ta tantance ya nuna mista Ahmed ya ruga zuwa kan ɗan bindigar tare da ƙwace makaminsa, kafin ya juya bindigar kansa - abin da ya sa ya miƙa wuya.

Mista Ahmed, wanda yake da shagon sayar da ƴaƴan itace, yana asibiti cikin koshin lafiya, inda aka yi masa aiki daga raunukan harsashi da ya samu a hannunsa, kamar yadda iyalansa suka shaida wa sashen Larabci na BBC.

Mutum 15 ne suka rasu sannan gommai suka jikkata a harin da ɗan bindigar ya kai ranar Lahadi da daddare lokacin da mutum kusan 1,000 ke halartar wani biki a Australiya.

Ƴan sanda sun ayyana lamarin a matsayin harin ta'addanci da aka kai kan al'ummar Yahudawa.

Mahaifin Ahmed, Mohamed Fateh, da mahaifiyarsa, Malakeh Hasan.

Asalin hoton, ABC News

Bayanan hoto, Mahaifin mista Ahmed, Mohamed Fateh, da mahaifiyarsa, Malakeh Hasan, sun nuna matukar farin ciki kan abin da ɗansu ya yi, kamar yadda kawunsa ya faɗa wa BBC

A ranar Litinin, Mahaifin mista Ahmed, Mohamed Fateh, ya shaida wa sashen Larabci na BBC cewa, ɗansa ba ya gajiya wa idan ya ga an kai wa mutane hari.

"Ahmed ya yi matukar ƙoƙari da kuma jin tausayin ɗan'adam lokacin da ya ruga ya je ya dakatar da maharin tare da ƙwace makaminsa," in ji shi.

Ɗansa ya fita waje ne tare da wani abokinsa domin zuwa shan gahawa, lokacin da suka haɗu da lamarin.

"Ya ga waɗanda lamarin ya shafa, jini, mata da kuma yara kwance kan titi, daga nan zabura," in ji mahaifin nasa.

Kawun Mohamed Ahmed.
Bayanan hoto, A Siriya, inda aka haifi mista Ahmed, kawunsa Mohamed Ahmed ya faɗa wa BBC cewa: "Muna alfahari da shi, ƙauyen mu, Syria, dukkan Musulmi da kuma faɗin duniya na alfahari da shi."

A can Siriya, inda aka haifi Ahmed kuma ya girma, kawunsa Mohamed Ahmed, ya tattauna da BBC, inda ya ce iyalansa suna alfahari da shi.

""Muna alfahari da shi, ƙauyen mu, Syria, dukkan Musulmi da kuma faɗin duniya na alfahari da shi," in jhi shi.

Ɗan uwan mista Ahmed, Mustafa, ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta Australiya, wato 7News ranar Lahadi cewa: "Shi gwarzo ne. Cikakken gwarzo. Ya samu harbi har guda biyu a jikinsa."

A wani sabon bayani a safiyar yau Litinin, Mustafa ya ce: "Ina fatan zai samu sauki. Na gan shi jiya da daddare. Yana murmurewa amma muna jira mu ji me likitoci za su ce.

Ƴansanda sun ce waɗanda suka kai harin sun kasance mahaifi da kuma ɗa - masu shekaru 50 da 24.

Sun tabbatar da cewa mutumin mai shekara 50 ya mutu nan take yayin da ɗan shekara 24 ɗin kuma ke cikin mawuyacin hali a asibiti.

Wurin da harbin ya wakana - wanda ya lakume rayuka 15.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Wasu ƴanbindiga biyu sun yi harbi daga kan wannan gadar

An yi ta yaɗa bidiyon yadda mista Ahmed ya afka kan ɗan bindigar a shafukan sada zumunta.

Bidiyon ya nuna ɗaya daga cikin ƴan bindigar na tsaye gefen wata bishiyar kwakwa kusa da wata gada, inda yake harbi zuwa wani wuri.

An ga yadda mista Ahmed, wanda ke ɓoye kusa da wata mota ya afka kan maharin.

Ya yi ƙoƙarin kwace bindigar da ke hannun maharin, ya tura shi ƙasa sannan ya juya bindigar kansa. Sannan ɗan bindigar ya fara ja da baya zuwa wurin gadar.

Daga nan Ahmed ya yi ƙasa da makamin sannan ya ɗaga hannu ɗaya a iska, inda yake nuna wa ƴansanda cewa baya cikin maharan.

'Zuwa ga haɗari'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Daga baya an ga wannan maharin a kusa da gadar yana ɗaukar wani makami tare da sake yin harbi.

Wani ɗan bindigar kuma ya ci gaba da buɗe wuta daga saman gadar. Ba a dai san wanene ko kuma me suke nufi ba.

A wurin taron menama labarai da yammacin ranar Lahadi, Premier na jihar New South Wales a Australiya, Chris Minns, ya yaba wa jajircewar Ahmed wanda ba a bayyana sunansa ba a lokacin.

"Wannan mutumi gwarzo ne, kuma ba na shakka akwai mutane da dama da ke raye a yau saboda irin jajircewar da ya nuna."

Firaministan Australiya, Anthony Albanese ya ce: "A yau mun ga Ƴan Australiya ya ruga zuwa cikin haɗri domin taimakawa wasu.

"Waɗannan ƴan Oustraliya gwaraza ne, kuma jajircewarsu ta ceto rayuka."

Da yake magana a wata liyafa kan Kirsimeti a fadar White House, shugaban Amurka Donald Trump, ya yaba wa Ahmed, inda ya ce "yana girmama shi" matuka.

"Mutum ne mai hazaka sosai wanda ya je ya fuskanci ɗaya daga cikin maharan, kuma ya ceci rayuka da dama," in ji Trump.