Me zai faru bayan tsige shugaban Koriya ta Kudu?

Lokacin karatu: Minti 2

An tsige shugaban Koriya ta Kudu daga kujerar shugabancin ƙasar bayan da kotun tsarin mulki ta amince da tsigewar da majalisar dokoki ta yi.

An dakatar da Yoon Suk Yeol dai a watan Disamban 2024 bayan da ƴan majalisar dokokin sun tsige shi sakamakon yunƙurin ƙaƙaba dokokin soji.

Magoya baya da abokan hamayya na murna da baƙin ciki dangane da tsigewar ta ranar Juma'a waɗanda suka taru a wurare da dama na birnin Seoul domin kallon yanke hukuncin.

Yanzu kenan dole ne a yi ɗan ƙwarƙwaryar zaɓe ranar 3 ga watan Yuni domin zaɓar mutumin da zai maye gurbin Yoon.

Mene ne abu na gaba?

Bayan watanni ana jiran abin da zai je ya zo, ƴan ƙasar Koriya ta Kudu na buƙatar sake sabuwar tafiya.

Da farko dai dole ne a yi garanbawul domin tabbatar da ba a samu a gaba ba, kuma matakin farko shi ne zaɓen sabon shugaba.

To sai dai ana ganin yanayin da Yoon ya jefa ƙasar ciki bai gushe ba duk da dai cewa watanni shida kawai ya yi yana jagorantar ƙasar a mulkin soja wani abu da ya zagwanye dimokraɗiyya.

Daren ranar 3 ga watan Disamba da Yoon ya umarci sojoji su far wa majalisar dokoki, ya sauya tunanin ƴan Koriya ta Arewa - Hakan ya fama raunin da ke zukatan ƴan ƙasar dangane da mulkin kama karya da suka fuskanta a baya.

Har yanzu da dama ƴan ƙasar na cikin damuwa dangane da abin da ya faru a wannan dare sannan suna fargabar cewa akwai yiwuwar wasu ƴan siyasa nan gaba ka iya bujuro da dokokin sojin na kama-karya.

Hukuncin na ranar Juma'a ya zo wa ƴan ƙasar cike da murna musamman abokan hamayya, inda su kuma magoya bayan shugaba Yoon abin bai yi musu daɗ ba.

To sai dai kuma shugaban riƙon ƙwarya, Moon Hyun-bae ya ce ɗan lokacin da Yoon ya yi mulki na soji haramtacce ne kuma ya yi abun da ya yi ne ba da yardar al'ummar da ya jagoranta ba.

Tuni ake ta samun kiranye-kiranyen buƙatar sauya tsarin kundin mulkin ƙasar domin ƙarfafa tsarin ƙasar da kuma taƙaice ikon da shugaban ƙasa ke da shi da manufar kauce wa faruwar hakan a nan gaba.

Sai dai kuma akwai buƙatar samun shugaban ƙasa mai kishin gaske a nan gaba da zai iya kawar da kai daga daɗin mulki ya rage wa kujerar shugaban iko.