Saƙon da Mahamat Deby ya ce mu faɗa wa Tinubu game da Boko Haram - Ribadu

Asalin hoton, X/Nuhu Ribadu
Gwamnatin Najeriya ta ce tana kan tattaunawa da takwararta ta Chadi game da aikin haɗin gwiwa a yaƙi da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi a yankin Tafkin Chadi.
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya faɗa wa BBC cewa ya jagoranci tawagar ta'aziyya zuwa ga Shugaban Chadi Mahamat Idris Deby kan sojojinsa da ƙungiyar Boko Haram ta kashe a baya-bayan nan.
Kisan sojojin kusan 40 ya sa Shugaba Deby ya yi barazanar ficewa daga rundunar Mutlinational Joint Taske Force (MNJTF) yayin da ya kai ziyara sansanin Barkaram - wani tsauni da ke yankin na Tafkin Chadi.
"Mun kai saƙo ne daga shugabanmu Bola Tinubu, ya ba mu takarda mu kai wa shugaban Chadi domin mu jajanta masa saboda duk abin da ya samu Chadi ya shafi Najeriya," a cewar Nuhu Ribadu.
Ƙasashen Najeriya, da Nijar, da Chadi, da Kamaru, da Benin ne ke yin karo-karon dakaru a rundunar, kuma masana na cewa barazanar da shugaban Chadi ya yi ka iya yin illa ga ƙungiyar mai shekara 10 da kafuwa.
Ribadu ya ce sun shafe kusan awa uku suna tattaunawa da shugaban na Chadi.
"Mun yi maganganu masu ma'ana ƙwarai, kuma za mu zauna da Shugaba Tinubu domin duba abubuwan da ya faɗa mana, amma dai abin bai kai a ce za su janye ba. Za mu ƙara gyarawa."
Haɗakar sojin ta ƙasashe biyar wadda ke da babban ofishinta a Chadi tana da dakaru kusan 10,000 a shekarar 2022.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A 2018 lokacin da ƙungiyar take da dakaru 8,000, Chadi ta bayar da 3,000 - mafi yawa bayan Najeriya wadda ta bayar da 3,250. Kamaru na da 2,250, sai Nijar mai sojoji 200, yayin da Benin ta kasance ta ƙarshe da sojoji 150, kamar yadda wani rahoto na makarantar nazarin harkokin soji ta ƙasa da ƙasa da ke Kamaru ta fitar.
Game da barazanar, Mahamat ya ce ƙungiyar ta hadin gwiwar soji ba ta da wani "kyakkyawan tsari" na gudanar da ayyukanta tare wajen yaƙar Boko Haram - saboda haka ne ya ce ƙasar na duba yuwuwar ficewa daga haɗakar da ke aikin tabbatar da tsaro a yankin da ya kasance wata cibiya da ƙungiyoyi masu makamai ke addabar ƙasashen huɗu.
Sai dai Ribadu ya ce Najeriya za ta ƙara ƙaimi a yaƙi da ƙungiyar Boko Haram.
"Da yawansu ['yan Boko Haram] sun gudu sun shiga Chadi da Nijar, kuma na ga can ma an yi ƙoƙari sosai. Mu ma Najeriya muna shiri, abin ya isa haka - da yardar Allah ba za mu bari ba."
Farfesa Oumar Ba na cibiyar nazarin harkokin diflomasiyya da dabaru a Faransa ya faɗa wa BBC cewa yunƙurin Chadi na ficewa daga haɗakar na nuna tarin matsalolin da ƙungiyar ke fuskanta.











