Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko kun san ƙwaƙular kunne na haifar da matsalar ji?
- Marubuci, Awwal Ahmad Janyau
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC Abuja
Kunne wani ɓangare ne mai muhimmanci a jikin ɗan’adam wanda ya kamata a kula da shi.
Kunnuwanmu na da mahimmanci ga lafiyarmu - amma duk da haka, galibi ba mu kula yadda ya kamata.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar uku ga watan Maris a matsayin "ranar ji ta duniya" don fadakar da al’umma muhimmancin kula da jinsu.
Taken bikin ranar ta bana shi ne “sauya tunanin mutane game da matsalar ji” - domin an gano akwai wani tunanin da mutane suke da shi wanda ke kara haifar da matsala ga jinsu.
Wata kididdiga ta Hukumar lafiya ta duniya ta nuna cewa aƙalla mutum miliyan 430 ne a fadin duniya ke fama da matsalar da ta shafi rashin ji, inda kuma a Najeriya fiye da mutum miliyan 20 ke fama da wannan matsalar.
Alƙalumman sun nuna cewa yawan mutanen da ke da matsalar ji a duniya yana karuwa kusan kullum.
Kuma masana sun ce galibi mutane ne ke yi wa kunnuwansu illa ba tare da sun sani ba ta hanyar bin wasu hanyoyi da ba su dace ba musamman ƙoƙarin cire dattin kunne ko idan sun ji sauyi ko ƙaiƙayi a kunnen.
Bisa shawarar likita, kada ka taɓa koƙarin tsaftace cikin kunnenka ta hanyar amfani da auduga ko yatsa ko cusa wani abu - domin yana da hatsarin haifar da matsalolin ji ko ma fasa dodon kunne.
Shin akwai dattin kunne?
Galibin mutane kan yi amfani da wasu abubuwa da nufin cire dattin kunne.
Ana amfani da audugar kunne da murfin biro da karen ashana ko tsintiya wajen cire dattin kunne.
Amma a cewar Dr Mustapha Sa’idu kwararren likitan kunne da hanci da kuma maƙogaro a asibitin Murtala da ke Kano a Najeriya, Allah ya halicci kunne ne yadda zai dinga goge kansa da kansa saboda haka ba a bukatar mutum ya riƙa saka wasu abubuwa da nufin cire dattin kunne.
Ya ce kunne yana da wani maiƙo wanda ke halittar kansa da ke taimakawa lafiyar kunnen.
“Abin da ake gani kamar datti idan an saka auduga ko wani tsinke –maiko ne ba datti ba ne wanda ke ba da kariya ga kunne da ke kare datti da hana ƙura zuwa ga dodon kunne.”
"Maiƙon yana sa kunnen yin dadi. Kunne yakan yi ƙaiƙayiyi saboda wata kwayar cuta amma kuskure ne saka wani abu a kunne da nufin cire datti," in ji likitan.
Likitan ya ce ƙoƙarin cire maiƙon a lokacin da yake aikinsa na ƙara lafiyar kunnen zai iya haifar da matsala.
Illar sakacen kunne
Mutane da dama na gani kamar amfani da abin audugar sakacen kunne ba ya da matsala amma kuma yana da illa da har zai shafi jin mutum, a cewar Dr Muhammad Sani, shugaban kwamitin gangami kan ranar ji ta duniya a Najeriya, kuma ƙwararre a babban asibitin kunne da hanci da maƙogoro a Kaduna.
Ya ce babbar matsala ce da kan iya faruwa ga yara da kuma manya.
“Cusa auduga ko tsinke a kune kan iya huje gangan kunnen ya sa jin mutum ya ragu,” in ji likitan.
Dr Mustapha Sa’idu na asibitin Murtala a Kano ya ce cusa audugar kunne ko marfin biro suna da hatsari da ke lahani domin suna iya fasa dodon kunne.
Ya ce datti na iya fitowa da kansa amma amfani da audugu da nufin goge kunne kan iya tura dattin can cikin kunnen.
A cewar likitan goge maiƙon yana da illa a kunne.
“Idan aka dade ana kwakular kunne zai sa ya bushe domin maikon da ke cikin kunne yana da amfani yana kare fatar kunnen daga bushewa kuma kariya ne ga kwayoyin cuta,”
“Ko wanka mutum ya fito ba daidai ba ne ya dinga sa audugar kunne yana ta goge kunne domin yana illata kunnensa ne,” in ji shi.
A cewarsa, ana iya saka yatsa idan ma kumfa ne a kunnen zai fito amma ba a saka tsinke ba ko auduga domin kunne yana wanke kansa da kansa.
Likitan ya ce kunne na yin ƙaiƙayi ne saboda wata kwayar cuta amma kuskure ne cusa wani abu a kunne.
Masana na ganin idan har kunnen mutum yana ciwo ko yawan ƙaiƙayi abin da ya fi dacewa shi ne ya gaggauta zuwa asibiti a duba