Man City ta shiga damuwa kan Rodri, Chelsea na tattaunawa da Xavi

Rodri

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City ta shiga damuwa kan rasa ɗan wasanta na Sifaniya, Rodri mai shekara 29, yayinda yake nazarin barin ƙungiyar ko tsawaita zamansa zuwa 2027. Real Madrid dai na zawarcinsa. (AS - in Spanish)

Everton na tattaunawa da ɗan wasan Ingila Jack Grealish mai shekara 29, kan zuwa aro daga Manchester City, kan kudin da zai kai £12m. (Times - subscription required)

Newcastle United ta faɗawa ɗan wasan Sweden, Alexander Isak ba za a sayar da shi a wannan kaka ba, kuma ba za ta yarda ya je Liverpool ba, bayan gabatar da tayin fam miliyan 110 kan matashin mai shekara 25. (Telegraph - subscription required)

Newcastle United ta amince da yarjejeniyar saye ɗan wasan Jamus da AC Milan, Malick Thiaw mai shekara 24, kan yuro miliyan 40. (£34.6m). (Mail)

Liverpool na son saye ɗan wasan Ingila, Marc Guehi mai shekara 25, idan ya bar Crystal Palace a wannan kaka. (Telegraph - subscription required)

Chelsea na tattaunawa da Manchester United kan ɗan wasanta na Argentina mai shekara 21, Alejandro Garnacho. (Athletic)

Chelsea na kan tattaunawa da ɗan wasan RB Leipzig mai shekara 22 daga Netherlands, Xavi Simons. (Sky Sports)

Brentford ta tuntuɓi Bournemouth kan saye ɗan wasan Burkina Faso, Dango Ouattara mai shekara 23. (Sky Sports)

Ƙungiyar Sunderland na gab da cimma yarjejeniyar £10m da ɗan wasan Getafe da Paraguay, Omar Alderete mai shekara 28. (Sun)

Ɗan wasan Nantes mai shekara 22 daga Faransa, Matthis Abline na jankalin ƙungiyoyin Paris FC da Eintracht Frankfurt da Wolves. (Fabrizio Romano)

Al Nassr na nazari gabatar da tayin yuro miliyan 30 kan ɗan wasan Bayern Munich mai shekara 29, Kingsley Coman. (Florian Plettenberg)

AC Milan ta shirya kalubalatar abokiyar hamayyarta Inter da Liverpool kan ɗan wasan Parma mai shekara 18 daga Italiya, Giovanni Leoni. (Corriere dello Sport - in Italian)