Wane ne shugaban China na mutu-ka-raba?

Xi Jinping

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Xi Jinping zai fara wa'adi na uku mai tarihi a matsayin shugaban China

Xi Jinping na shirin fara wa'adi na uku wanda ba a taba yi ba, a yayin babban taron jam'iyyar Kwaminisanci ta China na 20.

Hakan a takaice yana nufin Mista Xi zai ci gaba da zama a kan mulki har tsawon rayuwarsa.

Kasancewar jagororin kasar ta China sun kada kuri'a a 2018 inda suka cire dokar yin wa'adi biyu kawai da ake yi tun shekarun 1990. A karkashin mulkin Shugaba Xi tun 2012, China ta kara zama mai mulkin karfa-karfa a gida, inda take murkushe masu adawa da masu fafutuka, hatta hamshakan attajirai da 'yan kasuwa ba su tsira ba.

Wasu na bayyana shi a matsayin shugaban da ya fi karfa-karfa tun bayan tun Shugaba Mao".

A karkashin mulkinsa China ta bullo da sansanonin gudanar da shirin sauya akida a Xinjiang.

Abin da ake zarginta da yi na tauye hakkin dan-Adam a kan Musulmai 'yan kabilar Uyghur da sauran kananan kabilu.

Ta kara tsaurara rikon da ta yi wa Hong Kong sannan ta lashi takobin sake hadewa da Taiwan, da karfin tsiya idan har hakan ya zama dole.

A abin da ke zama wata alama ta tasirin shugaban, a shekara ta 2017, jam'iyyar Kwaminisanci ta jefa kuri'ar amincewa da shigar da salon mulkin Mista Xi a cikin tsarin mulkin kasar (Xi Jinping Thought on Socialism with Chinese Characteristics for the New Era)

Uban jam'iyya, Shugaba Mao Zedong da shugaban da ya bullo da sauye-sauyen tattalin arziki a shekarun 1980 ne Deng Xiaoping, kawai suka samu shiga cikin kundin tsarin mulkin kasar a cikin jagororinta.

Daga yarima ya koma talaka sannan ya zama shugaban kasa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An haifi Xi Jinping a Beijing a 1953. Mahaifinsa shi ne tsohon dan-gwagwarmayar juyin-juya-hali Xi Zhongxun, daya daga cikin shugabannin da suka kafa jam'iyyar Kwaminisanci, kuma tsohon mataimakin firimiya.

Saboda tushensa na babban gida, ana daukar Mista Xi a matsayin kamar wani yarima - dan manyan mutane wanda ya gaji gidansu.

To amma matsayin gidan nasu ya gamu da koma-baya lokacin da aka daure mahaifinsa a 1962.

Zargin da Shugaba Mao, ya shiga na fargabar juya masa baya daga shugabannin jam'iyya ya sa nan da nan a yi tankade da rairaya na wadanda yake dauka a matsayin abokan gabarsa.

Daga nan kuma sai a 1966 inda aka samu abin da aka kira juyin-juya-hali na al'adu, inda aka zargi miliyoyin 'yan kasar da zama makiyan al'adar China, abin da ya haddasa rikici da hare-hare a fadin kasar.

Su ma 'yan gidansu Mista Xi sun gamu da tasku a lokacin.

An zartar wa yayarsa, wato 'yar mahaifinsa ta farko, wadda ya haifa a auren da ya yi tun a baya hukuncin kisa, kamar yadda bayanan hukuma suka nuna.

Kodayake wani masanin tarihi wanda ya san abubuwan da ke gudana a tsakanin jiga-jigan jam'iyyar ya ce, watakila, an tilasta mata ta kashe kanta ne, kamar yadda wani rahoto na jaridar York Times ya nuna.

An cire Xi lokacin yana yaro daga makarantar da 'ya'yan manyan shugabannin jam'iyyar ke halarta.

A karshe yana shekara 15, ya bar Beijing, inda aka tura shi kauyen Liangjiahe da ke arewa maso gabashin kasar, domin sauya masa akida da kuma yin aiki wahala na dole tsawon shekara bakwai.

To amma maimakon ya juye ya zama mai adawa da jam'iyyra ta Kwaminisanchi, sai ma dai Mr Xi ya rungume ta.

A lokuta da dama ya yi kokarin shiga jam'iyyar amma ake watsi da shi saboda matsayin mahaifinsa.

A karshe dai ya samu karbuwa a 1974, inda ya fara daga lardin Hebei, yana ci gaba da rike manyan mukamai sannu a hankali a kan hanyarsa ta zuwa sama.

A 1989, yana shekara 35, ya zama shugaban jam'iyya a Ningde da ke lardin Fujian da ke kudancin kasar, lokacin da aka fara zanga-zangar neman karin 'yancin siyasa a dandalin Tiananmen na Beijin.

Lardin yana nesa daga babban birnin amma duk da haka aka ce Mista Xi, tare da sauran shugabannin jam'iyya suka tashi tsaye domin magance wannan zanga-zanga a larduna da kauyuka wadda ake shirin yi a Beijing.

Zanga-zangar wadda alama ce ta baraka a cikin jam'iyyar, da kuma yadda aka murkushe ta da karfin tsiya, a yanzu an goge su daga cikin tarihin kasar da kuma bayanan gwamnati.

lamarin ya kai sai da Chinar ta rasa damarta ta karbar bakuncin gasar Olympics ta 2000 saboda yadda gwamnati ta murkushe wannan zanga-zanga ta hanyar cin zarafin mutane a Dandalin na Tiananmen.

An yi kiyasin mutanen da aka kashe a wurin sun kama daga daruruwa zuwa dubbai.

Sai dai kuma bayan kusan shekara 20 da wannan zanga-zanga an nada Mista Xi ya jagoranci gasar Olympics ta bazara ta 2008.

China ta zaku ta nuna wa duniya cewa ta yi gaba kuma ta cancanci ta karbi bakunciun gasar.

Kuma ta nuna cewa hakan na aiki, inda wasannin ke nuna alamar China a matsayin kasa karfi da ke bunkasa.

Shi kuwa Mista Xi, likkafarsa sai kara gaba take yi a jam'iyyar inda ya kasance cikin manyan shugabanninta masu yanke hukunci.

Sannan kuma aka zabe shi a matsayin shugaban kasar ta China a shekara ta 2012.

Shugaba Xi da matarsa Peng Liyuan ( a dama)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Matar Shugaba Xi, Peng Liyuan (a dama), fitacciyar mawakiya ce a China

Ana yawan nuna Shugaba Xi da matarsa, Peng Liyuan, fitacciyar mawaki a kafafen yada labarai na China a matsayinsu na Iyalan Farko na kasar.

Wannan ya saba da al'adar shugabannin kasar na baya inda yawanci matar shugaban kasa ba kasafai take fito da kanta ba.

Ma'auratan suna da 'ya daya, Xi Mingze, amma kusan a ce ba a san komai a kanta ba illa cewa ta yi karatu a Jami'ar Harvard ta Amurka.

Sauran 'yan wannan iyali da harkokin kasuwancinsu na kasashen waje na gamuwa da binciken kwakwaf a manyan kafafen yada labarai na duniya.

Burin China

Mista Xi ya dage sosai wajen tabbatar da abin da ya kira gagarumar bunkasar kasar China.

A karkashin shugabancinsa China a matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya ta bullo da sauye-sauye domin ta yi maganin raguwar bunkasar tattalin arzikinta.

Matakan kuwa sun hada da rage yawan ma'aikatun gwamnatin kasar da suka yi girma sosai da rage illa ga muhalli da kuma gagarumin tsarin fadada alakar kasuwancin kasar.

Wani mutum na goge jirgin kasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani katafaren jirgin kasa na zamani kenan

Kasar na kara tura kanta cikin harkokin duniya, kama daga karfin ikon da take nunawa a tekun kudancinta, zuwa dabarun da take yi cikin ruwan sanyi na zuba jarin makudan kudade na biliyoyin dala a kasashen Asiya da Afirka.

Sai dai wasu daga cikin wannan bunkasa ta harkokin tattalin arzikin wadanda a baya ke karuwa da habaka sosai da sosai, a yanzu sun ragu saboda matakin shugaban na China na kin bayar da kai ko sassauci a game da batun yaki da cutar korona, inda kusan suka ware sauran kasashen duniya tun bayan annobar.

Haka kuma kasuwar harkokin gine-gine ta kasar da ke bunkasa, a yanzu tana ci baya sosai.

Bugu da kari ka-ce-na-cen da kasar ke yi da Amurka a kan harkokin kasuwanci abu ne da ke nuna babu alamar karewa.

Shugaban da ya fi karfa-karfa tun bayan Mao

Tun bayan da ya zama shugaban kasa, Mista Xi ya rika jagorantar matakan kakkabe almundahana da cin hanci da rashawa har zuwa manyan shugabannin jam'iyyar.

Masu suka sun bayyana wannan mataki a matsayin kakkabe na siyasa, wato kawar da abokan hamayyarsa na siyasa.

Haka kuma a karkashin mulkinsa China ta kara daukar matakan tauye 'yanci.

A lardin Xinjiang, kungiyoyin kare hakkin dan-Adam na ganin gwamnati ta tsare Musulman Uyghur sama da miliyan daya da sunan sake ilmantar da su ko kuma sauya musu akida.

Kasar ta musanta zargin da Amurka da sauran kasashe da hukumomi ke mata cewa tana kisan kiyashi ne a can.

Kaka-gidan da gwamnatin Chinar ke yi a kan Hong Kong, ma ya karu a karkashin mulkin Mista Xi.

Masu zanga-zanga a Hong Kong

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga a Causeway Bay, ta Hong Kong a 2019

Mista Xi ya kawo karshen zanga-zangar masu rajin dumukuradiyya a 2020, inda ya sanya hannu a kan dokar tsaro ta kasa.

Dokar ta bai wa gwamnati damar yanke hukuncin zaman gidan yari na rai da rai ga duk wanda aka samu da kalubalanta ko hada kai da wata kasar waje kan Hong Kong.

Dokar ta kai ga kama masu rajin dumukuradiyya da dama da 'yan siyasa tare da rufe fitattun kafafaen yada labarai ciki har da Apple Daily da Stand News.

A karkashin shugabancin Mista Xi, China ta kara tsananta hankalinta a Taiwan, inda ta lashi takobin sake hadewa da yankin mai cin gashin kansa.

Har ma ta yi barazanar amfani da karfin soja domin kare yankin da duk wani yunkuri na samun cikakken 'yancin kai.

Ganin yadda karfi da tasirin China suke, duniya za ta sanya ido a kan Mista Xi yayin da ya fara wa'adi na uku a matsayin shugaban kasa.

Kasancewar babu wani magajinsa a fili ana ganin shugaban mai shekara 69 shi ne jagoran China mafi nuna karfin iko tun mutuwar Mao Zedong a shekarun 1970.