Yadda Musulman Bosnia ke tunawa da kisan kiyashin da aka yi musu a 1995

Sabrija Hajdarevic na ɗaya daga cikin dubban 'yan ƙasar Bosniya waɗanda aka kashe mata iyali a shekarar 1995
Bayanan hoto, Sabrija Hajdarevic na ɗaya daga cikin dubban 'yan ƙasar Bosniya waɗanda aka kashe mata iyali a shekarar 1995
    • Marubuci, Natasa Andjelkovic and Grujica Andric
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Serbian
    • Aiko rahoto daga, Srebrenica

A kowane watan Yuli, Sabrija Hajdarevic na zuwa Srebrenica don ziyartar ƙabarin mijinta da mahaifinta, wadanda suke cikin maza da yara Musulmi na Bosnia kusan 8,000 da sojojin Sabiya suka kashe a 1995.

Sabrija Hajdarevic mai shekaru 67, yanzu tana zaune a Austiraliya, amma yin balaguro zuwa Srebrenica duk shekara yana da matuƙar mahimmanci a gare ta.

A bana, ziyararta zuwa Srebrenica babba ce domin ranar 11 ga watan Yuli ne za a gudanar da bikin ranar tunawa da wadanda sojojin Sabiya suka kashe a 1995 a Srebrenica karo na farko, bayan da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya yanke hukunci a watan Mayu.

"Ya kamata a san ainihin abin da ya faru a wannan rana, maimakon a ce labaran ƙarya su yi ta yaɗuwa wanda hakan ke ci min rai sosai, da a ce mijina da mahaifina suna raye, ai ba zan taɓa cewa an kashe su ba," in ji Sabrija yayin da take magana kan iƙirarin da ke musanta cewa ba kashe mutanen aka yi ba a Srebrenica.

Kisan kiyashin na Srebrenica, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi a matsayin kisan ƙare-dangi, ya kasance kololuwar yaƙin Bosnia, rikicin da ya barke bayan ballewar Yugoslavia a farkon shekarun 1990.

A Bosnia, ɗaya daga cikin sababbin ƙasashen da aka kafa, al'ummomi uku sun kasance cikin rikici: Sabiyawan Bosniya, waɗanda Serbia ke mara wa baya, da Bosniaks, da 'yan Croatia.

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 11 ga watan Yuli a matsayin ranar tunawa kisan kiyashin da aka yi a Srebrenica.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A watan Mayu ne babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar sanya ranar 11 ga Yuli domin tunawa da kisan ƙarep-dangi da Serbia ta yi

Ana zaton wuta a maƙera sai ta tashi a masaƙa

Garin Srebrenica, wanda a da ya shahara da arzikin azurfa da gishiri, ya kasance gida ga Musulmin Bosnia kusan 40,000.

A lokacin yaƙin 1992 da1995, an tilasta wa 'yan gudun hijira saboda yaƙin share fage na Sabiyawan Bosniya.

A shekara ta 1993, an ayyana garin a matsayin wani yanki mai tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, tare da aikin wanzar da zaman lafiya na ƙasashen duniya domin kare shi daga hare-hare.

Sai dai a watan Yulin shekarar 1995, sojojin Sabiyawan Bosniya ƙarƙashin jagorancin kwamandan soja Ratko Mladic, sun mamaye garin, inda suka yi galaba a kan dakarun wanzar da zaman lafiya. Sojojin Sabiyawan sun raba maza da yara maza da mata, inda ba a sake ganin yawancinsu da rai ba bayan hakan.

Ko dai an kashe su gaba ɗaya, ko kuma sun mutu a lokacin da suke yunƙurin tserewa wanda ya kai ga farautarsu a cikin tsaunukan da ke kewaye da Srebrenica, amma kuma yawancinsu an yi imanin an kashe su ne.

Maƙabartar Srebrenica

Asalin hoton, hoto by FEHIM DEMIR/EPA-EFE/REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Sojojin Sabiya sun kashe Musulmai maza da yara maza kusan 8,000

Mummunan kisan gillar da aka yi wa maza manya da yara kusan 8,000 ya zama sananne a matsayin kisan gilla mafi muni a Turai tun bayan yaƙin duniya na biyu. Ragowar mutane kusan 1,000 har yanzu ba a gansu ba.

Ratko Mladic, kamar shugaban siyasa na lokacin yaƙin, Radovan Karadzic, an daure shi rai da rai saboda laifukan yaƙi, ciki har da kisan kare-dangi, yayin da kusan Sabiyawan Bosnia 50 kuma aka yanke musu hukunci.

Ƙudirin Majalisar Dinkin Duniya na baya-bayan nan da ya ayyana ranar 11 ga watan Yuli a matsayin ranar tunawa da kisan kiyashin Srebrenica na duniya, ya kuma yi tir da duk wani yunƙurin musanta kisan gilla da ɗaukaka masu aikata laifukan yaƙi.

Amma yawancin Sabiyawan Bosniya, da kuma da yawa a Sabiya, sun sha musanta cewa abin da ya faru a Srebrenica a 1995 kisan ƙare-dangi ne.

Binne gawawwaki

Wasu iyalai a Bosniya sun yi shekaru da yawa suna jiran su binne 'yan uwansu.

Sabrija Hajdarevic ta ce ta samu damar binne ƙoƙon kai na mijinta, wanda shi ne bangaren jikinsa daya tilo da aka samu kawo yanzu.

Gawar mahaifinta har yanzu ba a samu ba, kodayake ta san an kashe shi ne a kusa da gidansu a Srebrenica.

Mahaifiyarta ta shaida kisan mahaifinta, kuma akwai hoton da ke nuna mutuwar mahaifinta, wanda Hajdarevic ta ajiye a shafinta na Facebook.

An binne da yawa daga cikin wadanda kisan kare-dangi na Srebrenica ya shafa a makabartar Potocari, kusa da sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

A kowace shekara a wurin bikin tunawa da kisan kiyashin, akan binne gawarwakin wadanda aka gano a cikin watanni 12 da suka gabata a Potocari.

Berija Delic ta rasa mijinta a kisan kuma sai a shekarar 2005 ta sami dawowa da gawarsa.
Bayanan hoto, Berija Delic ta rasa mijinta a kisan kuma sai a shekarar 2005 ta samu gawarsa

Berija Delic ta rasa mijinta a kisan kiyashin, kuma sai bayan shekaru 10 ne aka gano gawarsa, kuma daga karshe aka binne shi a shekara ta 2005. A bara, Delic ta yanke shawarar komawa Srebrenica bayan ta nemi mafaka a Malta biyo bayan yaƙin.

Ɗanta Musulmi, ya auri wata mata 'yar Sabiya mai bin ɗariƙar gurguzu ta Kiristanci.

Srebrenica, wanda akasarinsa garin Musulmin Bosnia ne kafin yaƙin shekarun 1990, yanzu yana da yawan al'ummar Sabiyawa.

Wasu mazauna yankin sojoji ne a lokacin rikicin.

"Har yanzu kuna iya ganin mutane suna yawo a cikin gari, sanin cewa sun kashe ƴan Bosnia, amma shiru ake yi saboda tsoron fuskantar wani bala'i," in ji Delic.

Matsalar rashin aikin yi na gama-gari

Bayan yaƙin, Bosnia ta kasu gida biyu: Jamhuriyar Srpska da Bosnia-Herzegovina, inda Srebrenica ta fada cikin Jamhuriyar Srpska.

A tsawon lokaci, yawan jama'ar Bosnia ya ragu yayin da yawan mutanen Serbia kuma ya ƙaru. Duk da wannan canjin alƙaluma, ƙungiyoyin biyu suna fuskantar ƙalubale na gama gari wato rashin aikin yi.

Slavisa Petrovic, 'ɗan Sabiya mai shekaru 37 da ke kula da ofishin yawon buɗe ido na cikin gida ya ce "Sabiyawa da Bosniyak ba su da wata matsala a tsakaninsu, ya ce duk inda aka ga an samu matsala, to daga waje ne.

A cewar Petrovic, kudurin Majalisar Dinkin Duniya na baya-bayan nan kan kisan kiyashin bai kawo wani sauyi ba. "Har yanzu mutane na barin Srebrenica kamar yadda suka yi kafin a amince da ƙudurin. Babu ayyuka a yanzu."

Alamun koma-baya sun bayyana a garin.

Slavisa Petrovic ne ke gudanar da ofishin yawon buɗe ido na gida
Bayanan hoto, Slavisa Petrovic ne ke gudanar da ofishin yawon buɗe ido na gida.

Hanyoyin da ke kai wa kauyukan da ke makwabtaka da su, wadanda a da suke da manoma masu wadata da lafiyayyun dabbobi, yanzu sun cika da ciyawa.

Yawancin gidajen cikin gida sun kasance kango, wanda ke nuni da yadda yankin ya kasance bayan yaƙin.

Wani masallaci da majami'ar Orthodox na Kiristanci suna zaune tare da juna a kan wani tsauni da ke kallon garin, alamomin tabon da Srebrenica ke da shi a lokacin yakin.

A Srebrenica, yaran Sabiyawa da Bosniak suna zuwa makarantar kindergarten da makarantu tare. Sai dai akwai yiyuwar nan ba da jimawa ba wadannan matasa za su bar garin na dindindin.

Slavisa Petrovic, wanda ke gudanar da ofishin yawon buɗe ido na yankin, ya bayyana baƙin cikinsa kan yadda mazauna yankin ke ci gaba da ficewa. "ji nake kamar daga gida na suke ficewa." in ji shi, yayin da yake shaida yadda ake ci gaba da tabarbarewar al'umma.

Hnayar zuwa Srebrenica
Bayanan hoto, Srebrenica ya zama tamkar birnin da ke raguwa da jama'a

Abokan karatunsa uku ne har yanzu suke zaune a Srebrenica, sauran sun koma wani wuri.

Yayin da Petrovic ya kuduri aniyar cigaba da zama a Srebrenica, ya yarda cewa 'yarsa mai shekara hudu da wuya ta ci gaba da zama a Srebrenica lokacin da ta girma.