Ko dabarar Trump ta barazana da rashin nuna alƙibla na tasiri a duniya?

Ko dabarar Trump ta barazana da rashin nuna alƙibla na tasiri a duniya?
    • Marubuci, Allan Little
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 8

A watan da ya gabata ne aka tambaye shi ko yana da shirin taya Isra'ila kai wa Iran hari, sai shugaban na Amurka Donald Trump ya ce, "watakila na yi. Kila kuma ba zan yi ba. Ba wanda ya san abin da zan yi".

Ya sa duniya ta sakankance cewa ya ba Iran mako biyu kan ta yanke shawara game da komawa kan tattaunawar shirin nukiliya. Amma kuma ba zato ba tsammani sai ya kai wa Iran din hari.

Yanzu dai wani abu na zama tabbas game da Trump: Abin da ba shi da tabbas a kansa shi ne, rashin sanin alkibilarsa. Nan da nan sai ya sauya ra'ayinsa. Ba shi da tabbas a kan abu.

Trump yana amfani da salon shugabanci irin wanda tsohon shugaban Amurka Richard Nixon ya yi fice a kai, kamar yadda farfesa Peter Trubowitz, masani a kan dhuldar kasasahe ta duniya a Jami'ar London ya ce.

Wannan salo kuwa shi ne wanda aka yi wa lakabi da, ''Madman Theory'' - wanda shi ne rashin tabbas a kan alkiblar mutum ta yadda ba za a iya hasashen abin da shugaba zai yi ba.

Shugaban yakan nuna wa masu hamayya da shi cewa zai iya amfani da fushi da bacin rai wajen cim ma muradunsa. Wato dai salo ne na kamar tirsasawa domin samun biyan bukata.

Wannan dabara da Trump yake amfani da ita yanzu ta rashin sanin alkiblarsa ta zama wani muhimmin jigo a siyasarsa.

A yanzu shugaban ya daukaka wannan salo na rashin sanin tabbas a matsayin wata manufa.

Kuma yanzu wannan salo ya zama wata hanya ta tafiyar da maufofin kasar waje da kuma tsaro a mulkin Amurka.

Wannan kuma na sauya yadda yanayin duniya yake a yanzu.

Wannan dabara ce a yanzu Trump yake amfani da ita wajen kai kawayen Amurka inda yake so.

To amma za a iya cewa wannan dabara ce da za ta iya aiki a kan abokan gaba? Sannan za a iya cewa idan ta kuskure ba a kai ga cimma bukata ba, za a iya gano dabarar cikin sauki?

Hari da cin mutunci da kuma abota

Trump ya fara shugabancinsa na wa'adi na biyu ta hanyar rungumar shugaban Rasha Vladimir Putin da kuma sukar kawayen Amurkar kanta.

Ya ci mutuncin Canada ta hanyar cewa zai kwace ta ta zama jiha ta 51 ta Amurka.

Sannan ya ce yana shawarar amfani da karfin soji wajen kama yankin Greenland mai cin gashin-kansa da ke karkashin kasar Denmark.

Bugu da kari ya kuma ce Amurka za ta sake karbe iko da mashigar Panama.

Doka ta 5 ta kungiyar tsaro ta Nato ta tanadi cewa dukkanin mambobin kungiyar za su hadu su yi taron-dangi domin kare duk mambarsu da ke fuskantar wata barazana.

Shugaba Trump ya jefa wannan tanadin doka cikin shakku, kamar yadda tsohon sakataren tsaro na Birtaniya Ben Wallace ya bayyana.

Haka kuma tsohon babban aluyan gwamnatin Birtaniya, Dominic Grieve, dan jam'iyyar Kwanzabatib ya ce: ''A yanzu dai wannan hadaka ta tsaro ta Nato ta zo karshe.''

Kazalika an ga wasu rubutattun sakonni na waya inda sakataren tsaro na Amurka Pete Hegseth yake kalamai na batanci ga kasashen Turai - kawayen Amurka.

Duka wadannan kalamai da Trump da jami'an gwamnatinsa ke yi na batanci da raini a kan kawayen Amurka na nuna shakku sosai a kan alakar Amurka da sauran kasashen duniya, in ji Farfesa Trubowitz.

"Duk wata fahimta da wadannan kasashe na Turai suke da ita da Amurka a kan tsaro da tattalin arziki da sauran abubuwa na iya sauyawa cikin dan kankanin lokaci.

"A fahimtata yawancin mutanen da ke kewaye da Trump suna ganin rashin sanin alkibila abu ne mai kyau, saboda hakan na ba Trump damar tursasawa ta samu yadda take so." In ji masanin.

Trump na cin nasara da wannan dabara, domin wata hudu da ya wuce Firaministan Birtaniya Sir Keir Starmer ya gaya wa majalisar dokokin kasar cewa Birtaniya za ta kara yawan kudaden da take kashewa a tsaro daga kashi 2.3 bisa dari zuwa 2.5 cikin dari daga arzikitinta na cikin gida.

Hasashe da rashin sanin alkibla

Trump ba shi ne shugaban Amurka ba na farko da yake amfani da wannan salo na rashin nuna alkibila wajen tafiyar da mulkinsa ba.

Shugaba Richard Nixon shi ne wanda ya yi fice da wannan salo.

A 1968 lokacin da shugaban yake son kawo karshen fadan Amurka da Vietnam, ya yi amfani da wannan salo.

''Shugaba Nixon ya gaya wa mai ba shi shawara kan tsaro Henry Kissinger, 'ya kamata ka gaya wa masu shiga tsakani a yakin nan na bangaren Vietnam cewa fa Nixon ya harzuka kuma ba ka san abin da zai yi nan gaba ba, saboda haka ya kamata ku zo a sasanta kafin abubuwa su baci', '' in ji Farfesa Micheal Desch na Jami'ar Notre Dame.

Ita ma Farfesa Julie Norman, ta Jami'ar London ta tabbatar da cewa yanzu dai akwai wannan tsari na rashin sanin alkibila - ana amfani da shi.

"Abu ne mai wuya ka san me zai faru a kullum.Ta ce. "Kuma wannan ita ce dabarar Trump a kodayaushe."

Trump ya yi nasara wajen amfani da dabararsa ta nuna fushi da harzuka wajen sauya alakar tsaro tsakanin Amurka da sauran mambobin kungiyar tsaro ta Nato.

Hakan ya kai ga har wasu shugabannin Turai na yaba wa shugaban a kokarin da suke na ganin yana tare da su bai rabu da su ba.

Babban Sakataren Nato, Mark Rutte ya aika wa da Trump sakon rubutu ta waya inda yake gode masa kan matakin da ya dauka a kan Iran - sakon da Trump ya fitar da shi duniya ta gani.

darektan sadarwa na Trump a lokacin mulkinsa na farko, Anthony Scaramucci, ya ce: "Mista Rutte, (Trump) na neman kunya ta ka ne, ranka ya dade, sir. Yana zaune a cikin jirgin shugaban kasa yana maka dariya ne kawai."

Idan haka ta tabbata to kenan wannan na nuna raunin wannan dabara ta Trump, domin ya mayar da hankali ne kenan wajen cin riba ta dan lokaci maimakon maimakon alaka ta tsawon lokaci.

Mika wuyan abokan hamayya

Akwai kuma maganar da ake yi kan cewa ko wannan dabara ta barazana da karfi ko rashin nuna alkibila na iya yin tasiri a kan abokan hamyya ko gaba.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky wanda Trump da mataimakinsa suka yi wa tatas a ofishin Trump din, daga baya ya yarda ya bai wa Amurka damar kwasar dimbin albarkatun kasa daga kasarsa.

To amma a daya bangaren Shugaba Vladimir Putin na Rasha ko gezau bai yi a kan dadin baki da barzanar Trump - A ranar Alhamis a lokacin da suke magana ta waya, Trump ya ce ya ji takaicin yadda Putin ya nuna ba a shirye yake ya kawo karshen yakin Ukraine ba.

To Iran fa? Trump ya yi alkawarin cewa zai kawo karshen shiga yaki da Amurka ke yi a Gabas ta Tsakiya har abada.

Saboda haka harin da ya kai wa Iran abu ne da ba a taba tsammani ba bisa wadancan kalamai nashi.

To amma maganar ita ce ko hakan da ya yi zai biya bukata?

Tsohon sakataren harkon wajen Birtaniya, William Hague yana ganin maimakon amfani kishiyar hakan matakin zai haifar.

Ya ce yana ganin wannan zai sa Iran ta tashi tsaye haikan yanzu a kan shirinta na nukiliya - ta ce lalle sai ta mallaki makaman nukiliya ganin abin da aka yi mana yanzu.

Daya daga cikin manyan misalai a kan wannan shi ne bayanin Farfesa Mohsen Milani na Jami'ar South Florida kuma marubucin littafi a kan Iran da gabarta da Amurka a Gabas ta Tsakiya (Iran's Rise and Rivalry with the US in the Middle East.)

''A 1980 lokacin da Saddam Hussein ya kai wa Iran hari nufinsa shi ne rushewar kasar,'' in ji shi. ''To amma abin da ya faru sabanin haka ne - sai ta kara bunkasa.''

''To wannan shi ne lissafin Amurka da Isra'ila.'' In ji malamin jami'ar.

To wannan na nufin dabarar Trump ta sa kasashen Turai sun tashi tsaye kenan wajen sauya tsarin tsaronsu tun bayan yakin duniya na biyu?

Farfesa Milani na ganin Trump na amfani da wannan dabara ta rasjhin sanin alkibila ko tursasawa domin tabbatar da dorewar karfin Amurka a duniya saboda China na barazanar kawar da ita a wannan matsayi.

Kawayen Amurka na Turai suna ganin ta hanyar dadin baki da yabo Trump ba zai yi watsi da su ba, to amma wannan hali nashi na rashin sanin alkibilarsa na nufin ba abin dogaro ba ne.

Kuma tuni suka farga da haka - shi ne ma ya sa yanzu suka fahimci cewa ba ta yadda za su ci gaba da dogaro da Amurka a kan tsaro.

A dangane da wannan, a iya cewa dabarar ta Trump ta rashin nuna alkibilarsa na amfani a kan wasu akalla.