Me ya sa ake ƙara samun tankiya tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu?

    • Marubuci, Joel Guinto
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Singapore
    • Marubuci, Juna Moon
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Korean
    • Aiko rahoto daga, Seoul
  • Lokacin karatu: Minti 4

Koriya ta Arewa ta zargi Koriya ta Kudu da aika jirage marasa matuƙa zuwa babban birninta, abin da ya ƙara janyo zaman tankiya a tsakanin maƙwabtan tsawon watanni.

Jirage marasa matuƙa a cewar rahotanni sun watsa takardu a Pyongyang, wani abu da Koriya ta Arewa ta bayyana a matsayin takala da ka iya kai wa ga yaƙi.

Bayan waɗannan zarge-zarge da ake yi wa Koriya ta Kudu a ranar Juma'a, Pyongyang ta ce ta bai wa sojojin da ke bakin iyaka umarnin su shirya kai hari.

Koriya ta Kudu a ɓangarenta ta ce a shirye take ta mayar da martani tare da gargaɗin cewa idan aka yi wa tsaron jama'arta barazana hakan zai alamta zuwan ƙarshen zamanin Koriya ta Arewa.

A ranar Talata kuma, Koriya ta Arewa ta kai harin da ya lalata ɓangarorin wasu tituna da ke kai wa ga Koriya ta Kudu.

Waɗannan su ne tashin hankalin baya-bayan nan tsakanin maƙwabtan junan da ya kai ƙololuwa cikin shekaru tun da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ya ayyana a watan Janairu cewa Koriya ta Kudu ce babbar abokiyar gabar gwamnatinsa.

Mene ne ke faruwa?

A ranar 11 ga Oktoba ne ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta zargi Koriya ta Kudu da tura jirage marasa matuƙa zuwa Pyongyang cikin dare tsawon mako biyu.

Ta ce takardun da jirage marasa matuƙa suka jefa suna ɗauke da ƙarairayi da shirme.

Ƴar'uwar Kim, Kim Yo-jong, ta gargaɗi Seoul kan gamuwa da mummunan sakamako idan aka ƙara samun jirage marasa matuƙa da suka shiga ƙasar.

Daga baya ta ce akwai hujja mai ƙarfi da ke nuna cewa Koriya ta Kudu ce ke da hannu a lamarin.

Koriya ta Arewa ta fitar da wasu daɗaɗɗun hotuna na abin da ta kira jirage marasa matuƙa suna tashi a sama da kuma hotunan da ke nuna takardun sai dai ba a iya tantance iƙirarin ba.

Yayin da Koriya ta Kudu tun asali ta musanta aika jirage marasa matuƙa zuwa Koriya ta Arewa, shugaban ma'aikatanta daga baya ya ce ba za su iya tabbatarwa ko ƙaryata zargin Pyongyang ba.

Akwai raɗe-raɗi cewa wasu ƴan fafutuka ne suka tuƙa jiragen waɗanda ke tura waɗannan kayayyaki zuwa Koriya ta Arewa ta hanyar amfani da balan-balan.

Park Sang-hak, shugaban gamayyar ƙungiyar Free North Korea, ya musanta iƙirarin Koriya ta Arewa game da mamayar jirage marasa matuƙa inda ya ce "Ba mu tura jirage marasa matuƙa ba zuwa Koriya ta Arewa".

A ranar Litinin, Kim ya haɗu da shugaban rundunar soji da manyan hafsoshin tsaro da ministocin tsaro da manyan jami'an gwamnati, in ji kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa, KCNA.

A can, Kim ya tsara shirin ɗaukan matakin soji cikin gaggawa. Wani babban jami'in Koriya ta Kudu, Lee Sung-joon ya ce Koriya ta Arewa na iya takalar fada kamar ta amfani da fashewa kan titunan da ke haɗa ƙasashen na Koriya.

Sai kuma ga fashewar da ta faru kan titunan Gyeongui da Donghae.

Yayin da aka daɗe da rufe titunan biyu, hakan na aika saƙo cewa Kim bai shirya tattaunawa da Koriya ta Kudu ba, a cewar masu sharhi.

Bayan fashe-fashen, sojin Koriya ta Kudu sun ce sun harba makamai kan iyakokinta a zaman nuna ƙarfi sannan kuma suna ƙara sa ido kan Koriya ta Arewa.

Sa'oi bayan nan, gwamnatin Lardin Gyeonggi da ke kewaye da Seoul, ta ware wasu yankuna 11 kan iyaka da ta ayyna su a matsayin masu haɗari a ƙoƙarin hana mutane tura takardun nuna ƙiyayya zuwa ga tsallaken iyaka.

"Lardin Gyeonggi ya ce matakin watsa takardu a Koriya ta Arewa na da haɗarin gaske wanda kuma zai iya janyo rikicin soji," in ji Kim Sung-joong, mataimakin gwamnan Lardin Gyeonggi, a wani taron ƴan jarida.

Rarraba waɗannan takardu na iya barazana ga rayuka da kuma tsaron jama'armu", in ji Kim, yayin da alaƙar ƙasashen biyu ke ƙara taɓarɓarewa.

Me hakan ke nunawa?

Masu sharhi sun ce batun jirage marasa matuƙa ya nuna cewa Koriya ta Arewa tana samun tallafin cikin gida ta hanyar nunawa kamar barazanar da ƙasar ke fuskanta na ƙaruwa.

Amfani da kalmomi kamar jihohi da ke rabe a matsayin Koriya ta Kudu da kuma jefa wasu kalmomi wani ɓangare ne na wannan dabara, in ji Farfesa Kang Dong-wan, da ke koyar da bkimiyyar siyasa da diflomasiyya a jami'ar Dong-a da ke Busan.

"Gwamnatin Koriya ta Arewa ta dogara ne kan siyasar kaɗa hantar maƙwabta sannan tana buƙatar abokin gaba a waje," in ji Farfesa Kang in ji shi.

"A duk lokacin da zaman ɗar-ɗar ya ƙaru, Koriya ta Arewa na ɗora alhaki kan wata ƙasa domin ƙara samar wa gwamnatin goyon baya."

Masu sharhi sun ce abin da ke faruwa tsakanin kasashen biyu na nuna yadda ƙasashen biyu suke gudun nuna gazawa.

"Babu wani ɓangare da ke son ja da baya a yanzu," in ji Farfesa Kim Dong-yup daga jami'ar North Korean Studies a Seoul.

Sakamakon rashin yadda da juna da ake da shi, Seoul na buƙatar su duba yadda za su tafiyar da rikicin", kamar yadda Farfesa Kim ya bayyana.

Shin ƙasashen Koriya na tunkarar yaƙi ne?

Masu sharhi sun ce ba dai yanzu ba.

"Ba na tunanin yanayin zai ƙazance har zuwa matakin yaƙi. Koriya ta Arewa na bin salon fito na fito domin ƙarfafa ƙarfinta a cikin gida," in ji Farfesa Kang.

"Ina da shakku kan ikon Koriya ta Arewa na takalo babban yaƙi. Gwamnatin ta san sarai irin sakamakon da irin yaƙin zai kawo," in ji Farfesa Kim.

Cacar bakin baya-bayan nan kan zargin aika jirage marasa matuƙa zai ci gaba da zama ne iya yaƙin cacar baka," in ji Farfesa Nam Sung-wook, da ke koyarwa a jami'ar.

Saboda Seoul da Pyongyang sun san cewa ba za su so a gwabza yaƙin fito na fito ba kamar yadda Farfesa Nam ya ce, "babu yiwuwar yin amfani da makaman nukiliya".

Mece ce alaƙarsu da ƙasashen waje?

Ƙasashen na Koriya har yanzu suna rikici tun da ba su rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya ba a lokacin da yaƙin Koriya ya zo ƙarshe a 1953.

Kim ya sa Koriya ta Arewa ta ƙara samun kusanci da Rasha a ƙarƙashin Vladmir Putin, abin da ya sa ƙasar ta yi baƙin jini a wajen Amurka da ƙasashen yamma, waɗanda ƙawayen Koriya ta Kudu ne.

Haka kuma, abu mai muhaimmanci shi ne daɗaɗɗiyar alaƙar Koriya ta Arewa da China.

A batun taƙaddama kan jirage marasa matuƙa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen China a ranar Talata ya yi kira ga ɓangarorin da su guji ƙazancewar rikicin.

Zaman ɗarɗar a ƙasashen biyu na ƙaruwa yayin da yaƙin neman zaɓen Amurka ke zuwa zagayen ƙarshe.