Yadda Lakurawa suka daɗe suna firgita ƴan ƙauyukan Najeriya

    • Marubuci, Makuochi Okafor
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Tun kafin hare-haren Amurka, ƙauyukan da ke jihohin arewa maso yamma sun daɗe a cikin zullumi saboda barazanar hare-haren ƴan bindiga.

Mayaƙan waɗanda suke amfani da muggan makamai, suke yawan amfani da kayan sojoji sun daɗe a garin Tangaza, wani ƙauye jihar Sokoto da ke da iyaka da jihar Neja na tsawon lokaci, wato Lakurawa.

Mazauna garin Tangaza, waɗanda yawanci musulmi ne sun ce suna zargin yawancin ƴan Lakurawa ƴan Jamhuriyar Nijar ne da Mali, kuma yawanci suna tsoronsu.

A kwanakin baya ne gwamntocin Amurka da Najeriya suka ce Lakurawa suna mubaya'a ga ƙungiyar IS, duk da cewa har yanzu IS ɗin ba ta taɓa alaƙanta kanta da ayyukan mayaƙan ba zuwa yanzu kamar yadda take yi da sauran ƙungiyoyi.

Da BBC ta ziyarci Nukuru, ɗaya ɗaga cikin ƙauyukan da ke Tangaza, mai nisan kilomita 10 daga inda harin Amurka ya sauka, yawancin ƴan ƙauyen suna cikin fargaba da tsoron magana a game da Lakurawa - saboda suna fargabar za su iya kai musu hari.

Sai da aka ba su tabbacin ɓoye suna da sauran bayanansu kafin suka amince za su yi magana, amma duk a haka, sun kasance suna magana cikin sauri da alamar fargaba.

Mun yi tafiyar mai kusan nisan kilomita 12 tare da rakiyar ƴansanda da ƙarin tsaron wasu jami'an tsaro.

Ƴansanda ba su cika shiga irin ƙauyukan nan ba saboda suna cewa ba su da manyan makamai da za su iya fuskantar ƴanbindida da suke yanki ko kuma kare kansu idan an kawo musu hari.

Sai wakilanmu ba su samu damar zuwa daidai wurin da aka ƙaddamar da harin ba saboda tsaro, sannan aka ba mu shawarar ficewa da sauri saboda fargabar ƴanbindiga za su iya dasa bam a hanyar ficewarmu.

Wani manomi da ke zaune a wani ƙauye a kusa da Nukuru ya ce bayan harin Amurka a ranar Alhamis, wasu ƴanbindiga sun tsere zuwa ƙauyensu.

"Sun zo ne a babura kusan 15," in ji shi a zantawarsa da BBC, inda ya ƙara da cewa duk babur akwai mayaƙa uku.

Ya ce ya ji lokacin da suke kiran ƴanuwansu suna faɗa musu cewa su tsere daga yankin, sannan suka tsere a babura.

"Da alama sun shiga ruɗani, suma suna cikin firgici," in ji shi. "Amma ba su ɗauko gawa ko ɗaya ba, kawai kayayyaki suka kwaso."

Amma mazauna Nukuru - wani ƙaramin ƙauye a yannkin sun ga illar harin.

"Harin sai da ya girgiza ƙoƙofi da rufin gidajenmu, rufin wasu gidajen ma sun rufta," in ji wani dattijo mai shekara 70.

"Mun shiga firgici muka kasa barci saboda muna jin girgiɗi, kuma ba mu san me ke faruwa ba kawai mun ji abubuwa na faɗowa ne daga sama, sai muka wuta ta tashi."

Amma duk da haka ƴan ƙauyen suna fargabar ƴanbindigar za su iya komawa. Da babura suke amfani, don haka zirga-zirga ba ya musu wahala.

Sai dai ƙauyen na fuskantar matsalolin rashin abubuwan more rayuwa, babu makaranta babu asibiti da hanyoyin kwalta.

A Nukuru, yawanci ƴan gari sun fi amfani da jaki ne domin zirga-zirga.

Sun ce da Lakurawa suka fara shiga garin, suka kafa kansu, sai ya zama ba su da wata mafita face su amince da dokokinsu da biyan kuɗin haraji. Idan ba su amince, za su fuskanci matsala.

"Mun san ƴan Lakurawa ne saboda mun ga shigarsu," in ji wani ɗan ƙauyen, inda ya kwatanta irin rawaninsu da ke kama da irin na mazauna sahara a Mali da Jamhuriyar Nijar.

Wasu daga cikin ƴanbindigan na magana da Fulatanci, amma suna magana ne da Hausa idan suna magana da ƴan ƙauyen.

Da farko da Lakurawa suka isa yankokin Sokoto da Kebbi, ƴan ƙungiyar sun fara da'awar cewa za su taimaka wa marasa ƙarfi ne, sannan suka fara taimaka musu da tsaro daga ƴanbindiga.

Idan Lakurawa sun shiga gari a yankin bakin iyakar Nijar da Najeriya, dole su kuma ƴanbindiga su fice zuwa wani garin daban.

Da farko sai ƴan ƙauyuka suka fara maraba da su, amma mazauna Tangaza suka ce ba da ɗaɗewa ba sai suka fara gindaya sharuɗa masu tsauri kuma suna tilasta amfani da su.

"Ba ma rayuwa yadda muke so," in ji wani matashi. "Ba ka isa ka saurara ƙida da waƙa ba ko da a cikin wayarka ne. Za su ƙwace wayar, sannan su maka hukunci."

Ƴan Lakurawa suna amfani da matasa da wasu ƴan gari a matsayin masu kwarmata musu bayanai, da kuma taimakonsu wajen sayo musu kayayyakin buƙatu.

Harin na ranar Alhamis ne karo na biyu da aka ƙaddamar da hari kan ƴan Lakurawa a ranar kirsimeti.

A kirsimetin bara, sojojin Najeriya sun kai hari kan Lakurawa a kusa da Gidan Sama da Rumtuwa da ke da nisan tafiyar wasu kilomita daga Nukuru, inda aka kashe fararen hula aƙalla guda 10.

Sannan daga baya gwamnatin Najeriya ta ayyana ƙungiyar a matsayin ƙungiyar ta'addanci.

Da Trump ya sanar da kai harin, ya ce, ƴan ƙungiyar, "sun kasance suna kai hare-hare musamman kan kiristoci ba tare da an sani ba na tsawon lokaci."

Ministan harkokin wajen Amurka, Yusuf Maitama Tuggar ya bayyana cewa hare-haren na haɗin gwiwa ne, "kuma babu wani addini da ake warewa wajen hari a yankin."

Sai dai yawancin ƴan ƙauyen da suka rayuwa a cikin firgici da tsoron ƴanbindigan Musulmi ne, ba Kirista ba.

Amma matuƙar gwamnatin Najeriya da Amurka za su iya haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen fatattakar Lakurawa, tabbas ƴan ƙauyen za su yi farin ciki.

Akwai ƙarin rahoto daga Abayomi Adisa da Gift Ufuoma