Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hujjoji sun tabbatar da jiragen Rasha marasa matuƙa sun yi luguden wuta kan fararen hula a Ukraine
- Marubuci, Yogita Limaye
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, in Kherson
- Lokacin karatu: Minti 5
Wata rana wani mutum mai suna Serhiy Dobrovolsky, ya dawo gidansa da ke Kherson a kudancin Ukraine. Yana shiga gidan, ya kunna sigarinsa yana gaisawa da maƙwabcinsa, kawai sai ya ji ƙarar shawagin jirgi mara matuƙi a sama.
Angela, matar Serhiy mai shekara 32 ta ce ta ga lokacin maigidanta ya ruga a guje ya samu mafaka a lokacin da jirgin ya harbo bom. "Ya rasu kafin motar ɗaukar marasa lafiya ta ƙaraso, an ce mani wani ƙarfe ne ya huda masa zuciya," in ji ta a cikin hawaye.
Serhiy yana cikin fararen hula 30 da hare-haren jirgi marasa matuƙa suka kashe na kwana-kwanan a Kerson tun daga 1 ga Yuli, kamar yadda hukumar sojin yankin ta shaida wa BBC. Jirage marasa matuƙa sun kai musu hare-hare sama da 5,000 a ɗan tsakankanin nan, inda sama da fararen hula 400 suka jikkata.
Amfani da jirage marasa matuƙa ya zo da wani sabon salo a yaƙin Ukraine, inda da ita Ukraine ɗin da Rasha suke amfani da su wajen kai hare-hare.
Amma BBC ta ji daga bakin wasu ganau, sannan ta samu hujjoji masu inganci da suka nuna cewa Rasha na amfani da jiragen a kan fararen hula a birnin Kherson.
"Suna ganin waɗanda suke kashewa," in ji Angela. "Haka suke so yaƙin ya kasance, ta hanyar jefa wa mutane masu tafiya a titi bama-bamai?"
Idan aka gano Rasha na kai hare-hare kan fararen hula, hakan zai zama laifukan yaƙi.
Rundunar sojin Rasha ba ta ce wa BBC komai ba a kan zargin, inda tun ƙaddamar da yaƙin da ta yi a Fabrailun 2022 a Ukraine, take musanta batun kai wa fararen hula hari da gangan.
Hujjojin amfani da jirage marasa matuƙa kan fararen hula suna bayyana ne a faye-fayen bidiyo da dama da ake yaɗawa a kafofin sadarwa da kafofin watsa labarai, inda BBC ta tantance wasu.
A kowane bidiyo da BBC ta tantance, mun ga yadda na'urorin naɗar hotuna na gida suke nuna mutane suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum, amma sai a harbo musu bama-bamai, inda da dama suke jikkata, wasu lokutan kuma, wasu su rasu.
Haka kuma BBC ta gano wani zauren Telegram wanda a ciki ake fara wallafa yawancin faye-fayen, kuma a ciki akwai guda biyar daga cikin shida da muka tantance.
Rundunar sojin Kherson ta shaida wa BBC cewa Rasha ta canja irin jirgi marasa matuƙa da take amfani da su, inda yanzu tsaron sararin samaniyar birnin ba ya iya kakkaɓo su.
"Mutum sai ya riƙa ji kamar ana neman rayuwarsa, kamar akwai wanda yake ganin duk inda ka shiga kuma zai iya harba maka bom," in ji Kristina Synia, wadda ke aikin sa kai a birnin.
Akwai alamar damuwa a fuskokin yawancin mazauna yankin da BBC ta gana da su, waɗanda suke kukan kura su fito waje domin sayen kayayyakin abinci. Valentyna Mykolaivna ta ce, "muna cikin mayuwacin hali. Idan muka fito waje, muna tafiya ne muna laɓewa a ƙarƙashin bishiya. Kullum suna kai hari kan motocinmu na haya, suna kuma jefa mana bama-bamai ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa," in ji ta.
Olena Kryvchun ta ce ta taɓa sha da ƙyar lokacin da wani jirgi mara matuƙi ya kai hari kan motarta mintuna kaɗan kafin ta shiga motar.
"Da a ce ina cikin motar, da na rasu. Shin na yi kama da soja ne? motata ta yi kama da motar soji ne?" in ji ta. Tana aikin share-share ne, kuma motar na da amfani a gare ta matuƙa wajen zirga-zirgarta, kuma ba ta kuɗin da za ta gyara.
Olena ta ce jirage marasa matuƙa suna firgita su idan suna shawagi a sama. "jirage marasa matuƙa suna da sauri, da sun ga, za su harba maka bom."
Ben Dusing ya bayyana cewa jirage marasa matuƙa sun fi hatsari. "Da zarar jirage marasa matuƙa sun ganka, to fa shi ke nan, babu yadda za ka iya tsira," in ji shi.
A ƴan watannin da suka gabata, kakakin rundunar sojin Kherson, Oleksandr Tolokonnikov ya ce sojojin na Rasha suna amfani da jirage marasa matuƙa suna harba bama-bamai a hanoyin wucewa da motoci da titunan motocin haya.
Olena ya ce yanzu da hunturu ke ƙaratowa, ana fargabar lamarin zai tsananta, "idan bishiyoyi suka bushe, babu inda mutane za su riƙa laɓewa."
Yadda muka tantance faye-fayen bidiyon
Mun bibiyi faye-fayen guda shida waɗanda aka naɗa a gabashin Kherson, ta hanyar nazari tare kwatanta wuraren da ke cikin bidiyon da wuraren da suke asalin yankin. A wani bidiyon - inda wani jirgi mara matuƙi ya harba bom kan mutum biyu masu wucewa, inda ɗaya daga cikin su ya jikkata, har ba ya iya tafiya - a wurin da ake kira T-Junction da ke gundumar Dniprovskyi, ko kuma gefen garin Antonivka.
Da zarar mun gane wane wuri ne, muka kwatanta shi da hoton da ke bidiyon da kuma tabbatar da garin da lamarin ya auku.
Domin tabbatar da inda aka fara wallafa bidiyon, muna binciken inda muka yanka daga bidiyon da dama a intanet. Yawanci suna nuna mana wani zauren Telegram ne, inda yake nuna an fara ɗora su kafin a ɗora a X da Reddita da wasu sa'o'o.
Bayan tabbatar da wurin da aka yi harin, sai mu lissafa tsawon lokacin da aka ɗauka ana naɗar bidiyon.
Faye-faye huɗu daga cikin waɗanda muka yi nazari, an ɗora su ne a zauren Telegram washegarin ranar da aka ɗauke su, ɗaya daga ciki ma an ɗora ne kimanin sa'a takwas a ranar da aka ɗauka.
Akwai ƙarin rahoto daga Imogen Anderson, Anastasiia Levchenko and Volodymyr Lozhko. Aikin tantancewa daga Richard Irvine-Brown