Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben shugaban Tanzania: Yadda mata ke neman kada shugaba Samia Suluhu
A karon farko a tarihi an gwabza babban zaɓen ƙasar Tanzania, amma a wannan karon, an samu mata masu takara da dama da suka tsaya a manyan jam'iyyun ƙasar.
Zaɓen na shekarar 2025, shugabar ƙasar mace ce kuma za ta sake shiga zaɓen ne domin shugabantar ƙasar a karo na biyu, sannan akwai wasu matan biyu da za su yi takara a manyan jam'iyyun hamayya na ƙasar, inda ya zama za a samu mata uku a masu takara a manyan jam'iyyu a babban zaɓen ƙasar.
Masu sharhi suna ganin hakan a matsayin wani ci gaba babba, inda suke cewa hakan na nuna cewa al'ummar Tanzania sun fara aminta da mulkin mata da shugabanninsu a manyan muƙamai.
Tarihin takarar mata
Karon farko da aka samu mace ƴar takara a zaɓen shugaban ƙasar shi ne 2005 lokacin da Anna Senkoro ta yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PPT Maendeleo party. Duk da cewa ita ce ta zo ta takwas a cikin ƴantakara 10 ɗin, takarar ta buɗe ƙofa ga mata ƴansiyasa.
Shekara 10 baya sai Anna Mghwira ta sake takara a ACT, inda ta zo ta uku a shekarar 2015.
Amma dai a zaɓen na 2020 ba a samu wakilcin mata ba sosai. A zaɓen 2020, Cecilia Mwanga ta jam'iyyar Demokrasia Makini da Queen Sendiga jam'iyyar ADC sun yi takara amma ba su samu tagomashi ba.
A zaɓen 2021 ne aka samu dama babba, inda mataimakiyar shugaban ƙasa John Magufuli wato Samia Suluhu Hassan ta ɗare karagar mulki bayan ya rasu.
Shi ne ya zama karon farko da aka samu shugaba mace a ƙasar da ke gabashin Afirka, amma tun a lokacin aka ci gaba da tafka muhawara a ƙasar kan rawar da mata za su iya takawa a siyasar ƙasar.
'Shekarar siyasar mata'
Wannan shekarar za a kafa tarihi domin akwai ƴantakara mata guda uku da suke takara: Samia Suluhu Hassan a jam'iyyar CCM, inda za ta yi takara bayan ta ɗare karagar mulki sanadiyar mutuwar Magufuli. Wannan kuma shi ne karonta na ƙarshe da za ta iya shiga zaɓen a dokar ƙasar.
Akwai Mwajuma Noty Mirambo ta jam'iyyar UMD, wadda tsohuwar ƴarwasa ce da ta koma siyasa, inda ta fara da takarar kansila, sannan ta yi takarar majalisa da dama. Ta sha gwagwarmaya sosai, sannan yanzu ta ce a shirye take ta mulki ƙasar.
Sai kuma Saum Hussein Rashid ta jam'iyyar UDP, kuma babbar sakatariyar jam'iyyar wadda ta dage kan samar da daidaito a siyasa da mulki tsakanin mata da maza.
Bayan waɗannan fitattun ƴantakarar, akwai wasu ƴantakara guda 10 da suka zaɓi mata a matsayin abokan takararsu. Wannan ne karon farko da aka samu wannan nasarar a siyasar Tanzania.
Jam'iyyu 18 ne za su fafata a takarar ta bana, kuma kasancewar an samu mata masu yawa ne ya sa matan suke kira zaɓen da "zaɓen mata."
Me hakan ke nufi?
Masana suna cewa yadda jam'iyyu suka dage wajen jawo mata a siyasa ya ƙaru ne a cikin shekara 15 da suka gabata.
"An samu ƙarin wayar da kai a cikin al'umma, kuma lallai wayar da kan ta yi amfani," in ji masanin siyasa Mohammed Issa.
Wasu lokutan jam'iyyu na fitar da sababbin fuska ne, wanda hakan ya sa suke tsayar da mata wataƙila saboda yadda matasa da mata suke da ɗimbin ƙuri'a a yanzu.
Ƙalubale
Duk da wannan nasarar da ake gani an samu na samun ƙaruwar mata a siyasar ƙasar, akwai ƙalubale masu yawa.
Sai dai har yanzu manyan masu riƙe da shugabancin jam'iyyun ƙasar duk maza ne, kuma mata suna fama da rashin kuɗi da ƴansiyasa da za su taimaka musu wajen yaƙin zaɓe.
"Idan ka cire ƴar takarar CMM Samia Suluh Hassan da sauran ƴantakarar manyan jam'iyyun hamayya za ka ga akwai giɓi babba a hamayya saboda babu hamayya sosai a takarar," Mohammed Issa.
Haka kuma ana sukar yanayin hukumar zaɓen, ciki har da zargin hukumar zaɓen d rashin ba ƙananan jam'iyyu dama.
A wajen ƴan takara Mwajuma da Saum Rashid da za su fuskanci babbar jam'iyyar CCM, wani babban gwaji ne, sannan har yanzu ana ci gaba da ganin mata a matsayin masu rauni wajen shugabanci.