Man United ta kara karo da tasgaro a Premier a Old Trafford

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta yi rashin nasara 2-0 a hannun Crystal Palace a wasan mako na 24 a Premier League da suka kara ranar Lahadi a Old TTrafford.
Palace ta ci ƙwallon ne ta hannun Jean-Philippe Mateta, sannan shi ne ya kara na biyun da ta haɗa maki ukun da take bukata.
Wasa na uku a jere da ƙungiyar Selhurst Park ta yi nasara a waje kenan a Premier, wadda rabonda ta yi wannan ƙwazon tun bayan Mayun 2019.
Palace ta je ta doke Leicester City 2-0 a gasar ta Premier League ranar 15 ga watan Janairu, haka ma yi nasara a West Ham 2-0 ranar 18 ga watan Janairu da wannan na United.
Kuma maki na 16 da ta haɗa kenan tun daga Kirsimeti, ba wata ƙungiyar da ta samu maki da yawa hak kamar na Palace a lokacin.
Palace ta yi nasara a kan United karo na shida daga wasa 12 baya, wadda ta yi canjaras uku da rashin nasara uku daga karawa shida da ta yi a Old Trafford.
Rasmus Hojlund ya shiga wasan, sauran minti 20 a tashi karawar, wanda ya canji Mainoo, kenan Hojlund ya buga lik da kofi na 13 ba tare da cin ƙwallo ba.
Rabonda Hojlund ya ci wa United ƙwallo tun 12 ga watan Disamba a Europa League a karawa da Victoria Polzen.
Wannan shi ne karo na bakwai da aka ci United a Premier League a Old Trafford a bana, bayan Liverpool da ta ci 3-0 da Tottenham da ta yi nasara 3-0 da Nottingham Forest da ta je ta ci 3-2.
Sauran ƙungiyoyin da suka doke United a gida a Premier sun haɗa da Bournemouth da ta ci 3-0 da Newcastle da ta yi nasara 2-0 da kuma Brighton da ta ci 3-1.
United ta yi kasa zuwa mataki na 13 da maki 29, bayan cin wasa takwas da canjaras biyar aka doke ta karawa 11.
Palace kuwa ta haye gurbi na 12 da maki 30, wadda ta yi nasara bakawi da canjaras tara aka doke ta fafawa takwas.










